Ɓangaren yanzu model
Darasi Ziyaran Birnin Annabi
Haƙiƙa darajan Madinah mai albarkah ta ɗaukaka sakamakon hijiran da Annabi (S. A. W) yayi zuwa gare ta, har aka fifita ta a bisa sauran wurare koma bayan Makkah Almukarramah, kuma an shar'anta ziyaranta a kowana lokaci ba sai a lokutan aikin hajji ba, Annabi (S. A. W) yace: "Ba a niƙa gari saidai zuwa masallatai guda uku: Masallacin Harami, da Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Masallacin Ƙudus" Bukhari: 1189, Muslim:1397). Kuma Madinah tana da falala masu yawa, daga :cikinsu akwai masu zuwa
Ya kasance farkon abunda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aikata bayan zuwarsa garin Madinah shi ne gina Masallacin Annabi mai darajah wanda ya kasance cibiyar ilimi da da'awa da kuma yaɗa alheri a tsakanin mutane. Kuma wannan masallaci mai albarkah yana da falala mai girman gaske, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Sallah guda ɗaya a wannan masallacin nawa tafi salloli dubu a cikin waninshi sai dai Masallacin Harami" (Bukhari: 1190, Muslim: 1397).
2. Kuma lalle ta kasance amintacciyar harami ne
Haƙiƙa Annabi (S.A.W) ya mai da ita harami da wahayi daga Allah, saboda haka ba a zubar da jini a cikinta, kuma ba a ɗaukan tokobi a cikinta, kuma ba a tsoratar da kowa a cikinta, kuma ba a sare bishiya a cikinta da wanin haka na daga ababen da suke shiga cikin haramta ta, Manzon Allah (S. A. W) yace: "Ba a yanke ciyayinta, kuma ba a sare bishiyoyinta, kuma ba a ɗaukan tokobi domin yaƙi a cikinta" (Abu Dawood 2035, Ahmad: 959).
3. Tana da Albarkah cikin Arziƙi, da ƴaƴan itace kuma tana da daɗin rayuwa:
Annabi (S. A. W) yace: "Ya Allah Ka saka mana albarkah a cikin ƴaƴan itatuwanmu, kuma Ka saka mana albarkah a cikin garinmu, kuma Ka saka mana albarkah a ma'auninmu, kuma Ka saka mana albarkah a cikin mudunmu, Ya Allah lalle Annabi Ibrahima bawanKa ne kuma badaɗenKa ne kuma AnnabinKa ne, kuma lalle ni ma bawanKa ne kuma AnnabinKa ne, kuma lalle shi ya roƙe ka akan Makkah, kuma lalle ni ina roƙonKa akan Madinah da kaman abunda ya roƙe Ka a Makkah da kuma kwatankwacin shi tare da shi" (Muslim: 1373).
4. Allah Ya kare ta daga Annoba da kuma Dujjal:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Akwai Mala'iku akan hanyoyin Madinah, saboda haka Dujjal da kuma Annoba ba zasu shige ta ba" (Bukhari: 1880, Muslim: 1379).
5. Falalan zama a cikinta, da rayuwa da kuma mutuwa a cikinta:
Haƙiƙa Annabi (S. A. W) yayi alƙawarin ceto a ranan Alkiyama ga wanda yayi haƙuri a bisa ƙuncin Madinah da tsananin rayuwanta. An karɓo daga Sa'ad Ɗan Abi Waƙƙas Allah Ya kara mishi yarda yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: "Madinah ita tafi musu alheri da sun kasance masu sani babu wanda zai barta domin gudanta face Allah Ya canza shi da wanda ya fi shi alheri, kuma babu wani wanda zaiyi haƙuri a bisa tsananinta da takurar rayuwanta face na zamto mishi mai ceto ko ya zamto shahidi a ranan Alkiyama" (Muslim: 1363).
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda zai iya mutuwa a Madinah to ya mutu a cikinta, domin lalle zan ceci duk wanda ya mutu a cikinta" (Attirmizi: 3917, Ibnu Majah: 3112).
6. Lalle ita kogon imani ne, kuma tana kore munana da dauɗa daga gare ta:
Imani yana komawa zuwa gare ta duk yadda tsanani ya kai, Miyagun mutanen da na banza kuma basu da mazauni a cikinta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Lalle imani yana tattaruwa a Madinah tamkar yadda macijiya take tattaruwa a cikin raminta" (Bukhari: 1876, Muslim 147), Kuma Manzon Allah (S. A. W) yace "... Na rantse da wanda rai na yake hannunShi babu wanda zai barta domin guje mata face Allah Ya canza shi da wanda ya fi shi alheri, lalle ku sani Madinah tana nan ne tamkar ƙira tana kore dauɗa kuma Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai Madinah ta kore miyagun dake cikinta kaman yadda Ƙira take tafiyar da dauɗan ƙarfe" (Muslim: 1381).
