Ɓangaren yanzu model
Darasi Gamammun hukunce-hukuncen waɗanda suke yawaita a lokacin hunturu
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ya kamata a kashe wutar da ake yawan kunna ta a lokacin hunturu gabanin bacci, hakama na'urori masu ɗumama wuri domin zasu iya haifar da gobara, Daga Abu Musa Al-Ash'ari Allah Ya kara masa yarda yace: Gobara ta cinye wani gida akan mutanenta a Madinah a cikin dare sai aka baiwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi labarinsu, sai yace: «Lalle wannan wutar maƙiyarku ce, idan zakuyi bacci toh ku kashe ta akanku» (Bukhari: 6294, Muslim: 2016), a cikin wani hadisi kuma: "Kada ku bar wuta a gidajenku yayin da kuke bacci" (Bukhari: 6293, Muslim: 2015).
1- Zai tuna ikon Allah Mai girma da ɗaukaka wajen yadda Yake sarrafa iska; Mai sanyi da mai zafi, mai sauƙi da mai tsanani, ta kudu da ta arewa, wacce take ɗauke da ruwa da bushashshiya, da wanin haka, Allah Maɗaukakin Sarki Yace: (Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da sãɓãwar dare da yini, da jirãge wadaɗnda suke gudana a cikin tẽku (ɗauke) da abin da yake amfãnin mutãne, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta, kuma Ya wãtsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da jũyãwar iskõki da girgije hõrarre a tsakãnin sama da ƙasa; haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali) (Albakara: 164).
Daga Abdullahi Ɗan Zubair: Lalle ya kasance idan yaji tsawa sai ya bar hira, kuma yace: "Tsarki ya tabbata ga wanda tsawa take tasbihi da gode maSa, Mala'iku kuma domin tsoronShi" kuma wannan lafazin yazo a cikin Alkur'ani: {Kuma arãdu (Tsawa) tanã tasbĩhi game da gõde Masa, da malã'iku dõmin tsoronsa. Kuma Yanã aiko tsãwawwaki, sa'an nan Ya sãmi wanda Yake so da su alhãli kuwa sũ, sunã jãyayya a cikin ( al'amarin ) Allah kuma shĩ ne mai tsananin hĩla} (Arra'ad: 13).
Allah Ya wasafta ruwan sama da cewa lalle shi mai albarkah ne. Allah Maɗaukakin Sarki Yace:(Kuma Mun sauƙar da ruwa mai albarkah daga sama) (Suratu Ƙaf: 9), Kuma daga cikin ababen da akeyi yayin sauƙan ruwan sama: 1- Mutum zai yaye wani ɓangaren jikinshi domin ruwan ya taɓa, an karɓo hadisi daga Anas Allah Ya kara mishi yarda yace: Ruwan sama ya same mu alhali muna tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace: sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ɗan yaye tufafinshi domin ruwan ya taɓa shi, sai mukace: Ya Manzon Allah me yasa ka aikata hakan? sai yace: Lalle shi bai daɗe da barin ubangijinshi Maɗaukaki ba) (Muslim: 898)
2- Zai yi Addu'a, Kuma yazo a cikin da yawa daga asari cewa lalle lokacin sauƙan ruwan sama lokacin amsa addu'a ne.
Addu'o'i yayin sauƙan ruwan sama da bayan sauƙanshi.
Idan ruwan sama yayi tsanani kuma akaji tsoron kada ya cutar, an so mutum yayi addu'a yana mai ɗaga hannayenshi, kuma daga cikin addu'ar da tazo a cikin hakan. "Ya Allah a kewayenmu ba a kanmu ba, ya Allah akan tsaunuka da duwatsu, da ƙoramai da kuma matsiran bishiyoyi".(Bukhari: 1014, Muslim: 879).