Ɓangaren yanzu model
Darasi Rubuta Sunnah Da Mahimman Litattafanta
Malaman musulmai sun himmatu da rubuta sunnah, sai suka ƙarar da shekarunsu a wajen kiyaye ta da tantance ingantaccenta daga masu rauninta da bayanin yanayin masu rawaito ta da abunda ba a taɓa samun irinshi a tarihin ɗan Adam gaba ɗaya ba.
Ma'anar Rubuta Sunnah
Shi ne kiyaye da rubuta ababen da suka zo daga Annabi Muhammadu (S. A. W) na daga zance, da aiki ko tabbatarwa, sai aka tattara dukkanin waɗannan ababe a cikin wasu litattafan da aka buga su.
Dawwana Sunnah da kuma rubuta hadisan Annabi (S. A. W) ya bi ta wasu matakai masu yawa, kaman haka:
Matakin Farko:
Rubutu a zamanin Annabi (S. A. W) da sahabbanshi, hakan ya kasance ne a ƙarnin farko na daga hijirah, haƙiƙa Manzon Allah (S. A. W) ya kasance ya hana rubuta hadisanshi a farkon musulunci, tsoron kada ya cakuɗu da Alkur'ani.
Daga Abu Saeedil Khuduri Allah Ya kara mishi yarda, lalle Manzon Allah (S. A. w) yace: «Kada ku rubuta wani abu daga gare ni, kuma duk wanda ya rubuta wani abinda ba Alkur'ani ba daga gare ni to ya goge shi, amma kuma kuyi ta hira akaina babu damuwa» [Muslim: 3004].
Sai hadisan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare suka kasance ana haddace su a zukata, kuma ana musayansu da baki ta hanyan riwaya. Sa'annan daga baya sai Annabi (S. A. W) ya baiwa wasu daga cikin sahabbai izinin rubutu.
Daga Abdullahi Ɗan Amru Allah Ya kara musu yarda yace: Na kasance ina rubuta dukkanin abunda naji daga Manzon Allah (S. A. W) domin na kiyaye shi, sai Ƙuraishawa suka hanani kuma suka ce: Kana rubuta dukkanin ababen da kake ji alhali kuma Manzon Allah (S.A.W) Mutum ne yana magana a cikin fushi, da kuma yarda, sai na dakatar da rubutun, sai na ambatawa manzon Allah (S. A. W) hakan, sai yayi nuni da yatsarshi zuwa bakinshi, sai yace: «Ka rubuta, na rantse da wannan rai na yake hannunShi babu wani abunda yake fita daga gare shi face gaskiya» [Sunanu Abi Dawood: 3646].
Kuma a cikin hadisin Waleed Bin Muslim, daga Auza'i cewa lalle Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda yace: Yayin da Allah Ya buɗewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi garin Makkah, sai ya tashi a cikin mutane, ya godewa Allah kuma yayi jinjina a gare Shi. [sai Abu Hurairah ya ambaci huɗubar sa'annan yace:] Sai Abu Shah ya tashi -Wani mutum daga cikin mutanen Yaman- sai yace: ku rubuta mini ya Manzon Allah, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «ku rubutawa Abu Shah», waleed yace: sai nacewa Auza'i: Me yake nufin da faɗinshi: ku rubuta mini ya manzon Allah? sai yace: yana nufin wannan huɗubar da ya ji ta daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi [Bukhari: 2434, Muslim: 1355].
Mataki Na Biyu:
Dawwana hadisi a ƙarshen zamanin tabi'ai, a ƙarni na biyu na daga hijirah, kuma wannan rubutun ya zamto na musamman domin anan ne aka rubuta dukkanin sunnar Annabi, amma kuma bai kasance a bisa wani tsari na musamman ba, kuma ya kasance farkon wanda ya himmatu da hakan shi ne Amirul Muminina Umar Ɗan AbdulAzeez -Allah Yayi mishi rahama- sai ya umarci limamai biyu Ibnu Shihab Azzuhri da Abubakar Bin Hazam da su tattara Sunnah, kuma ya rubuta zuwa garuruwa daban-daban cewa: ku duba hadisan Manzon Allah (S. A. W) da suke wajenku, ku tattara su ku kiyaye su; domin lalle ne ina tsoron lalacewan Ilimi da kuma ƙarewan malamai".
