Ɓangaren yanzu model
Darasi Ta Yaya Mutum Zai Shiga Musulunci
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Kalmomin Shahada Guda Biyu Su Ne:
Lalle lokacin da mutum ya shiga cikin musulunci shi ne lokaci mafi tsada a cikin rayuwar shi, kuma a lokacin ne aka haife shi a bisa haƙiƙa bayan yasan sababin ramuwar shi a cikin wannan duniyar. Kuma an shar'anta bayan shigarshi cikin wannan addinin da yayi wanka kuma ya jiƙa dukkanin jikinshi da ruwa, kamar yadda ya tsarkake gangan jikinshi daga shirka da saɓo, anaso ya tsarkake zahirinshi ma da ruwa.
Kuma Lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarce ɗaya daga cikin sahabbai -Kuma yana daga cikin shuwagabannin larabawa- yayin da yayi niyyar shiga musulunci da yayi wanka (Al-Baihaƙi: 837).
To kuma duk wanda wannan ya kasance shi ne halin da yake ciki, ya kamata yayi matiƙar ƙoƙari wajen ganin cewa baiyi sakaci ya sake faɗawa cikin tarkon shaiɗan ta hanyan komawa zuwa aikata zunubi ba.
Mutum zai shiga Musulunci ne yayin da ya furuta kalmomin shahada guda biyu yana sane da ma'anarsu mai yaƙini dasu, kuma yana mai mika wuya ga ababen da suke nuni zuwa gare su.
Tuba
Sharruɗan ingancin tuba:
Matakan Tabbata Akan Tuba:
Menen Za A Aikata Bayan Tuba?
Sai mumini ya zamto ba shi da zunubi bayan ingantacciyar tuba kuma na gaskiya, saidai ma Allah zai sakawa waɗanda sukayi gaskiya, suka tuba, suka kuma koma zuwa ga Allah da wani sakamako mai girman gaske wanda shi ne: Allah zai sauya musu munanan ayyukansu da kyawawa kamar yadda Allah Yace: {Sai dai wanda ya tuba, yayi imani, kuma ya aikata aiki na gari, to waɗannan Allah zai sauya munanan ayyukansu zuwa kyawawa, kuma lalle Allah Mai yawan gafara ne Mai yawan jin ƙai} [Alfurkan: 70).
Wanda son Allah da ManzonShi suka kasance su ne mafi girman soyayya a gare shi, kuma ya zamto yana son mutane gwargwadon kusancinsu ga Allah da ingancin Addininsu da musuluncin su, kuma ya kasance ya tsani komawa zuwa abunda ya kasance akanshi na daga kafurci da shirka da kuma ɓata kamar yadda baya son a ƙona shi da wuta, to babu shakka lalle zai gane cewa imani yanada ɗanɗano da kuma daɗi a cikin zuciyarshi, domin zai samu natsuwa da Allah da kwanciyan hankali da shari'arShi, da ni'imarshi na shiriya akanshi, kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ababe guda uku duk wanda suka kasance a cikinshi ya samu ɗanɗanon Imani da su, wanda Allah da ManzonShi suka kasance sunfi soyuwa a gare shi fiye da waninsu, kuma yaso mutum kada ya so shi sai domin Allah, ya kuma tsani komawa zuwa kafurci bayan Allah Ya tsiratar da shi daga gare shi kamar yadda ya tsani a jefa shi a cikin wuta" (Bukhari: 21 , Muslim: 43).
Riƙo da Addini Da Haƙuri Akan Cutarwa A Cikinshi:
Kuma bai kamaci musulmi da yayi baƙin ciki idan wani masifa ya same shi bayan musuluncinshi ba, saboda wannan shi ne sunnar Allah a cikin jarabawa, kuma waɗanda suka fi mu alheri ma an jarrabe su da mafi tsananin jarrabawa sunyi haƙuri, kuma sunyi ƙoƙari, Annabawan Allah an jarrabe su da nau'i daban-daban na bala'i daga makusantansu da kuma waɗanda suke nesa dasu, kuma basu samu rauni a sakamakon abunda ya same su a tafarkin Allah ba, basu canza ba kuma basu sauya ba. Saboda haka, jarrabawa gwaji ne daga Allah don gwada gaskiyar imanin musulmi da kuma ƙarfin yaƙininshi, saboda haka ya kamata ya jurewa wannan jarrabawan, yayi riƙo da wannan addinin, kuma ya dinga Addu'a zuwa ga Allah kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yawaita cewa: "Ya Mai jujjaya zukata Ka tabbatar da zukatanmu a bisa addininka" (Attirmizi: 2140).