Ɓangaren yanzu model
Darasi Tarihin Rayuwar Annabi (S. A. W) (2)
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Aiko shi (S. A. W) Da Saƙon Musulunci
A lokacin da Annabi (S. A. W) ya doshi shekara Arba'in, sai keɓantuwa ya soyu zuwa gare shi, sai ya kasance yana gudanar da watan Ramadan a cikin kogon hira, yana keɓantuwa da kanshi kuma yana nazari -yana bauta- a cikinshi, kuma Annabi (S. A. W) bai gushe a bisa wannan yanayin ba har na tsawon shekara uku, har sai da wahayi ya zo mishi yayin da yake cikin wannan keɓantar tashi.
Yayin da ya cika shekara Arba'in (S. A. W) sai hasken annabta ya bayyana a gare shi, sai Allah Ya karrama shi da saƙonShi, kuma Ya aike shi zuwa ga halittunShi, kuma Ya kebance shi da karamominShi, kuma Ya sanya shi ya zamto amininShi a tsakanin Shi da bayinShi, sai mala'ika Jibrilu Alaihis salam ya sauƙo zuwa gare shi da umarnin Allah Mai girma da ɗaukaka, kuma sai Allah Maɗaukaki Ya aike shi domin ya zamto rahama ga talikai, kuma zuwa ga dukkanin mutane, yana mai bishara kuma mai gargaɗi.
Tun lokacin da Annabi (S. A. W) ya samu umarnin Ubangijinshi mai girma da ɗaukaka da ya isar da saƙo cikin fadinShi: {Ya kai wanda kake lulluɓe * Ka tashi kayi gargaɗi} [Suratul Mudassir: 1 - 2], nan take sai ya tashi ya fara ƙiran mutane zuwa bautatawa Allah Shi kaɗai, da kuma zuwa karɓan Addinin da Allah Ya aiko shi da shi.
Ƙira A Ɓoye
Farkon Wanda Ya Musulunta
Sai umarni yazo daga Allah Mai girma da ɗaukaka da ya bayyana ƙira zuwa gare Shi da fadin: {To kayi yekuwa da abunda aka umarce ka}[Alhijir: 94], Sai Annabi (S. A. W) ya bayyana ƙira zuwa ga Musulunci, kuma yayi yekuwa da gaskiya kamar yadda Allah mai girma da ɗaukaka Ya umarce shi.
A yayin da Manzon Allah (S. A. W) ya bayyana ƙira zuwa ga Allah, sai manya-manyan Ƙuraishawa suka ƙalubalanci da'awarshi da kau da kai da kuma hana wannan da'awar ta hanyoyi daban-daban, da izgili, da ƙasƙanci, da zolaya, da kuma karyatawa, domin wulaƙanta Musulmai, da kashe musu gwiwa, da muzanta karantarwar Addinin Musulunci, da sanya shubuha, da yaɗa da'awar karya, da yarjejeniya da Annabi akan ya bar wannan da'awa su kuma zasu bashi ababen duniya na musamman.
A yayin da Annabi (S. A. W) ya kasance a cikin wannan yanayin, wanda da'awarshi tana tsakanin kaiwa ga nasara da kuma taɓewa, sai hadisar Isra'i da Mi'iraji ta faru, kuma wannan hadisar tazo ne a matsayin tabbatar da Annabi (S. A. W) da kuma karrama shi bayan shekaru da dama na daga da'awa, da haƙuri a bisa cutarwar mushirkai da wulaƙancinsu, da makircinsu da kuma jafa'insu.
Ƙira A Wajen Garin Makkah
Caffa Biyu Na Aqabah (Bai'atã Al-Aƙabah)
Bayan yawancin musulmai sunyi hijirah daga Makkah, sai Annabi (S. A. W) da Abubakar Allah Ya kara mishi yarda suka fita suna masu hijirah zuwa Madinah, sai dai su sun fiskanci hanyar da take akasin hanyan Madinah domin ɓoyewa Ƙuraishawa lamarinsu, sai suka sauƙa a kogon Sauri kuma suka zauna a cikinshi na kwanaki uku, sa'annan sai suka fita suka fiskanci Madinah ta hanyar da mutane basu saba da ita ba wacce take kusa da gaɓar Bahrul Ahmar (Jan Kogi), a yayin da Annabi (S. A. W) da abokinshi suka kusanto Madinah, sai musulmai suka tarbe su cikin wani yanayi mai kwarjini suna cike da murna da kuma farin ciki.
Ya kasance farkon aikin da Annabi (S. A. W) ya fara bayan ya isa zuwa Madinah shi ne gina masallacin Annabin, da kuma kulla ƴan uwantaka a tsakanin mutanen Makkah (Almuhajirun) da mutanen Madinah (Al-Ansar), yana mai nufin tabbatar da ginshiƙin sabon Addinin Musulunci da aikata hakan.
Allah Mai girma da ɗaukaka ya sauƙar da izinin yaƙi ga musulmai, domin su kare kawukansu da kuma daularsu, kuma domin su faɗaɗa yaɗa saƙon musulunci tabbatacce, Allah Maɗaukaki Yace: {An yi izini ga waɗanda ake yaƙansu cewa an zalumce su} [Alhajj: 39]. Kuma ita ce farkon ayar da ta sauƙo tana ba da izinin yaƙi, kuma haƙiƙa Manzon Allah yayi yaƙoƙa guda ashirin da bakwai, kuma ya tura anje yaki sau hamsin da shida.
Manya-Manyan ababen da suka faru bayan hijirah
Shekara ta farko na daga hijirah:
Shekara ta biyu na daga hijirah
Shekara ta uku na daga hijirah
Shekara ta huɗu na daga hijirah
Shekara ta biyar na daga hijirah
Shekara ta shida na daga hijirah
Shekara ta bakwai na daga hijirah
Shekara ta takwas na daga hijirah
Shekara ta tara na daga hijirah
Shekara ta goma na daga hijirah
A yayin da da'awa ta kammala, kuma musulunci ya gama yaɗuwa a yankin larabawa, kuma mutane suka shiga addinin Allah taru-taru, kuma addinin ya fara yaɗuwa a sassan duniya, kuma ya bayyana a bisa dukkanin addinai, sai manzon Allah (S. A. W) yaji a jikinshi cewa ajalinshi ya kusa, sai ya fara shirin saduwa da ubangijinshi, sai wasu ayyukanshi da kuma zantukanshi suka nuna cewa lalle ya kusa tafiya ya bar wannan duniya mai karewa.
Kuma a cikin shekara ta goma sha ɗaya na daga hijirah: Sai Manzon Allah (S. A. W) ya rasu, kuma hakan ya kasance a ranar litinin ne, sha biyu ga watan rabi'ul Auwal.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rasu kuma ya kasance yana da shekaru sittin da uku, daga cikinsu akwai shekaru arba'in gabanin Annabta, da kuma shekaru ashirin da uku yana matsayin Annabi kuma Manzo, daga cikinsu akwai shekaru goma sha uku a garin Makkah, da kuma shekaru goma a Madinah.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rasu amma kuma Addininshi ya wanzu; Ya rasu amma kuma bai bar wani alheri ba face ya nunawa Al-ummah, kuma bai bar wani sharri ba face ya gargadi Al-ummah daga gare shi, kuma mafi alherin abin da yayi nuni zuwa gare shi shi ne Tauhidi da kuma dukkanin abunda Allah Yakeso kuma yake yardar da Shi, kuma sharrin da yayi gargaɗi daga gare shi shi ne shirka da kuma dukkanin ababen da Allah ba Ya so kuma Ya tsane su.