Ɓangaren yanzu model
Darasi Annoba Wa'azi ne da Izina
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Jarrabawa da annoba suna daga cikin ƙaddarorin Allah Ta'ala waɗanda suke sauƙa akan mutane, musulminsu da kafuransu, sai dai yanayin musulmi a cikin jarrabawa ba kaman na waninshi ba ne, domin shi zai mu'amalance ta ne da abin da Ubangijinshi ya umarce shi da shi na daga haƙuri da kuma amfani da sabbuban shari'a wajen kore ta gabanin faruwanta da neman waraka daga gare ta idan ta same shi.
Cikin yaɗuwan annoba da sababin wani halitta mai rauni wanda ba za a iya ganinshi da ido ba sai da na'ura, da kuma sanya firgici da tsoro a cikin zukata -Kaman yadda ya faru a zamanin annobar korona- akwai nuna girman ƙaddarar Allah Ta'ala, da kuma raunin halittu duk matsayin da suka kai na ci gaba da kuma abunda suka mallaka na fasahan zamani, saboda haka duk yadda suka kai ba za su fita daga da'irar rauni da gazawa irin na ɗan Adam ba, kuma hakan yana nuna cewa lalle Allah Mai girma da ɗaukaka Shi ne Mai asalin ƙarfi, Wanda babu wani abunda zai iya gagaranShi a cikin sama ko a cikin ƙasa.
Hukunci Da Ƙaddara Gaskiya Ne
Musulmai sunyi imani da cewa lalle kowana abu a cikin kauni haƙiƙa Allah Ya ƙaddara shi kuma Ya rubuta shi gabanin Ya halicci dukkanin halitta, kuma wannan aƙidar ce zata basu natsuwa ta kuma tabbatar da su yayin firgici, su kasance suna karɓan ƙaddarar Allah da buɗaɗɗiyar zuciya.
Wa'aztuwa da ɗaukan izina
Yanayin masifa da Bala'i akan Musulmi:
Daga cikin manya-manyan ibadu yayin aukuwan masifa da bala'i: Ƙasƙantar da kai, da natsuwa da kuma tawali'u zuwa ga Allah Mai girma da ɗaukaka, da kuma ibadar neman agaji, da neman yaye ƙunci da baƙin ciki daga Allah Ta'ala Shi kaɗai, Allah Maɗaukakin Sarki Yace:(To, don me a lokacin da tsananinMu ya je musu basuyi tawali'u ba? Sai dai zukatansu suka ƙeƙeshe, kuma Shaiɗan ya ƙawata musu abin da suka kasance suna aikatawa) (Al-An'am: 43). Kuma Addu'a ta gaskiya tana buɗe ƙofar sama, kuma tana keta shamaki, kuma tana kusanto da nesa, kuma tana kusantarwa zuwa ga rahamar Allah (Kuma idan bayiNa suka tabaye ka dangane da Ni, to lalle ina kusa, ina amsa ƙiran mai ƙira yayin da ya ƙira Ni) (Albakara: 186). Wahab Bin Munabbih Allah Yayi mishi rahama yace: "Masifa tana sauƙa ne domin ta tono Addu'o'i".
Yana daga cikin ruɗu mai girma da kuma aminta daga makircin Allah Ta'ala mu yi ƙudurin cewa lalle zamu tsira daga waɗannan bala'o'i da cututtukan, kuma ya kasance ƙarshen abin da muke tunani akai shi ne samuwar alaƙa tsakanin musibu da zunubai, bayan kuma tana daga cikin tabbatattun ababe a cikin Alkur'ani a cikin aya sama da ɗaya. Allah Ta’ala ya ce: (Shin, kuma a lokacin da wata masifa, haƙiƙa ta same ku, alhali kuwa kun samar da biyunta, ku kace: Daga ina wannan yake? Ka ce: ‘Daga wurin rayukanku yake) (Ali-Imran: 165). Kuma Ya ce: "Kuma abin da ya sãme ku na wata masĩfa, to, sabõda abin da hannãyenku suka aikata ne, kuma Yanã yãfe laifi mãsu yawa." (Ash-Shura: 30).
{Allah Mai tausayin bayinShi ne}:
Yarda da Allah da kuma cikakken dogaro akanShi suna daga cikin manya-manyan hanyoyin fita daga cikin masifa da bala'i, saboda haka mu kasance a bisa yaƙinin cewa lalle baƙin ciki zai gushe nan ba da jumawa ba. kuma ka yaɗa alheri a cikin waɗanda kake tare da su, kuma ka nisanci karaya da sarewa, domin babu yadda tsanani ɗaya zai ci galaba akan sauƙi biyu {Kuma lalle tsanani yana tare da sauƙi * lalle tsanani yana tare da sauƙi} {Alsharhi: 5, 6).
Daga cikin sunnonin Allah waɗanda Ya sanya su a cikin Kauni cewa lalle riƙo da sabbuban shari'a waɗanda za a iya riƙo da su yana daga cikin dalilan ture sharri, kuma da su ne Manzanni da bayin Allah managarta sukayi riko, kuma wannan shi ne cikakken dogaro akan Allah da kuma tabbatar da bautarShi.
Wani halitta wanda ba a ganinshi ya tawaye wa mutanen duniya ni'imarsu da jin daɗinsu, tsaronsu da kwanciyan hankalinsu da rayuwarsu, to shin ya kamata mai hankali balle mumini ya riƙe ta a matsayin mazaunin tabbata, wanda zai samu natsuwa a cikinta, ya yi rigima dominta, ya kuma yi gasa akan ababenta da basu da tabbas?!
Lalle yana daga cikin abin da babu shakka a cikinshi cewa lalle waɗannan ƙwayoyin cutan suna daga cikin ayoyin Allah na kauni waɗanda Allah Yake tsoratar da bayinShi da su, kuma Yake tura su don wa'aztuwa da kuma ɗaukan izina daga gare su, da kuma raya ibadar tsoro, Allah Ta'ala Yace: {Kuma ba don komai Muke turo da ayoyi ba sai don tsoratarwa} (Al-Isra: 59).
Raya bautar tsoron Allah daga ayoyin Allah:
Lokaci shi ne jarin musulmi a duniya, kuma yafi dukiya tsada, kuma yafi kowana irin abu farashi; an rawaito daga Ɗan Abbas Allah Ya kara musu yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi lalle yace: «Ni'imomi guda biyu da yawa daga cikin mutane suna hasaransu: Lafiya da lokaci» (Bukhari: 6412).