7. Lalle tana kore zunubai da laifuka:
Daga Zaidu Ɗan Thabit Allah Ya kara mishi yarda yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Lalle ita tsarkakka ce - Yana nufin Madinah- kuma lalle tana kore dauɗa tamkar yadda wuta take tafiyar da dattin Azurfa" (Bukhari: 4589, Muslim: 1384).
Maziyarcin Madinah ya kamata ya kiyaye wasu ladduba, daga cikinsu:
1. Abunda aka shar'antawa wanda yayi niyan tafiya zuwa Madinah shi ne yayi nufin ziyaran Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma nikan gari zuwa gare shi ba zuwa kabarin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba; Saboda faɗinshi (S. A. W): "Ba a niƙan gari sai dai zuwa masallatai guda uku: Masallacin Harami, da Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Masallacin Ƙudus" (Bukhari: 1189, Muslim: 1397).
2. Idan Maziyarci ya isa zuwa Masallaci an sunnanta mishi da ya gabatar da kafanshi na dama sai yace: «Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa (Muslim: 713).
3. Zai yi sallah raka'a biyu gaisuwan Masallaci, idan kuma ya sallace su a Raudah mai daraja hakan yafi.
4. An sunnanta ziyarar kabarin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da na abokanshi biyu, sai mutum ya tsaya dab da kabarin Annabi cikin ladabi yana mai sauƙe sautinshi sai yace: "Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya Annabin Allah da rahamarShi da albarkanShi, lalle na shaida cewa kai Annabi ne na gaskiya, kuma lalle ka isar da saƙo, ka cika amana, ka yiwa Al-umma nasiha, kuma kayi matiƙar ƙoƙari a cikin addinin Allah, saboda haka Allah Ya saka maka da mafificin alheri akan Al-ummarka".
Sa'annan sai yayi taku ɗaya ko biyu ta damanshi domin tsayawa akan kabarin Abubakar Allah Ya kara mishi yarda, sai yayi sallama a gare shi ya kuma nema mishi yardan Allah. Sa'annan sai yayi taku ɗaya ko biyu ta damanshi domin tsayawa akan kabarin Umar Allah Ya kara mishi yarda, sai yayi sallama a gare shi ya kuma nema mishi yardan Allah.
5. An sowa Maziyarcin Masallacin Annabi da ya yawaita yin sallah a Masallacin Annabi (S. A. W) domin ya tara lada mai ɗimbin yawa wanda Annabi yayi alƙawari a faɗinshi: "Sallah guda ɗaya a wannan masallacin nawa tafi salloli dubu a cikin waninshi sai dai Masallacin Harami" (Bukhari: 1190, Muslim: 1394).
6. An sunnanta mishi Ziyarar masallacin Ƙuba domin yin sallah a cikinshi, don samun falalan da yazo akan sallah a cikinshi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda ya tsarkaka daga gidanshi sa'annan ya taho zuwa wannan masallacin - Masallacin Ƙuba- sai yayi sallah a cikinshi, ya kasance yana da lada tamkar na umrah» (Annasa'i: 699).
7. An sunnanta ziyarar Maƙabartan Baƙi'a, da Maƙabartan Shahidan Uhud domin Annabi (S. A. W) ya kasance yana ziyartansu kuma yana musu Addu'a, Kuma ya kasance daga cikin Addu'o'in da yakewa waɗanda suke cikin kabari: "Amincin Allah ya tabbata a gare ku ya ku ma'abota wannan gidan na daga muminai da musulmai, kuma mu ma da yardan Allah zamu riske ku, ina roƙa mana lafiya da ku baki ɗaya" (Muslim: 975).
8. Musulmi yayi matiƙan ƙoƙarin ganin cewa ya kasance a daidaice akan umarnin Allah a cikin wannan birnin, yana mai lizimtar biyayya a gare Shi yana kuma bibiyan sunnar ManzonShi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kuma mai tsananin tsoron kada ya faɗa cikin bidi'a da aikin saɓo.
9. Kada ya kuskura a cikin Madinah da ya sare wata bishiya ko yayi farauta; domin hadisin da yazo daga Manzon Allah a bisa hakan, kaman faɗinshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi "Lalle Annabi Ibrahima ya haramta Makkah, kuma lalle ni kuma na haramta Madinah a cikinta ba a sare bishiyoyinta, kuma ba a farautan dabbobinta",(Muslim: 1362).
10. A yayin da musulmi yake cikin wannan birnin ya kamata ya dinga jin cewa lalle shi yana cikin garin da haske ya yaɗu daga gare shi, kuma daga gare shi ne ilimi mai amfani ya fito ya mamaye dukkanin sassan duniya, sai ya kwaɗaitu a bisa samun ilimin addini wanda zai tafi zuwa ga Allah a bisa basira da shi musamman ma idan neman ilimi ne a Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; domin hadisin Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda cewa lalle yaji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Duk wanda ya shiga wannan masallacin namu domin koyon alheri ko ya sanar da shi, ya kasance tamkar mai jihadi ne a tafarkin Allah, wanda kuma ya shiga domin wanin haka to ya kasance ne tamkar wanda yake ganin abunda ba na shi ba" (Ahmad: 10814, Ibnu Hibban: 87).