Ɓangaren yanzu model
Darasi Haƙƙokin Mace a Musulunci
Addinin Musulunci na gaskiya tare da karantarwar Ubangiji da shiriyarsa, ya kula da mace Musulma, ya kiyaye mata mutuncinta, ya ɗauki nauyin tabbatar mata da ɗaukakarta da jin daɗin ta, ya samar mata da hanyoyin rayuwa mai daɗi, nesa da wuraren zato, fitintinu, sharri da fasadi. Kuma duk wannan yana daga cikin rahamar Allah Ta’ala ga mata musamman, da kuma al’umma gaba ɗaya. Kuma wannan kulawan yana da nau'i mai yawa.
Girmamawa da maɗaukakin matsayi
Musulunci ya tabbatar wa mata da martabarsu da mutuntakarsu, inda ya ba su matsayin da ya dace a kowane matsayi –a matsayin uwa, mata, ƴaƴa mata da sauransu. Ya yi umarni da kyautatawa, tausayi, da kulawa ta musamman ga mata. Bugu da ƙari, ya yi yaƙi da gurbatattun al'adun addinin da aka gada, da na hankali, da na zamantakewa waɗan da suke rage darajar mata, ko wulakanta su ko muzguna musu.
Umar Ɗan Khaɗɗab Allah Ya kara mishi yarda yace: “Wallahi a zamanin jahiliyya ba mu ɗauki mata da wani muhimmanci ba, har sai da Allah ya sauƙar da abin da ya sauƙar a kansu, kuma ya raba musu abin da ya raba musu na daga gado. (Bukhari: 4913, Muslim: 1479). Hasken Musulunci ya haskaka sama da shekaru 1400 da suka gabata, wanda ya ɗaukaka matsayin mata.Ya kawar musu da yawan zaluncin da mutane da kuma al’ummomi da dama suke yi musu, wanda ya haɗa da cewa mata ba su da ƴancin mallakar dukiya ko gado, kuma mace za a gaje ta ko a ƙona ta idan mijinta ya mutu, kamar yadda aka kasance ana kasuwancin su. Wannan al'ada ta ci gaba da kasancewa -a Ingila, misali - har zuwa farkon ƙarni na ashirin.
Adalci tsakanin mace da miji
Musulunci addinin Ubangijin talikai ne, Masani, Mai Adalci, Mai hikima. Yana daga cikin adalci da hikimar Allah ba Ya daidaita waɗanda suka bambanta, kuma ba ya bambanta masu kamanceceniya. Don haka ne muka ga shari’ar Musulunci ta sanya maza da mata su daidaita a cikin abin da suka yi kama da juna a cikinsa, ta kuma bambance tsakaninsu a cikin abunda suka bambanta a cikinsa. Wannan shi ya tabbatar da cewa haƙƙi da nauyin da ke kansu sun yi daidai da yanayin kowane daga cikinsu, da buƙatunshi, da ikonshi, da kuma halin da Allah ya halicce su da shi. Musulunci ya bai wa mata haƙƙinsu a kowane fanni kuma ya tabbatar da daidaito tsakanin su da maza ta ɓangarori da dama waɗan da suka haɗa da:
Asalin Halitta
Irin wulaƙancin da al'ummomin da suka gabata suka yi wa mata ya kai matakin da suka cire su daga cikin cikakkun ɗan adam. Aristotle ya ce: Mace mutum ne wanda ba cikakke ba, kuma yanayi ya bar ta a mataki mafi ƙasƙanci na tsanin halitta. Socrates ya kwatanta ta da itaciya mai guba. An yi babban taro a Roma inda suka yanke shawarar cewa mata ba su da rai ko dawwama, kuma ba za su gaji rayuwar lahira ba, ba su da tsarki, kuma kada su ci nama, ko suyi dariya, ko a basu damar yin magana. Dangane da Faransawa kuwa, sun gudanar da wani taro a shekara ta 586 miladiyya domin tattauna wata tambaya mai mahimmanci: Shin mace mutum ce ko a'a?! Shin tana da ruhi ko babu?! Idan kuma tana da ruhi, ruhin dabba ne ko ruhin mutum?! Idan kuma na mutum ne, shin tana kan matakin ruhin mutum ne ko ƙasa da shi?! A ƙarshe dai suka yanke shawarar cewa mata mutum ne amma an halicce su ne don su yi wa maza hidima. Amma Musulunci kuma duk da haka, ya tabbatar da daidaito tsakanin na miji da ta mace a asalin halitta. Allah Maɗaukaki yace: {Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta daga gare shi, matarshi, kuma Ya watsa daga gare su maza da mata masu yawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa wanda kuke rõƙon jũna da shi, da mahaifu. Lallai ne Allah Ya kasance a kanku, Mai gani ne.} [Nisa: 1].
