Ɓangaren yanzu model
Darasi Mu'amalan mumini tare da Annoba
Zamuyi imani da ƙaddara alherinshi da sharrinshi domin hakan rukuni ne daga cikin rukunnan imani, kuma duk abunda ya samu bayi na daga Annoba da cututtuka da masifu suna faruwa ne da hukuncin Allah da kuma ƙaddararShi; sai mu yarda da hukuncin Allah kada muyi fushi ko ƙorafi ko hayaniya. Allah Ta'ala Yace: (Babu wani masifa da zai auku sai da izinin Allah, kuma duk wanda yayi imani da Allah, Allah Zai shiryar da zuciyarshi kuma Allah Masanin dukkan komai ne) (Attgabun: 11).
Mumini yana ƙudurta cewa lalle cututtuka ba sa cutarwa da ƙarfinsu, sai dai da umarnin Allah da ƙaddarar Shi, kuma duk da haka haƙiƙa ya umarce mu da riƙo da sababin kiwo lafiya da na rigakafi na zahiri, ta hanyan nisantar ababen da suke jawo cututtuka da wuraren da annoba ta sauƙa, da kuma kula da lura da rashin cakuɗuwa da marasa lafiya. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Babu camfi babu surkulle tsubbu, amma kuma ka gudu daga kuturu kaman yadda zaka gudu daga Zaki» (Bukhari: 5707).
Cututtukan annoba azaba ne daga Allah Maɗaukaki ga kafirai da munafukai, kuma rahama ce ga muminai, ta hanyan ɗaga musu darajansu da kankare musu kura-kuransu. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya labartawa Aisha Allah Ya kara mata yarda yayin da ta tambaye shi dangane da Annoba yace: «Lalle shi azaba ce wacce Allah yake turawa wanda Yake so, kuma lalle Allah Ya sanya ta rahama ce ga muminai, babu wani wanda zai faɗa cikin annoba, sai ya zauna a garinshi yana mai haƙuri mai neman lada, ya san da cewa babu abunda zai same shi sai dai abunda aka rubuta mishi, face ya kasance yana da kwatankwacin ladan shahidi» (Bukhari: 3474).
Ya wajaba akan musulmi a cikin wannan yanayin da ya dinga amfani da shawarwarin hukumomin kula da lafiya, da kuma ɗaukan nauyi wajen gabatar da maslahar Al-umma akan ta shi maslahar, ya kuma ba da gudunmawa wajen samun lafiya da komawar rayuwa zuwa yadda take a baya. Allah Ta'ala Yace: {Kuyi taimakekkeniya akan biyayya ga Allah da taƙawa, kuma kada kuyi taimakekkeniya akan zunubi da ƙiyayya} (Al-Ma'idah: 2).
Ababen da aka haramta a lokacin Annoba:
Babu shakka cewa lalle yáɗa labaran da ba gaskiya ba yana daga cikin ƙaryar da aka haramta, kuma yana daga cikin sabbuban yaɗa ɓarna a cikin mutane, saboda haka yana da Mahimmanci mutum ya kwaɗaitu a bisa rashin watsa duk wani labarin da bai da tabbaci akanshi. Allah Ta'ala Yace yayin da Yake ambatan siffofin munafukai: {Kuma idan wani lamari na daga tsaro ko tsoro ya zo musu sai su yaɗa shi, da ace sun komar da shi zuwa ga Allah, da zuwa ga Manzo, da kuma mahukunta daga cikinsu da waɗanda suke ciro hukunci daga cikinsu sun sanshi} (Annisa'i: 83).
Allah Ya haramta boye abun sayarwa, da ha'inci, da ɗaga farashi, da wasa da ababen rayuwan mutane, musamman a lokutan da masifu suke faruwa, wannan yana daga cikin cin dukiya da ƙarya da ha'inci, da kuma lalata amana, da mummunar manufa. Manzon Allah (S. A. W) yace: «Duk wanda ya ɓoye wani abun sayarwa domin yayi tsada akan musulmai to shi mai laifi ne». (Almusnad 8617).
Sakaci wajen yaɗuwan annoba daga mara lafiya zuwa mai lafiya ta kowace hanya ce haramun ne, kuma yana daga cikin manya-manyan zububai da laifi, kaman yadda ya cancanci uƙuba a duniya, kuma wannan uƙubar tana bambanta ne da yanayin girman laifi da kuma tasirinshi akan ɗaiɗaikun mutane da kuma Al-ummah gaba ɗaya.
Uƙubar wanda yake yaɗa Annoba zuwa waninshi da gangan:
4. Zagin Cuta:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana zagin Zazzaɓi, Daga Jabir Ɗan Abdullahi Allah Ya kara musu yarda, lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yacewa Ummu Sa'ib: «Kada ki zagi zazzaɓi, domin lalle shi yana tafiyar da kura-kuran ɗan Adam, kaman yadda ƙira take tafiyar da dauɗan ƙarfe» (Muslim: 2575).