Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Ƙiran Sallah

Allah Ya shar'anta wa musulmai ƙiran sallah; domin ƙiran mutane zuwa ga Sallah, da kuma sanar dasu shigan lokacinta. A cikin wannan darasin zaka san yadda ake ƙiran sallah da tayar da iƙama.

  • Sanin siffar ƙiran sallah
  • Sanin siffar iƙama
  • Sanin falalar nanata kiran sallah a bayan ladan. 

Ƙiran Sallah

Allah Ya shar'anta wa musulmai ƙiran sallah domin ƙiran mutane zuwa ga Sallah da kuma sanar dasu shigan lokacinta.

Kuma an shar'anta ikama domin sanar dasu lokacin shiga sallah da kuma fara ta.

Yaya aka shar'anta ƙiran sallah?

Musulmai sun kasance yayin da suka taho zuwa Madinah suna taruwa suna tsayar da sallah, kuma babu wanda yake kira daga cikinsu, wata rana sai suka tattauna akan haka, sai wasunsu sukace: Mu riƙi ƙararrawa kamar na Nasara, wasunsu kuma suka ce muyi amfani da ƙaho irin na yahudu, sai Umar yace: Shin ba zaku tura wani daga cikinku ya kira sallah ba? Sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ya Bilal ka tashi ka ƙira mana sallah") Bukhari: 604, Muslim: 377).

Hukuncin ƙiran Sallah da Iƙama

Ƙiran sallah da iƙama wajibi ne akan jama'a banda mutum ɗaya, amma kuma idan suka barsu da gangan sallar su ta inganta sai dai sun aikata abunda ba dai dai ba.

Ta yaya ladan zai ƙira sallah?

An shar'anta ƙiran sallah da ɗagaggen sauti kuma kyakkyawa domin mutane suji su taho zuwa ga Sallah.

Sigar yadda ake kiran sallah

Ka saurari ƙiran sallah

Kuma ladani zai ƙara faɗin:(Assalatu khairun minan naum, Assalatu khairun minan naum) a cikin sallar Asuba, bayan faɗin: (Hayya alal falalh).

Sigar yadda ake iƙama

Nanatawa a bayan ladan

Kuma anso ga wanda yaji ƙiran sallah da ya nanata a bayan ladan, sai ya faɗi kwatankwacin abunda ladan yake faɗa, sai idan ladan yace: (Hayya alas salat) ko (Hayya alal falah) sai shi kuma yace: (La haula wala ƙuwwata illa billah). Sa'annan bayan an gama ƙiran sallan sai yace:(Allahumma Rabba hazihid da'awatut Tammah, wassalatul ƙa'imah, Ãti muhammadan alwasilata walfadilah, wab'ashu maƙaman mahmudan allazi wa'adtah).

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa