Ɓangaren yanzu model
Darasi Haƙƙokin Yara
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Allah Ya cusawa zukatan iyaye maza da mata son samun zuriya masu lafiya da inganci. Wannan ita ce fatar babanmu Annabi Adamu da matarsa, Sallallahu Alaihi Wasallama. Allah Ta’ala ya ce: {Shi ne wanda Ya halicce ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, matarshi, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Kuma a lõkacin da ya rufe ta (ya sadu da ita), sai ta yi ciki mara nauyi, kuma ta ci gaba a cikinsa. Kuma a lokacin da ya yi nauyi, sai suka ƙirayi Allah Ubangijinsu cewa: "Idan Ka ba mu ɗa nagari, to, lalle ne mu muna daga masu godiya" [A'araf: 189]. Kuma cikan wannan burin kawai wata ni'ima ce da falala daga Allah Maɗaukakin Sarki. wanda ya wajaba a gode mi Shi a bisa hakan a koda yaushe.
Musulunci ya himmatu da lamarin zurriyya da abin da ya shafe su, kuma daga cikin abunda yake nuni zuwa ga wannan maganan a cikin Alkur’ani mai girma game da mahimmancin zuriya da ni'imar ƴaƴa shi ne lalle Allah Ya yi magana akan hakan bayan magana game da mulkin Allah a kan sammai da ƙasa. Allah Ta’ala ya ce: (Mulkin sammai da ƙasa na Allah ne kawai. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã bãyar da ɗiya mace ga wanda Yake so, kuma Yanã bãyar da ƴaƴa maza ga wanda Yake so. (49) Ko kuma Ya haɗa su maza da mãtã, kuma Yanã sanya wanda Yake so bakarãre (Wanda baya haihuwa). Lalle Shĩ Masani ne, Mai ĩkon yi. [Ash-Shura: 49-50] Kuma Allah Maɗaukakin sarki ya sanya zuriya a cikin adon rayuwar duniya, kamar yadda Shi Mai girma da ɗaukaka ya ce: (Dukiya da ƴaƴa ado ne na rayuwar Duniya) (Alkahfi: 64).
Shari’ar Musulunci ta ba ƴaƴa da tarbiyyarsu muhimmanci mai girman gaske, domin su ne ginshiƙin nan gaba, kuma ta hanyar nagartan su ne bautar Allah Maɗaukakin Sarki zata ci gaba a doron ƙasa, kuma za a raya kasa yadda Allah Maɗaukakin Sarki Ya keso. Allah Ta’ala ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani, ku tsare kanku da iyalanku daga wuta wadda makamashinta mutane ne da duwatsu} [Tahrim: 6]. Ali Allah Ya yarda da shi ya ce: Wannan yana nufin ku koyar dasu, kuma ku ladabtar da su. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda ya reni ƴaƴa mata guda biyu har sai sun balaga, ni da shi za mu zo ranar kiyama kamar haka,” sai ya haɗa yatsunshi wuri guda (Muslim 2631).
Haƙƙoƙin yara akan iyayensu
Waɗannan haƙƙoki sun haɗa da samar da wurin zama, da abinci, da abin sha, da tufafi, da kula da lafiya, da kashe kuɗi ga yara kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada. Kuma babu shakka Waɗannan haƙƙoƙi sun wajaba a kan uba idan har yana da iko.
Daga cikin mafi girman haƙƙokƙin ciki wadɗanda suka wajaba akan iyaye dangane da yaransu shi ne ta da su a bisa nagartacciyar turba wacce take kan ingantattun ginshiƙan addini, sai su koya musu Alkur'ani mai girma da ingantacciyar sunnar Annabi, da tarihin rayuwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma su rene su a bisa koyarwar musulunci ta hanyar aikata umarnin Allah da nisantar haninShi, da kuma lizimtar ababen dake cikinshi na kyawawan ɗabi'u, kuma wannan dukka yana cikin inuwar girmama Allah Mai girma da ɗaukaka da sonShi, da son AnnabinShi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da son addininShi da kuma shari'arShi.
Kyautatawa ga yara yana da matuƙar tasiri wajen tarbiyyar su da ci gaban hankalinsu, matukar hakan bai kai ga wuce gona da iri wanda zai kaisu ga lalaci a rayuwa ba. Saɓanin haka, rashin tausayi da kyautatawa ga yara, da mu'amalantarsu da muzgunawa da tozartawa, ko rashin kulawa da su, yana iya baƙanta musu ruhi, ya kashe hasken hankali a cikin zukatansu, ya jarabce su zuwa ga saɓawa iyaye, da tawaye haƙƙoƙinsu, da watakila ma fasadi da ɓarna.
Daga cikin haƙƙoƙin yara akan iyayensu akwai samar da yanayi na mutuntawa, natsuwa, kwanciyar hankali da ƙauna acikin iyali, ta yadda kada abar rigiman dake tsakanin iyaye ko manyan ƴan uwa ya cika gidan, domin hakan zai iya shafan ɗabi’un ƙananan yara ya kuma sanya su cikin ɗimuwa da tashin hankali.
Daga cikin manyan haƙƙoƙin yara akan iyayensu akwai sama musu abokai na gari da kuma rashin barinsu su cakuɗu da yara masu miyagun halaye ko munanan ɗabi'a domin hakan zaiyi tasiri a cikin halayensu.
Ya kamata iyaye su dinga bibiyan yanayin ƴaƴansu maza da mata, su kuma kula da halayensu da ayyukansu, kuma su ba su shawara, su faɗakar da su, su shiryar da su a duk lokacin da akwai buƙatan hakan, kuma daidaito yana da mahimmanci a cikin hakan, domin bai kamata shiryarwa da faɗakarwan ya kasance a koda yaushe ba, kaman yadda bai kamata su kasance akan kowana abu ba. Domin wannan na iya sa yaron ya gaji ya kuma ƙosa da saurare ko aiki da shawaran; saboda haka ya kamata iyaye su zabi lokuta da hanyoyin da suka dace don ba da shawara ga ƴaƴansu da kuma faɗakar da su.