Ɓangaren yanzu model
Darasi Garkuwan shari'a:
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Wasu garkuwan shari'a na daban:
Tare da ƙaruwar firgici a tsakanin mutane dangane da cututtuka da annoba, musulmi yayin da yake ɗaukar matakan kariya, zai kuma sake kare kansa da ingantattun matakan kariya na shari'a.
Abu na farko mai muhimmanci kuma mafi girman wanda mumini zai kare kanshi da shi a lokacin masifu da bala'i, shi ne komawa zuwa ga Allah Maɗaukaki, da neman tsari da kariya daga gare Shi don nisantar sharri. Misali, a lokacin da matar sarkin Masar ta yi yunƙurin lalata da Annabi Yusufu Alaihis Salam, sai ya ce: “Ina neman tsarin Allah” (Yusuf 23). Kuma a lokacin da Jibrilu ya bayyana ga Maryama, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta, sai ta ce: “Ina neman tsarin Allah Mai rahama daga gare ka.” (Maryam: 18).
Da ƙasƙantar da kai zuwa ga Allah da komawa zuwa gare Shi, da buƙatuwa zuwa gare Shi domin ɗage bala'i da yaye damuwa, domin addu'a ita ce garkuwan musulmi da kuma takobinshi, a yayin da bala'i ya kasance yana aukuwa ne da ƙaddarar Allah da kuma hukuncin Shi to babu abunda zai kawar da shi sai Addu'a. Manzon Allah (S. A. W) yace: «Babu abunda yake mayar da hukuncin Allah face addu'a» (Attirmizi: 2139).
Da neman waraka da shi domin lalle shi waraka ne ga kowana irin cuta na bayyane da na ɓoye {Kuma Muna sauƙarwa daga Alkur'ani abunda ya kasance waraka da kuma rahama ga muminai} (Al-Isra: 82). Kuma duk da imani, da yaƙini da gaskiya buƙatuwa zuwa waraka yana ƙaruwa domin faɗin Allah Ta'ala: {Kace shi shiriya ne da waraka ga waɗanda sukayi imani} (Fussilat: 44).
Musamman ma sallar Asubahi; domin faɗin Manzon Allah (S. A. W): «Duk wanda yayi sallar asubahi a cikin jama'a to yana cikin kariyar Allah» (Muslim: 657).
Addu'a yayin ganin marasa lafiya da waɗanda bala'i ya same su yana daga cikin garkuwa mai mahimmanci, ya zo a cikin hadisi cewa: «Duk wanda yaga wani wanda aka jarrabe shi sai yace: Na godewa Allah Wanda Ya bani lafiya daga abunda Ya jarrabe ka da shi, kuma Ya fifita ni a bisa da yawa daga waɗanda ya halitta fifitawa, wannan bala'in ko jarrabawar ba za ta same shi ba». (Attirmizi: 3432).
Domin lalle a cikin kiyaye ambaton Allah akwai alheri mai yawan gaske a cikin wannan duniyar da kuma lada mai girma a lahira, kuma ambaton Allah na safiya da na maraice suna daga cikin mahimman azkar ɗin da ya kamata musulmi ya kiyaye su. Domin daga cikin fa'idodinsu akwai: Yalwatan ƙirji, da natsuwar zuciya, da kasancewa tare da Allah, da kuma ambaton bawa a wajen mala'iku masu daraja.