Ɓangaren yanzu model
Darasi Hukunce-hukuncen da suka shafi Annoba
Ya halatta ayi rigakafi domin kariya daga cuta gabanin aukuwanta, kuma hakan ba ya cin karo da dogaro akan Allah domin faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin hadisi ingantacce: «Duk wanda yaci dabinon Ajwa guda bakwai da safe, guba ko tsafi ba za su cutar da shi ba a cikin wannan ranan» (Bukhari: 5445, Muslim: 2047), kuma wannan yana daga cikin tunkuɗe cuta gabanin aukuwanta.
Musulunci ya kwaɗaitar da masu lafiya da su nisanci cuɗanya da marasa lafiya, haƙiƙa Manzon Allah (S. A. W) yace: «Kada mai kula da majinyaci ya dinga cuɗanya da masu lafiya» (Bukhari: 5771, Muslim: 2221).
Saboda haka ne lalle za a nisanci shiga kan majinyaci idan har cutar ta kasance mai yaɗuwa ce, amma kuma za a iya ziyartan mutanenshi a tambaye su yanayin jikinshi, da yi mishi addu'a, da ba da agaji wajen magungunanshi da abunda ya sawwaƙa na daga kuɗi ko alfarma ko wanin haka, tare da riƙo da sabbuban kariya daga yaɗuwar wannan cutar.
Baya halatta a shiga garin da akwai Annoba a cikinshi ko a fita daga gare shi, kuma hadisin Abdurrahman Ɗan Auf Allah Ya kara mishi yarda yana nuni i zuwa hakan, lalle Annabi (S. A. W) yace: «Idan ku kaji cewa akwai ta a wani gari, to kada kuje wannan garin, kuma idan ta sauƙa a wani gari alhali kuna cikinshi, to kada ku fita kuna masu guje mata». (Bukhari: 5729, Muslim: 2219). Kuma wannan shi ne abin da yawancin malamai suka tafi akai na cewa baya halatta ayi tafiya zuwa garin da annoba ta sauƙa a cikinshi haka kuma baya halatta fita daga garin domin gujewa annobar.
Sallar jam'i wajibi ne akan maza, amma kuma malamai sun ambata cewa tana faɗi akansu yayin samun wani uzuri wanda shari'a ta amince da shi, kuma abin da ya nuna hakan shi ne hadisin Aisha Allah Ya kara mata yarda, lalle Annabi (S. A. W) yayin da yayi rashin lafiya ya bar yiwa musulmai sallar jam'i kuma yace: «Ku umarci Abubakar yayi sallah da mutane». (Bukhari: 664, Muslim: 418). Sai wannan ya nuna cewa lalle idan musulmi ya kasance yana da uzuri na rashin lafiya ko na wahala na zahiri, to lalle an bashi damar barin sallar jam'i a cikin masallaci sai yayi sallarshi shi kadai.
Ana son musulmi ya samar da wurin sallah a gidanshi domin yin sallar farilla yayin da ya rasa ta a jam'i saboda wani uzuri ingantacce, da kuma yin sallar nafila. Wannan yana daga cikin shiriyar Manzon Allah (S.A.W). A cikin hadisin Itban Bin Malik Allah Ya kara mishi yarda, wanda Muslim ya ruwaito, cewa lalle shi ya ambata ma Annabi (S. A. W) cewa ganinshi ya yi rauni, kuma idan ruwan sama ya sauƙa, to lallai akwai wani kwari tsakaninsa da mutanensa, kuma ba zai iya zuwa masallacinsu ba. Don haka sai ya nemi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ya ziyarce shi a gidansa, domin ya yi sallah a cikinta, don ya riƙi gurbin Sallar Annabi a matsayin wurin sallah. Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo ya yi sallah raka’a biyu a cikin gidan shin.
Haka ma Maimuna Allah Ya kara mata yarda ta kasance tana da masallaci a gidanta, Ammar Binu Yasir ma ya kasance yana da masallaci a gidanshi. ya kamata mu amfana daga wannan ababen, kuma mu kasance mu ma muna da masallatai a gidajenmu.
