Ɓangaren yanzu model
Darasi Hunturu da Sallah da kuma Azumi
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Idan sanyi ya tsananta a cikin hunturu to za a duba: Idan har tsananin sanyin ba zai iya hana mutane fitowa zuwa Sallah ba to lalle ƙiran sallah zai kasance kaman yadda yake.
Mutane suna kunna wuta a lokacin hunturu, wataƙila ma tana kasancewa a ɓangaren alkiblan sallar, amma abin da yafi shi ne kada wutar ta kasance ta ɓangaren da ake sallar, domin gujewa kama da Majusawa waɗanda suke bautawa wuta, kuma zata dinga ɗaukan hankalin mai sallah, amma kuma idan canza mata wuri zai ba da wahala, to babu damuwa.
Amma kuma abu mai ɗumama wuri wanda babu harsunan wuta a tattare da shi, to babu matsala wajen yin sallah zuwa gare shi.
Haɗa tsakanin Salloli biyu
Daga cikin uzurorin da suke bayar da damar haɗa sallah kuma waɗanda suke yawaita a cikin hunturu: Ruwan sama, kuma wasu malamai suna ƙarawa da: Iska mai tsananin sanyi, ko sanyi mai tsanani, ko ƙanƙaran dake rufe hanyoyin wucewa, ko taɓon da yake cika hanyoyi.
Abun nufi da uzurorin da suke bada daman haɗa sallah: Su ne yanayin da zai bawa mutane wahalan sake fitowa zuwa masallaci domin sallan jama'a, sai a ba da izinin haɗa sallah, koma bayan ruwan sama mai sauƙi wanda ba zai hana mutane daga fita shaƙatawa ko biyan buƙatunsu ba.
Wanda ba ya sallan jam'i -Kaman mace da mara lafiya da wanda yake sakaci da sallar jam'i- ba zai haɗa tsakanin salloli ba, domin bai da buƙatan haɗawa, to sallah akan lokaci abun buƙata ne a gare shi, haka nan ba a haɗa sallah idan uzuri ya gushe gabanin ya sallaci sallah ta biyun.
Yayin haɗa salloli biyu ƙiran sallah guda ɗaya ya wadatar, amma za a tayarwa kowana sallah iƙama, kuma zai sallaci sunnoni ratibai a bayansu, kuma zaiyi azkar na sallah a bayansu.
Ana samun saɓani a masallatai da yawa dangane da uzurin da ke ba da damar haɗa sallah, amma kuma asalin lamari shi ne limami shi ke da alhaƙin wannan, sai yayi ijtihadi idan har ya kasance mai ilimi ne kuma ya shawarci wanda yake da ilimi, idan kuma halaccin hakan bai bayyana a gare shi ba, to ba zai haɗa ba, kuma bai kamaci mutanen masallaci da suna jayayya akan hakan ba.
Yazo a cikin wasu asari cewa: "Hunturu mashayan mumini ne; domin an taƙaita mishi yininshi don yayi azumi, kuma an tsawaita mishi darenshi don yayi sallah" Baihaƙi ne ya fito da shi a cikin "Assunan Alkubra" (8456), Kuma an saka mishi suna mashaya ne domin yana shaƙatawa a cikinshi da motsa jiki wajen ibadah, domin ana iya azumtan ranar lokacin hunturu ba tare da wahalan yunwa ko ƙishirwa ba.
Kuma yazo a cikin wani asarin cewa: «Azumi a cikin hunturu ganima ce mai sanyi» Ahmad ne ya fitar da shi (18959), Umar Allah Ya kara mishi yarda yace: «Hunturu ganimar bayin Allah masu ibadah ne», Abu Na'eem ne ya fitar da shi a cikin "Alhilyah" (1 /51).