Ɓangaren yanzu model
Darasi Azumin Nafila
Allah Ya farlanta azumin wata ɗaya a shekara amma kuma Ya kwaɗaitar akan Azumin wasu ranaku ga wanda ya samu iko kuma yake da daman aikata hakan, domin neman ƙarin lada da sakamako, daga cikin waɗannan azumin:
Kuma shi ne ranan goma ga watan Muharram; watan farko a cikin kalandar musulunci, Kuma ita ce ranar da Allah Ya tsiratar da AnnabinShi Musa alaihis salam daga fir'auna, sai musulmi ya azumce shi domin godiya ga Allah abisa tsirar Musa alaihis salam da kuma domin bin sunnar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi saboda shi ma ya azumce shi, Kuma yayin da aka tambaye shi (S. A. W) akan azumin ranan Ashura sai yace: "Yana kankare kura-kuran shekarar da ta gabata" (Muslim: 1162). kuma anso da ya azumci ranar da take gabaninshi, ranan tara kenan, lalle yazo daga Annabi (S. A. W) yace: «Idan har na kai shekara mai zuwa lalle zai azumci ranar tara" (Muslim: 1134).
Kuma shi ne ranar goma ga watan Zul-Hijjah, watan goma sha biyu a jerin kalandar musulunci, a cikin wannan ranar ne Alhazan ɗakin Allah suke taruwa akan dutsen Arafah suna masu roƙon Allah Mai girma da ɗaukaka suna masu ƙanƙan da kai zuwa gare Shi, kuma shi ne mafificin ranakun shekara, kuma an shar'antawa waɗanda basu je aikin hajji ba azumtarshi, kuma a yayin da aka tambaye shi (S. A. W) akan azumin ranar Arafah sai yace: "tana kankare kura-kuran shekarar da ta gabata da kuma mai zuwa" (Muslim: 1162).
Shawwal shi ne wata na goma a jerin kalandar musulunci, Manzon Allah (S. A. W) yace: "Duk wanda ya azumci ramadan sa'annan ya bishi da shida na daga shawwal, zai kasance tamkar wanda yayi azumin shekara" (Muslim: 1164)
Daga Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda yace: "Masoyina yayi mini wasiyya da ababe guda uku waɗanda kada na barsu har sai na mutu: Azumin ranaku uku a cikin kowana wata, da sallar Duha, da bacci akan witiri" (Bukhari: 1178, Muslim: 721)