Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Ginshiƙan zaɓan mace da na miji

A cikin wannan darasin zamu san mahimman ginshiƙan zaɓan ma'aurata

  • Gabatarwa akan matsayin ɗaurin aure a Musulunci. 
  • Sanin mahimman ka'idoji wajen zaɓan ma'aurata. 
  • Bayanin adalcin Musulunci ga mace wajen zaɓan miji. 

Daurin aure yana daga cikin mafi mahimmanci kuma mafi girman ababe a cikin Musulunci. Shari'ar Musulunci ta kewaye ta da matakai na share fage da ke shirya kowane ɓangareshi don cimma amfaninshi da cin gajiyarshi, da kuma taimakawa wajen ganin an ci gaba da zaman aure cikin kwanciyar hankali a gidan musulmi.

Rukunnan Iyalai

Manyan ginshiƙai guda biyu na gina iyali su ne miji da mata, kuma haƙiƙa shari’a ta kwadaitar a bisa kasancewar kyakykyawar alaƙa a tsakaninsu, kuma ta sanya tabbatar da hakan yana daga cikin ayoyin Allah da kuma ni’imominShi da ya yi wa bayinShi.

Allah Ta’ala ya ce: {Kuma daga cikin ayoyinShi ne Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku natsu zuwa gare su; Kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.} [Ar-Rum: 21].

Kyautata zaɓan ma'aurata

Zabar abokiyar rayuwa mai kyau shi ne mataki mafi mahimmanci domin tabbatar da rayuwan aure mai daɗi da kuma gina iyali mai ɗorewa.

Mahimman ƙa'dojin zaɓar ma'aurata

١
Ingancin Addini da halaye.
٢
Natsuwar Rai

Ingancin Addini da halaye

Wannan shi ne asalin da ya kamata kowanne daga cikin ma'aurata ya mai da hankali akanshi yayin zaɓan abokin rayuwa, domin ingancin addini da halaye da yardan Allah shi kaɗai ya isa ya samar da jin daɗi da rabauta a cikin duniya da lahira.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwaɗaitar da a zaɓi mace ta gari mai addini, yana mai cewa: “Ana auren mace saboda dalilai guda huɗu: saboda dukiyarta, da zuriyarta, da kyawunta, da addininta, don haka ka zaɓi mai addini, hannayenka za suyi albarkah”. (Al-Bukhari 5090, da Muslim 1466). Mace mai addini ita ce zata ji tsoron Allah Ta'ala ta kuma kiyaye haƙƙin gidanta da na mijinta a gabanshi da kuma a bayanshi.

Dangane da zaɓar wanda za a aura kuma, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan wanda kuka yarda da halayensa da addininsa ya zo muku, to ku aure shi, idan ba ku yi haka ba, za a samu fasadi mai girma da ɓarna a bayan ƙasa" (Ibn Majah 1967). Wasu daga cikin musulman farko sun kasance suna cewa: “Idan zaka aurar da ƴarka to ka aurar da ita ga mai addini, idan yana sonta sai ya girmama ta, idan kuma ya ƙi ta to ba zai zalunce ta ba.

Natsuwar Rai

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Rayuka suna nan nau'o'i kala-kala, daban-daban waɗanda suka gane juna suna kusantar juna, waɗanda kuma ba su saba da juna ba su yi nisa”. (Al-Bukhari 3336, Muslim 2638). Wannan yana jaddada mahimmancin natsuwar zuciya da kwanciya a rai tsakanin ma'aurata don samun jituwa da kuma rayuwar aure mai daɗi ta ci gaba.

Saboda haka ne Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umurci duk wanda zai nemi auren mace da cewa: “Kayi dubi zuwa gare ta, lallai hakan zai saka jituwa a tsakaninku” (At-Tirmizi 1087). Wannan yana nufin soyayya a tsakaninsu zata dawwama. Kuma wannan kallon haƙƙi ne na namiji da mace, domin kowa ya san ɗayan kuma ya natsu da shi.

Aji

Aji yana nufin ya kasance akwai daidaituwa da kamanceceniya tsakanin ma'aurata a cikin abin duniya da yanayin zamantakewa. Wasu malaman sun jadadda wannan a matsayin sharaɗi ne na aure, wasu kuma sun tabbatar da cewa lalle abun la'akari da shi kawai shi ne addini da kyawawan halaye. Amma kuma babu shakka, rashin daidaituwa da kusantar juna a cikin dukiya, zamantakewa, da ilimi, a tsakanin ma'aurata yana iya lalata rayuwar aure tare da yin barazana ga rugujewarshi.

Yarda da amincewa

Bayan la’akari da kyakkyawan zaɓi, kuma lalle dole ne a yi aure tare da yarda da amincewa daga dukkan ɓangarorin biyu, ba tare da matsin lamba ko tilastawa daga kowa ba, ko da kuwa na kusa da su ne.

Musulunci ya yi adalci ga mata, kuma ya sharɗanta yarda da amincewarsu da miji. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Kada a aurar da bazawara har sai an nemi shawararta, kuma kada a aurar da budurwa sai an nemi izininta”. Suka ce: Ya Manzon Allah yaya ake samun izininta? Ya ce: "Da shirunta." (Al-Bukhari 5136, da Muslim 1419). Kuma a cikin kissar Khansa bintu Khidham al-Ansariyyah, “Mahaifinta ya aurar da ita tana bazawara, sai ta ƙi hakan, sai ta tafi wajen Manzon tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ya warware aurentan” (Bukhari 5138).

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa