Ɓangaren yanzu model
Darasi Manzon Allah (S. A. W) A Matsayin Miji
Yana daga cikin hikimar Allah da ya sanya ManzanninShi suka zama mutane, domin su zamto hujja akan mutane wajen koyi da su, da siffantuwa da siffofinsu da kuma aikata ayyuka irin nasu. Lalle babu shakka jin daɗin musulmi a duniya da lahira yana cikin bin littafin Allah da Sunnar Annabi (S.A.W) da tafiya a kan tafarkinsa ne. Don haka ya kamata musulmi ya kwaɗaitu wajen sanin tarihin rayuwar Manzon Allah (S.A.W) domin ya yi ƙoƙarin koyi da shi cikin dukkanin fannin rayuwarsa.
Rayuwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi gidansa da matansa ita ce babban abin koyi ga dukkan bil adama. Kuma shi ne abin koyi ga duk magidancin da yake sowa iyalansa kyakkyawar rayuwa a duniya da kuma rabauta da Aljanna a Lahira. Allah Ta'ala yana cewa: {Lallai kuna da abin koyi mai kyau ga Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana fatan haɗuwa da Allah da Ranar Lahira, kuma ya yawaita ambaton Allah} [Ahzab: 21].
Daga cikin kyawawan ɗabi'un Manzon Allah (S. A. W) tare da matanshi
Daga Aisha Allah Ya kara mata yarda, Lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Mafi alherinku shi ne mafi alheri ga iyalanshi, kuma ni ne mafi alheri ga iyalai na» (Attirmizi: 3895). Saboda haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarci maza daga cikin Al-ummarshi da su kyautata wa matansu, kuma yana yabawa wanda yake aikata hakan, sa'annan ya bayyana cewa lalle shi ne abun koyinsu a cikin hakan.
Himmatuwan Annabi (S. A. W) wajen kwantarwa matanshi hankalinsu da kuma biya musu buƙatunsu na shari'a
An karɓo daga A’isha Allah Ya yarda da ita ta ce: “Na ga Annabi (S. A. W) ya lulluɓe ni da mayafinsa alhalin ina kallon Habashawa suna wasa a masallaci, har sai da na gaji, don haka ku yi la’akari da shauƙin yarinya, mai kwaɗayin shagala. (Al-Bukhari 5236, Muslim 892). Don haka yin koyi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya haɗa da miji ya kasance mai hankalta, mai kula da sha’awar matarsa, da sanin buƙatunta na rai da zuciya, da biya mata su matuƙar basu saɓawa shari'a ba.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ƙirga wasan da mutum yake yi da iyalinsa a matsayin abin shagala da ya halatta, kuma ya kore cewa wasa ne abin zargi. Kuma tsira da amincin Allah sutabbata a gare shi ya ce: “Duk abin da ɗan Adam yake yi na shagaltuwa bashi da kyau sai dai abubuwa uku: Harbi da baka, da horar da dokinsa, da kuma wasa da iyalinsa, to waɗannan babu laifi a cikinsu.” (Ahmad: 17337).
Ya tabbata daga Aisha Allah Ya kara mata yarda cewa lalle ta kasance tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin tafiya, tace: Sai mukayi tsere da shi, sai na tsere mishi akan ƙafafuna, a lokackin da nayi jiki sai muka sake tsere sai ya tsere mini, sai yace: "Yanzu nima na rama" (Abu Dawood: 2578), Saboda haka Manzon Allah ya kasance yana wasa da matanshi kuma yana raha da su, domin kada rayuwar aure ta zamto mara daɗi mai gundura.
Hikimar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wajen mu'amala da matsalolin iyalai
Babu wani gida da ya kuɓuta daga wasu matsalolin da suke tasowa a tsakanin ma'abotansa, kuma Manzon Allah (S. A. W) ya ba mu misalai masu ban mamaki na yadda za a magance waɗannan matsalolin. An karɓo daga Anas Allah Ya yarda da shi ya ce: “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance tare da ɗaya daga cikin matansa, sai wata daga cikin Uwayen Muminai ta aika wani bawa da kwanon abinci, sai wacce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ke wurinta ta bugi hannun bawan, sai kwanon ya faɗi ya fashe. Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tara fasashshen kwanon ya zuba abincin da ya kasance a cikin kwanon a cikinshi, yana mai cewa: “Kishin Mahaifiyarku ya motsa". Sannan ya tsare bawan har sai da aka kawo kwano daga gidan matar da yake tare da ita. Sai ya ba wa matar da aka fasa kwanon ta kwanon da bai fashe ba, ya kuma ajiye wanda aka fasan a gidan matar da ta fasa. (Al-Bukhari 5225).
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance baya yawan damuwa da dabi’un matansa ko na mutanen gidansa. Ya kasance yana bin kowane yanayi da dabara da hikima. Ko da al’amarin zai iya haifar da rikici ko jayayya ne, to shi Sallallahu Alaihi Wasallam zai bi shi ta hanyar hikima da natsuwa da rashin ɓata rai, ta inda zai kwantarwa kowa da hankalinsa tare da tabbatar da adalci ga kowane ɓangare.
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yarda matarshi tayi fushi da shi ta kuma bayyana mishi hakan, kuma sai ya mu'amalance ta da kyautatawa da kuma tausayi, Daga Aisha Allah Ya kara mata yarda tace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Lalle ni nasan lokacin da kike yarda da ni da kuma lokacin da kike fushi da ni» tace: sai nace: ta yaya kake gane hakan? sai yace: «idan kin kasance kin yarda da ni to kina cewa: A'a na rantse da Ubangijin Muhammadu, idan kuma kina fushi da ni kina cewa: A'a na rantse da Ubangijin Ibrahim» tace: Hakane wallahi ya Manzon Allah, babu abunda nake kauracewa sai dai sunanka)(Bukhari: 5228, Muslim: 2439).
