Ɓangaren yanzu model
Darasi Ladduban neman aure
Neman Aure shi ne mutum ya sanar da waliyyin mace cewa lalle shi yanada buƙatar aurenta a bisa sunnar Allah da kuma sunnar ManzonShi (S. A. W).
Yana daga cikin ni'imomin Allah Maɗaukakin Sarki cewa Ya tsara laduban neman aure, waɗanda za su samar da gamsuwa, da kyakkyawan zaɓi da da natsuwa, kuma zasu taimakawa kowane daga ma'auratan da su kasance cikin fahimtar juna da jituwa da juna.
Daga cikin ladduban neman Aure
1- Kada ya nemi aure a bisa neman ɗan uwanshi musulmi, Manzon Allah (S. A. W) yace: «Kada mutum yayi ciniki a bisa cinikin ɗan uwanshi, kuma kada ya nemi aure a bisa neman ɗan uwanshi sai dai idan shi ya ba shi izini.(Bukhari: 5142, Muslim: 1412).
2- Kallon matar da ake so a aura, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace wa Mughirah Ɗan Shu’bah a lokacin da ya ke so ya auri wata mata: “Ka kalle ta, domin lallai hakanne mafi kusantar samun jituwa a tsakaninku” (At-Tirmizi 1087). Kallon wanda za a aura shima haƙƙi ne na mace, har ma wasu malamai suna ganin cewa mace ita tafi cancanta ma da kallon wanda yake son auranta. Ma'anar "don samar da jituwa a tsakaninku" shi ne: Domin haifar da soyayya mai ɗorewa a tsakaninku.
An karɓo daga Jabir Ɗan Abdullah, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Idan ɗayanku yana neman mace da aure, idan har zai iya ganin abin da zai ƙarfafa shi ya aure ta, to ya yi”. Ya ce: “Saboda haka na kasance ina neman wata budurwa, sai na kasance ina ɓuya ina kallonta har sai da na ga abin da ya ƙarfafa ni akan aurenta sai na aure ta.” (Abu Dawud 2082)
Daga cikin ladduban kallon wanda ake so a aura:
3- Daga cikin muhimman ladubban neman aure shi ne mace da namiji su yi zaɓi nagari, sannan su mayar da hankali kan ingantattun ginshiƙai waɗnda za su samar musu da gida wacce zata cika da natsuwa da jin daɗi da kuma kwanciyar hankali da yardan Allah.
4-Daga cikin ladubban neman aure akwai mutum ya kasance mai kwaɗayin ya auri mace mai haihuwa domin ƙara yawan zuriya ta gari, kamar yadda manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi nasiha da cewa: "Ku auri mata waɗanda kuke so kuma masu haihuwa, domin lallai ni zanyi alfahari da yawan adadinku a cikin al'ummai" (Abu Dawud 2050).
5- Neman shawara da neman zaɓi da kuma addu'a. Musulmi yana neman zaɓin Ubangijinshi Maɗaukaki ne a koda yaushe kuma yana roƙonShi, kuma yana yin shawara da ma'abota hankali da hikima a cikin kowane hali. Kuma lalle yanke hukuncin yin aure wani babban lamari ne mai muhimmanci a cikin rayuwar mutum, saboda haka ne ya kamata yayi abin da ya dace ta fuskar tuntuɓa da neman shawara da kuma addu’a.
6- Dole ne dukkanin ɓangarorin biyu su kasance masu gaskiya da amana wajen bayyana dukkan al'amura da yanayi, ta yadda babu wani aibi da zasu ɓoye, ko kuma suyi amfani da ƙarya da gangan ko yaudara wacce za ta shafi alaƙar da ke tsakanin ɓangarorin biyu a nan gaba bayan aure.
7-Kiyaye hukunce-hukuncen shari’a da suka shafi neman aure, kasancewar wannan alƙawarin aure ne kawai ba auren kansa ba. Don haka musafaha, kaɗaitaka, yin magana cikin sassauta zance ko sanya turare da ado ga mai neman aure, bai halatta ba.