Ɓangaren yanzu model
Darasi Natsuwa a cikin sallah
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ita ce haƙiƙanin sallah da asalinta, kuma ma'ananta shi ne zuciyar mai sallah ta kasance tare da Allah a cikin sallah da tsanaki, da ƙanƙan da kai tare da mayar da hankali akan ababen da yake faɗa na daga karatun Alkur'ani da Addu'o'i da kuma ambaton Allah.
Natsuwa a cikin sallah tana daga cikin mafifitan ibadu da kuma manya-manyan biyayya ga Allah; saboda hakane ma Allah Ya tabbatar a cikin littafinShi cewa lalle tana daga cikin siffofin muminai, Kamar yadda Allah Ta'ala Yace: (Haƙiƙa muminai sun rabauta * Waɗanda suke da Natsuwa a cikin sallarsu)(Almuminun: 1- 2).
Kuma duk wanda yake natsuwa a cikin sallah babu shakka ya ɗanɗana daɗin ibadah da kuma imani, saboda hakane Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa: "Kuma an sanya sanyin idanu na a cikin sallah" (Annasa'i: 3940). Ma'anan sanyi idanu shi ne matiƙar murna, da farin ciki, da jin dadi.
Ababen da suke taimakawa wajen samun natsuwa a cikin sallah.
Kuma hakan yana kasancewa ne da sammako zuwa gare ta ga maza, da sanya tufafi mai kyau wanda ya dace, da tafiya zuwa gare ta cikin tsanaki da natsuwa.
Kada yayi sallah alhali a gabanshi akwai abunda zai iya shagaltar dashi na daga hotuna, da ababen shirme, ko kuma yana sauraron abunda zai shagaltar dashi na daga sautuka, kuma bazai fara sallah alhali yana matse da fitsari ko bayan gida ba, ko yana jin yunwa ko yana jin kishin ruwa alhali kuma an kawo abinci da abun sha a kusa dashi, domin waɗannan ababen da aka ambata zasu shagaltar da ƙwaƙwalwan mai sallah daga babban lamarin dake gabanshi wanda shi ne sallah da kuma ganawa da ubangijinshi.
Kuma lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana samun tsanaki a cikin ruku'unshi, da sujjadarshi, har sai kowana gaɓa ya miƙe yadda ya kamata, kuma ya umarci wanda bai kyautata sallarshi ba da ya natsu a cikin gudanar da ayyukan Sallah gaba ɗayanta, kuma ya hana gaggawa a cikinta, ya kuma kamanta hakan da yadda hankaka yake cakan hatsi a ƙasa.
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake sata daga sallarshi", Sai sahabbai sukace: Ta yaya zaiyi sata daga sallarshi ya manzon Allah? sai yace:" baya cika ruku'unta da sujjadarta" (Ahmad: 22642). Kuma duk wanda baya yin sallarshi cikin tsanaki ba zai taɓa samun natsuwa ba, kuma wannan gaggawan zai tafi da ladan sallar.
Sai ya tuna girman Mahalicci da ɗaukakarShi da kuma rauninshi da ƙasƙancinshi da kuma cewa lalle shi yana tsaye ne a gaban Ubangijinshi yana ganawa da shi kuma yana roƙonshi, yana mai ƙanƙan da kai mai karaya, kuma ya tuna abunda Allah Ya tanadawa muminai a lahira na daga lada da abunda Ya tanadawa mushirkai na daga gwale-gwale, kuma ya tuna cewa zai tsaya a gaban Allah ranar lahira kamar hakan.
Saboda an sauƙar da Alkur'ani ne domin a dinga tuntuntuni a cikin ayoyinshi, Allah Ta'ala Yace: (Wannan littafi ne mai albarkah wanda Muka sauƙar da shi zuwa gare ka domin suyi tuntuntuni a cikin ayoyinshi kuma masu hankali su wa'azta) (Sad: 29).