Ɓangaren yanzu model
Darasi Eidi
Eidi yana daga cikin alamun bautan Allah na zahiri
Eidi a cikin musulunci shi ne Ranar da musulmai suke bayyana farin ciki a cikinshi domin kammala ibadah don nuna godiya ga Allah ta'ala a bisa shiriyarShi, da datarwarShi ga ibadah, kuma an shar'anta shigar da farin ciki cikin zukatan mutane gaba ɗaya a cikin ta, da sanya mafi kyawun tufafi, da kyautatawa mabuƙata, da hutar da rai da dukkanin ababen da suke halal kaman bukukuwa da shugulgula waɗanda suke shigar da murna cikin zukatan kowa da kowa, da kuma tunatar dasu ni'imar Allah akansu.
Musulmai suna da Eidi guda biyu waɗanda suke bukukuwa a cikinsu, kuma baya halatta da a keɓance wata ranan da mutane zasu dauke ta a matsayin ranar Eidi koma bayan ranaku biyun nan, kuma waɗannan ranakun su ne:
Ita ce sallar da musulunci ya ƙarfafa ta ya kuma kwaɗaitar da musulmai maza, da mata ,da yara akan fita zuwa gareta. lokacinta shi ne daga ɗagowan rana daidai da mashi a sama bayan fitowarta a ranar Eidi har zuwa zawalinta (Ma'ana gusewanta daga tsakiyan sararin sama).
Sallar Eidi raka'a biyu ne, Limami yana bayyana karatu a cikinsu, kuma zaiyi huɗuba guda biyu bayan sallah, kuma an shar'anta ƙara kabbarori a farkon kowace raka'ah a sallar Eidi, sai liman yayi kabbara guda shida gabanin fara karatu a raka'ar farko koma bayan kabbarar harama, kuma zaiyi kabbara biyar a raka'a ta biyu banda kabbarar tasowa daga sujjada.
Na daga yara, da manya, da maza, da mata da dukkanin hanyoyin da suke na halal, da sanya mafi kyawun tufafi, da kuma bautawa Allah da ci da sha a yini wannan ranar, saboda haka ne ma aka haramta azumtar ranar Eidi.
An shar'anta kabbara a cikin ranar Eidin sallar azumi; domin bayyana farin ciki da ranar Eidin, da kuma kammala azumin ramadan mai albarkah, da kuma godewa ni'imar Allah akanmu a bisa shiryar damu da Yayi zuwa ga azumi, Allah Ta'ala Yace: (Domin ku cika lissafi kuma ku girmama Allah a bisa abunda Ya shiryar daku zuwa gare shi kuma domin ku gode) (Albakara: 185). Kuma an shar'anta kabbarori a cikin Eidin sallar laiha ma domin bayyana farin ciki, da gudanar da faralin hajji ga Alhazai, da kuma datarwa ga ayyukan alheri a cikin kwanaki goma na Zul-Hijjah ga Alhazan da kuma sauran musulmai, Allah Ta'ala Yace: yayin ambaton ababen da ake yankawa a laiha:(Namansu da jininsu basa riskan Allah sai dai tsoron Allanku ne yake riskanShi, kaman hakane muka horar muku dasu, domin ku girmama Allah a bisa abunda Ya shiryar daku, kuma ka yiwa masu kyautatawa albishir) (Alhajji: 37).
Yadda ake kabbarorin Eidi
Kuma an shar'anta wa maza ɗaga muryansu ta yadda ba za su cutar da mutane ko su takura musu ba, mata kuma zasu sauƙe sautinsu da su.