Sallar jam'i ta halatta a cikin gida idan har tsayar da ita a masallaci ya gagara, kuma za a samu ladan sallar jam'i haƙiƙa tsayar da sallar jam'i a gida ya tabbata daga da yawa daga cikin sahabbai kaman Ibnu Mas'ud da Anas Allah Ya kara musu yarda da wasunsu yayin kuɓucewar sallar limam.
Idan za ayi sallar jam'i a cikin gida, to wanda yafi dacewa da ya zamto limami shi ne mai gidan, idan har bai gabata domin limancin ba sai a samu wanda yafi kowa karatun Alkur'ani, idan suka daidaita wajen karatun Alkur'ani sai wanda ya fisu sanin hukunce-hukuncen sallah, idan anan ma suka daidaita to wanda ya fi shekaru shi ya cancanci limanci.
Idan musulmi ya yi sallah a gidanshi idan mamu ya kasance na miji ne, to sunnah shi ne ya tsaya a daman liman idan har ya kasance shi kaɗai ne, idan kuma sun kasance su da yawa ne, to sunnah shi ne su tsaya a bayanshi, idan kuma mamu ta kasance ta mace ce, to sunnah shi ne ta kasance a baya, idan kuma maza da mata suka haɗu a matsayin mamu, sai mazan su tsaya a bayan liman matan kuma su kasance a bayan mazan.
Waɗannan masifun manyan damammaki ne waɗanda za muyi amfani da su wajen koyawa mutanen gidanmu yadda ake sallah da sharruɗanta, da hukuncin tsarki da ababen da suke wajibi a cikinta, kuma muyi wasiyya da su a cikinta.
An sunnantawa mata sallar jam'i a cikin gidaje domin tabbatan hakan daga Ummu Waraƙah da Aisha da kuma Ummu Salamah Allah Ya kara musu yarda, kuma a cikin sallar jam'insu akwai falala da lada daga Allah, kuma limaminsu za ta kasance ne a tsakiyan sahu.
Ya haramta ga wanda annoba mai yaɗuwa ta kama shi da ya halarci taron mutane domin babu shakka hakan zai cutar da su, Allah kuma Yana cewa: {Lalle waɗanda suke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da wani abin da suka aikata ba, to haƙiƙa sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne} (Ahzab: 58).
Kuma daga cikin tabbatattun ƙa'idojin shari'a: Babu cuta kuma babu cutarwa, saboda haka baya halatta ga wanda ya kamu da wannan cutar da yana cuɗanya da mutane masu lafiya, kuma lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Kada mai kula da majinyaci ya dinga cuɗanya da masu lafiya» (Bukhari: 5771, Muslim: 2221).
Ba a so mai sallah ya rufe bakinshi yayin sallah domin haƙiƙa Manzon Allah (S. A. W) ya hana hakan, amma kuma yayin buƙata ko yayin tsoron kamuwa da cuta to ya halatta a gare shi da ya sanya irin waɗannan takunkumin bakan.
Yayin da sallar jam'i ta samu damuwa, to hukunce-hukuncen ranar jumma'a suna nan, an shar'anta karanta Suratul Sajadah da Suratul Insan a sallan Asuba a ranan jumma'a, da kuma yin addu'a a lokacin da ake tsammanin karɓan Addu'ar, da yawaita yiwa Annabi salati a cikin yininta, da karanta Suratul Kahfi, domin asali shi ne aikata waɗannan ababen a ranar jumma'a tare da gudanar da sallar jumma'an.
Yin musafaha da tafukan hannaye sunnah ce, Annabi (S. A. W) yace: «Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu suyi musafaha face an gafarta musu gabanin su rabu» (Abu Dawood), idan musulmi yaji tsoron kamuwa da annoba ta hanyar musafaha, to lalle zai taƙaita da sallamar fatan baki, kuma da yardan Allah za a rubuta mishi ladarta.