Sai ya kasance farkon wanda ya dawwana hadisi da umarninshi shi ne Al-imam Azzuhri -Allah Yayi mishi rahama-, kuma wannan shi ne farkon dawwana hadisi da kuma sunnah gaba ɗaya.
Rubuta sunnah a bisa tsarin bugaggun litattafai tsararru ko a bisa babin maudu'an ilimi kaman Imani da tsarki da sallah da sauransu, ko kuma a bisa hanyar masanid sai a ambaci musnadin Abubakar sai na Umar, kaman haka.
Kuma a wannan matakin ne aka wallafa: Muwaɗɗan Imamu Malik Bin Anas -Allah Yayi mishi rahama-, kuma wannan matakin ya keɓanta da tsarawa da kuma cakuɗa maganganun Annabi (S. A. W) da maganganun sahabbai da na Tabi'ai da kuma fatawowinsu.
Matakin ware hadisin Annabi (S. A. W) da buga shi, da tattara shi, da tsara shi ba tare da haɗashi da waninshi na daga zantukan sahabbai da tabi'ai ba -sai dai da ɗan kaɗan wanda za a iya buƙatanshi-, kuma wannan matakin ya fara ne a farkon ƙarni na uku na daga hijirah, kuma daga cikin manyan litattafan da aka wallafa a cikinshi akwai: Musnadin Imamu Ahmad, da musnadin Humaidi, da waninsu.
Daga nan sai dawwana hadisi ya kankama a tsakiyan ƙarni na uku na daga hijirah, a yayin da Al-Imam Bukhari ya wallafa Sahihul Bukhari, Iman Muslim ya wallafa Sahihu Muslim, aka kuma wallafa litattafai da yawa kaman su: Sunanu Abi Dawood, da Sunanut Tirmizi, da na Nasa'i, da na Ibnu Majah, da Sunanud Darimi, da wasunsu na daga shahararrun litattafan hadisi.
Litattafan da suka shahara daga cikin litattafan da aka buga su a cikin sunnar Annabi (S. A. W) litattafai shida ne, kuma su ne: Sahihul Bukhari, da Sahihu Muslim, da kuma Sunanu Abi Dawood, da na Ibnu Majah, da na Nasa'i, da na Tirmizi.
Kamar yadda waɗannan ma suka shahara daga cikin litattafan sunnah: Sunanud Darimi, da Musnadin Al-Imam Ahmad, da Muwaɗɗan Al-Imam Malik.
Bayani Akan Litattafan Sunnah
Daga cikin mafi shararan litattafan sunnan da suka samu karɓuwa a wurin Al-ummah, su ne litattafai guda shida, kuma su ne:
1. Sahihul Bukhari: (256H)
Kuma yana daga cikin manyan litattafan da aka tara dukkanin abunda ya isa zuwa ga mawallafinshi na daga hadisan Manzon Allah (S. A. W) na ɓangaren Aƙida, da ibadah, da mu'amala, da yaƙoƙa, da tafsiri, da falalan ayyuka, kuma hakƙiƙa mawallafinshi ya lizimci inganci a cikinshi, kuma shi ne mafi ingancin littafi bayan Alkur'ani mai girma.
2. Sahihu Muslim (261H)
Shi ma yana daga cikin manyan litattafan hadisi, kuma haƙiƙa mai shi ya lizimci inganci a cikinshi, saidai sharruɗan inganci a wurinshi bai kai sharruɗan ingancin Bukhari ba, kuma shi ne littafin hadisi na biyu bayan littafin Bukhari.
3. Sunanu Abi Dawood (275H)
Kuma shi yana daga cikin litattafan sunnan da mai shi ya tsara shi akan babin fiƙihu, kuma haƙiƙa ya tara sahihan hadisai da kuma hasan a cikinshi, kuma bai kawo hadisai masu rauni ba sai ɗan kaɗan.
4. Sunanut Tirmizi (279H)
Shi ma yana daga cikin manyan litattafan hadisan Annabi (S. A. W), wanda ya tara dukkanin abunda ya isa zuwa mawallafinshi na daga hadisan Manzon Allah (S. A. W) na Aƙida da Ibadah da mu'amala da yaƙoƙa da tafsiri da falalan ayyuka, amma kuma mai shi bai lizimci inganci a cikinshi ba, saboda haka a cikinshi akwai ingantattun hadisai, akwai kyawawa, kuma akwai masu rauni.