Musulunci ya daidaita tsakanin maza da mata ta fuskar wajibai na addini da lada da sakamakonsu a duniya da lahira. Allah Ta'ala yana cewa: {Duk wanda ya aikata aiki na ƙwarai, namiji ne ko mace, alhali yana mumini, to, lalle ne, za mu raya shi rayuwa mai kyau, kuma za mu ba su sakamakonsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa} [Nahl: 97]. Kuma Allah Ta'ala Ya sake cewa: {Kuma duk wanda ya aikata aiki na ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhali yana mumini, to, waɗannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a zalunce su ba, ko da tsagin dabino ne.” [Nisa: 124]. An tambayi Manzon Allah (SAW) game da mutumin da ya sami jiƙa (A wandon shi) amma bai tuna cewa ya yi mafarki ba. Sai ya ce: “Zai yi wanka". An kuma tambaye shi game da mutumin da ya yi imanin cewa ya yi mafarki amma bai ga ruwa ba. Sai ya ce: “Babu wanka a gare shi”. Sai Ummu Sulaim ta ce, “Mata ma suna ganin haka, shin akwai wanka akansu? Sai ya ce: “Eh, mata ai takwarorin maza ne". (Sunan Abu Dawud 236).
Kuma farkon wanda ya fara imani da saƙon Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ita ce mace wato uwar muminai Khadija Allah ya kara mata yarda. Kuma akwai mata a cikin ayarin farko na hijira zuwa Habasha, kuma suna cikin tawaga ta farko da ta zo daga Yathrib, suka yi mubaya’a ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Mata a tarihin Musulunci sun ba da misalai masu haske, waɗanda aka san su da kyawawan halaye, da ɗimbin iliminsu, da fahimtar sakƙon Musulunci. A lokuta da dama sun kasance jagaba a wannan fanni, domin musulmi sun koyi abubuwa da dama na addininsu daga waɗansu mata musulmai masu ilimi da suka yi gaba a fannin ilimi da karantarwa, musamman Uwar Muminai Aisha, Allah ya kara mata yarda.
Kuma mata suna tarayya da maza wajen ibadar jama’a, a bisa fuskar wajabci, ko mustahabbi, ko halacci, kamar Umrah, da Hajji, da Sallar roƙon ruwan sama, da Sallar Eidi, da Sallar Juma’a da ta Jam’i. Kuma an umarce su da su gayyaci wasu zuwa ga Musulunci, kuma suyi umurni da kyakkyawa kuma suyi hani daga munana, da wasu ababe da dama waɗan da suke bayyane wajen nuna daidaito tsakanin miji da mace a cikin wajibai na shari'a. Kuma babu wani abu da aka keɓe daga wannan sai abin da ke da alaƙa da bambancin halitta a tsakaninsu.
Yayin da Musulunci ya kafa ka'idar daidaito a cikin wajibai a matsayin babban ka'ida, sai kuma ya yi la'akari da bambancin yanayi tsakanin na miji da ta mace, da sakamakon da ya haifar na bambancin ayyuka. Sai ya tsara waɗannan ayyukan kuma ya sanya kowa a daidai wurinsa da ya dace, wanda hakan kuma shi ne abunda zai kawo jin daɗin rayuwa. Namiji ne ke da alhakin ciyar da mace da ƴaƴa, kuma dole ne akanshi ya kiyaye su ya kuma kula da duk wani lamuran iyali. Mace ce ke da alhaƙin kula da gidanta da mijinta da ƴaƴanta, kuma tana da wasu nauyin da ya wajaba akanta da ta ɗauke su.
Musulunci ya ba wa mata haƙƙinsu na zamantakewa, da na mutumtaka, kuma waɗannan haƙƙokin an baiwa mata ne tun farkon zuwan addinin Allah da shekaru 1400 da suka gabata, kuma tun kafin ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama da na fararen hula su fara ƙira zuwa gare su a cikin wannan zamani.
Haƙƙokin mata na cikin Al-ummah da na zamantakewa
Haƙƙokin mace a cikin zamantakewa da aure
Waɗan nan ƴan misalai ne kawai don bayyana wasu daga cikin haƙƙokin mata a Musulunci, amma haƙƙokin da shari’ar Musulunci ta ba mata suna da yawa.