Ɓangaren yanzu model
Darasi Sallar Jumma'a
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Allah Ya farlanta wata sallah a ranar jumma'a a lokacin sallan azahar, kuma tana daga cikin manya-manyan ibadu a musulunci, Ya kuma tabbatar da wajabcinta, musulmai suna taruwa sau ɗaya a cikin sati, su saurari wa'azi da faɗakarwa waɗanda limamin jumma'a zai gabatar musu, sa'annan sai su sallaci sallar jumma'a.
Falalan ranar jumma'a
1- Lalle Allah Ya keɓance Al-ummar Annabi da ita koma bayan wasunsu daga cikin Al-ummu, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Allah Ya ɓatar da waɗanda suka rigaye mu akan jumma'a, sai yahudawa suka kasance suna da ranar asabar, nasara kuma suka kasance suna da ranar lahadi, sai Allah Yazo damu daga baya, sai kuma Ya shiryar damu zuwa ga ranar jumma'a" (Muslim: 856).
2. Lalle Annabi Adam alaihis salam an halicce shi ne ranar jumma'a, kuma alkiyama zata tsaya ne a ranar jumma'a, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Mafi alherin yinin da rana ta fito a cikinshi shi ne ranar jumma'a, a cikinta ne aka halicci Annabi Adam, a cikinta aka shigar da shi Aljannah, a cikinta aka fitar da shi daga gare ta, kuma alkiyama ba zata tashi ba sai a ranar jumma'a" (Muslim: 856).
Akan waye jumma'a take wajaba?
Anaso musulmi yayi wanka gabanin lokacin sallar jumma'a, da sammako zuwa masallaci kafin a fara huɗuba, da fesa turare, da sanya kyawawan tufafi.
Musulmai suna taruwa a masallacin jumma'a, sai liman ya gabace su, ya hau kan Mimbari, yana mai fiskantar musulmai, sai yayi musu huɗuba guda biyu, yana mai raba tsakaninsu da ƙaramar zama, yana tunatar da su da tsoron Allah a cikinsu, kuma yana gabatar musu da nasihohi, da wa'azi yana kuma karanta musu ayoyi.
Ya wajaba akan musulmai da su saurari huɗuba, kuma magana ko shagaltuwa da wani abu yayin huɗuba ya haramta domin zai hana su amfanuwa da huɗubar, koda ace kuwa wasa da sallaya ne ko tsakuwa ko yashi ba aso.
Wanda sallar jumma'a ta wuce shi
Wanda yayi jinkirin zuwa sallar jumma'a
Duk wanda sallar jumma'a bata wajaba akanshi ba kaman mace da matafiyi, to lalle jumma'a tana inganta daga garesu idan suka sallace ta tare da jama'an musulmai, sai sallan azahar kuma ta faɗi daga gare su sakamakon sallan jumma'ar da sukayi tare da jama'an musulmai.
Wajabcin halartan jumma'a
Da menene Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsoratar da waɗanda suke saɓa zuwa sallar jumma'a?
Karɓaɓɓen uzurin barin sallar jumma'a ga wanda ta wajaba a gare shi shi ne: Duk wani abunda zai haifar da wata wahala mai tsanani wacce ba a saba da ita ba, ko ake tsoron cutarwa daga gare ta, wacce zata iya cutar da rayuwar musulmi ko lafiyarshi.