5. Sunanun Nasa'i (303H)
Kuma shi ma an tsara shi a bisa babin fiƙihu, kuma a cikinshi akwai ingantattun hadisai, da kyawawa, da kuma masu rauni.
6. Sunanu Ibnu Majah (273H)
Kuma shi ma an tsara shi akan babin fiƙihu, kuma a cikinshi akwai ingantattun hadisai akwai kyawawa kuma akwai masu rauni, da wani shashin masu raunin da ba a amfani da su.
Al-Imam Hafiz Abul Hajjaj Almazzi yace (742H):
"Amma kuma ita sunnah, haƙiƙa Allah Ya horar mata da wasu mahaddata masana kuma gwaraza masu sani kuma masu tsananin tantancewa, waɗanda suka tsarkake ta daga shishshigin masu wuce gona da iri, da lalatawan masharrata, da kuma ta'awilin jahilai, sai suka sannafata nau'i nau'i kuma suka ƙware wajen dawwana ta a wurare da yawa da kuma lokaci daban-daban, domin kare ta da kuma tsoron lalacewanta, kuma daga cikin wanda yafi kyawun tsari, kuma yafi kyawun wallafawa, kuma yafi yawan dacewa, kuma yafi ƙarancin kura-kurai, kuma yafi ko wanne amfanarwa, kuma yafi kowanne girman fa'idah, kuma yafi kowanne yawan Albarkah, kuma yafi kowanne sauki, kuma yafi kowanne karɓuwa a gurin wanda ya yarda da wanda ya saɓa, kuma wanda yafi kowanne matsayi shi ne" Sahihu Abi Abdullahi,Muhammad Bin Isma'il Al-Bukhari" sai "Sahihu Abil Hasan Muslim Bin Hajjaj Annaisaburi", sa'annan a bayansu sai littafin "Sunan" na Abi Dawood Sulaiman Bnul As'ath Assajistani, sai kuma littafin "Aljami'u" na Abu Isa Muhammad Bin Isa Attirmidi, sai littafin "sunan" na Abu Abdurrahman Ahmad Bin Shuaibu Annasa'i, sai littafin "Sunan" na Abu Abdullahi Muhammad Bin Yazeed wanda akafi saninshi da Ibnu Majah Alƙazwini, dukda dai shi bai kai darajar sauran da aka ambata ba.
Kuma kowana ɗaya daga cikin waɗannan "litattafai guda shidan" yanada wani abunda ya bambanta shi wanda masu ilimin hadisi sun san hakan, sai waɗannan litattafai suka shahara a cikin mutane, kuma suka yaɗu a garuruwan musulunci, kuma aka yawaita amfanuwa dasu kuma ɗaliban ilimi suka kwaɗaitu a bisa mallakarsu" [Tahzibul Kamal: 147 / 1].
Musulmi zai iya sanin darajojin hadisi, shin wannan hadisin ingantacce ne, ko karɓaɓɓe ne, ko mai rauni ne, ko kuma bai samu karɓuwa ba, ta hanyan komawa zuwa ga ma'abota ilimi waɗanda suka himmatu da ilimin hadisi kuma suka ba da lokaci a cikin shi. domin haƙiƙa sun karanci hadisi ta ɓangaren yanayin sanadi da matani, da kuma ta ɓangaren karɓanshi ko barinshi.
Kuma akwai litattafai da yawa waɗanda aka wallafa su aka kuma tsara su akan hakan, kuma akwai manhajoji da dama da ingantattun dandali daban-daban na yanar gizo waɗanda suke taimakawa wajen sanin ingantattun hadisai daga hadisai masu rauni.
Daga cikin manhajoji da kuma dandalin yanar gizo wadanda suke taimakawa wajen sanin matsayin hadisai akwai:
Almausu'u Alhadisiyya wacce ake samunta a shafin Addurar Assunniyyah, kuma ta ƙunshi dubbanin darurrukan hadisai, tare da bayyana hukunce-hukuncen malaman hadisi akansu (waɗanda suka gabata, da waɗanda suka zo daga bayansu, da kuma waɗanda suke raye), kuma za a iya isa zuwa gareta ta wannan adreshin: https://dorar.net/hadith