Ɓangaren yanzu model
Darasi Eidin sallar azumi da Eidin sallan Laiha
Eidin Sallan Azumi
Menene aka shar'anta a ranar Eidin sallan Azumi?
Allah Ya farlantawa duk wanda ya mallaki sama da abunda yake buƙata na daga abinci a ranar eidi da darenta da ya fitar da kimanin mudu ɗaya na daga abincin mutanen garin na daga alkama ko shinkafa, ko masara, ko dabino ya baiwa talakawa da miskinai na daga cikin musulmai, domin kada a samu wani mabuƙaci a ranar Eidi.
Daga faɗuwan ranar ranan ƙarshe na daga watan Ramadan har zuwa lokacin sallan Eidi, kuma ya halatta da a gabatar da ita kafin ranar Eidi da kwanaki biyu ko da kwana ɗaya.
Mudu ɗaya na daga abincin mutanen garin na daga alkama ko shinkafa ko masara ko dabino da makamantanau, Mudu kuma shi ne kwatankwacin kilo guda, amma kuma ƙaddara shi da ma'auni yafi domin gane asalin kimarshi, kuma shi ne kaman kimanin nauyin kilo giram 3
Tana wajaba ne akan wanda ya mallaki fiye da abunda yake buƙata na daga abinci wanda zai wadatar da shi da kuma waɗanda suke ƙarkashin shi kaman matarshi da yaranshi a ranar eidi ko a daren shi, kuma anso da a fitarwa jinjirin dake cikin mahaifiyarshi, sai a fitarwa kowana mutum mudu guda na daga abincin mutanen garin, wato kilo giram 3 a taƙaice.
Hikimar dake cikin fitar da zakkan fidda kai
Kuma shi ne Eidi na biyu ga musulmai, yana kuma zuwa ne a ranar goma ga watan Zul Hijjah (Wata ta goma sha biyu a cikin jerin kalandar musulunci), kuma lalle an tara falala masu yawa a cikinshi, daga cikinsu:
1. Yana daga cikin mafifitan kwanakin shekara
A cikinshi ne ake aiwatar da manya-manyan ayyukan hajji da waɗanda sukafi kowanne mahimmanci da darajah, kaman ɗawafi a kewayen Ka'abah, da yanka hadaya,, da jifan Shaiɗan.
Menene aka shar'anta a cikin ranar Eidin laiha?
Ita ce ababen da ake yankawa na daga raƙuma, ko shanaye, ko raguna, ko awaki domin neman kusanci zuwa ga Allah Ta'ala a ranar Eidin laiha daga bayan sallar Eidi har zuwa faɗuwan ranan goma sha uku na daga watan Zul Hijjah, Allah Ta'ala Yace: (Kayi sallah ga ubangijinka kuma kayi yanka) (Alkausar: 2). Kuma haƙiƙa an fassara sallah anan da sallar Eidi, yanka kuma da laiha.
Hukuncinta:
Kuma an shar'antawa wanda yayi niyan laiha da kada ya cire wani abu daga gashinshi da faratunshi da kuma fatarshi; tun daga ganin jaririn watan Zul Hijjah har zuwa lokacin yanka.
Sharruɗan dabbobin da za ayi laiha dasu
Kuma su ne Raguna da Awaki, ko Shanaye, ko Raƙuma, kuma laiha bata inganta da wasunsu na daga dabbobi ko tsuntsaye. kuma tinkiya ko akuya ta isarwa mutum da mutanen gidanshi, kuma mutane bakwai zasu iya tarayya a cikin shanu ɗaya ko rakumi ɗaya.