Kyakkyawan rayuwan Annabi (S. A. W) da matanshi
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana taimakon matanshi a cikin ayyukan gida; domin tausayi a gare su da kuma sauƙaƙa musu, kuma ya kasance daga cikin halayenshi (S. A. W) yana yiwa kanshi hidima a cikin ababen da suka keɓance shi.
Kuma haƙiƙa an tambayi Aisha Allah Ya kara mata yarda cewa: Menene Annabi ya kasance yana aikatawa a cikin gidanshi? tace: «ya kasance yana taimakon iyalanshi ne -tana nufin hidimar iyalanshi -idan lokacin sallah ya gabato sai ya fita zuwa sallah» (Bukhari: 676), Kuma tace a cikin wani hadisin: «Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana gyara takalminshi, yana ɗinke tufafinshi, kuma yana aiki a gidanshi kamar yadda ɗayanku yake aiki a gidanshi» (Ahmad: 25341).
Daga cikin salon nunawa mata soyayya
Ƙiransu da sunayen soyayya.
Yazo a cikin hadisi cewa lalle Annabi (S. A. W) ya cewa Aisha Allah Ya kara mata yarda: «Ya A'ish wannan Mala'ila Jibrilu ne yake miki sallama» (Bukhari: 3768). Kuma ya kasance yana ƙiranta da "Humaira".
Ciyarwar miji ga matarshi
Daga Sa'ad Ɗan Abi Waƙƙas Allah Ya kara mishi yarda lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace da shi: «Lalle duk abunda ka kashe sadaka ce, har abincin da zaka sanya shi a cikin bakin matarka» (Bukhari: 2742).
Miji ya bayyanawa matarshi cewa yana sonta
Daga Amru Ɗan Al'As Allah Ya kara mishi yarda, Lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tura shi a cikin wata runduna wacce ake ce mata "zatus salasil" yace: sai na same shi nace mishi: A cikin mutane wa kafi so? yace: «Aisha» (Bukhari: 3662), Muslim: 2384).
Sauraren labarinsu da himmatuwa da su
Daga cikin abunda yake nuna hakan kuma shi ne hadisin "Ummi Zar'i" mai tsawon nan, a cikinshi Aisha Allah Ya kara mata yarda ta hakaito labarin mata goma sha ɗaya waɗanda suka zauna kuma kowacce ta bada labarinta tare da mijinta, sai Annabi ya kasance yana sauraron Aisha har saida ta kammala zayyano mishi ckkakken abunda ya faru a tsakaninsu.
Adon Annabi (S. A. W) da kwalliyarshi ga matanshi
An tambayi Aisha Allah Ya kara mata yarda cewa: Da menene Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana farawa idan ya shiga gidanshi? tace: da Asuwaki" (Muslim: 253), kuma haƙiƙa ya tabbata daga gare ta cewa lalle tace: «Na kasance ina sanyawa Annabi mafi kyawun turare har sai da naga turare ya faranta mishi gashin kanshi da na gemunshi» (Bukhari: 5923).
Halaccin Annabi (S. A. W) ga matanshi
Daga cikin mafi bayyanan wannan halaccin abunda ya kasance na halin Annabi (S. A. W) tare da Khadijah Allah Ya kara mata yarda bayan rasuwanta da wasu shekaru, daga cikin hakan lalle Zainab ƴar Annabi (S. A. W) yayin da ta buƙaci fansan kanta daga Abul As -Kuma ya kasance ya aure ta a gabanin musulunci sai ya zamto bawa a ranar Badar- da sarƙan Khadijah Allah Ya kara mata yarda, sai hakan ya baiwa Annabi tausayi sosai sai yace: «Idan kuka ga dama ko sake mata bawanta kuma ku mayar mata da abunta» (Abu Dawood: 2692). kuma halaccinshi a gare ta ya kai matsayin da Aisha Allah Ya kara mata yarda tana kishinta kuma bata ganta ba, bata kuma rayu da ita ba, Daga Aisha Allah Ya kara mata yarda tace: Ban yi kishin wata daga cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kamar yadda nake kishin Khadijah ba, ban ganta ba amma kuma Annabi yana yawan ambatonta, sau da yawa ma zai yanka tunkiya sai ya sassarata gaɓa gaɓa ya rabawa ƙawayen Khadijah, sai nace mishi: Kaman babu wata mata a duniya sai khadija! sai yace: Haƙiƙa ta kasance kaza, da kaza, kuma na kasance ina da yara daga gare ta" (Bukhari: 3818, Muslim 2435).
Adalcin Annabi (S. A. W) a tsakanin matanshi
Darajawan Annabi (S. A. W) ga matanshi da kuma shawartansu
Kuma abu mafi bayyana daga hakan shi ne shawartan matarsa Ummu salama Allah Ya kara mata yarda da yayi a ranar Hudaibiyyah, a lokacin da ya bukaci musulmai da su yi yanka su kuma yi aski sai babu wanda ya tashi daga cikinsu, sai ya shiga wajen Ummu Salamah, sai ya ambata mata abinda mutane suka mishi, sai Ummu Salamah tace: Ya Manzon Allah shin kana son hakan? Ka fita sa'annan kada ka yiwa kowa magana daga cikinsu koda kalma guda ce, har sai ka soke rakumarka, kuma ka ƙira mai askinka ya maka aski, sai ya fita kuma bai yiwa kowa magana daga cikinsu ba har sai da ya aikata hakan; ya soke rakumarshi ya kuma kira mai askinshi yayi mishi aski, a yayin da suka ga hakan sai suka tashi suka soke ababen yankansu kuma sashinsu ya kasance yana aske sashi" (Bukhari: 2731).