Ɓangaren yanzu model
Darasi Mummunan Nema da Hada-hadan kuɗi na haramun
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Daga cikin nema akwai wanda yake mai kyau na halal, daga cikinshi kuma akwai wanda yake mummuna mara kyau na haram, Allah Ta'ala Yace: (Ya ku waɗanda sukayi imani ku ciyar daga kyawawan ababen da kuka nema da kuma abunda muka fitar muku da shi daga cikin ƙasa, kuma kada ku ɗauka mara kyau mummuna kuna ciyarwa daga gare shi) (Albakara: 267).
Kuma a cikin hadisin Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda, lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Lalle wani zamani zai zowa mutane, mutum bai damu da abunda ya karɓa na daga dukiya ba, na halal ne ko na haram» (Bukhari: 2083).
Shi ne cin dukiyar mutane da ƙarya ba tare da haƙƙi ba, ko kuma nema ta hanyar da aka hana a shar'ance.
Hanyoyin Mummunar Nema
Sabbuban da suka kaiwa ga mummunan nema
Cutarwan Mummunan Nema
Nau'ukan ababen da suke haramun a hada-hadar dukiya
Ababen da suke haramun ne a karan kansu
Duk wata mu'amalar da ta saɓawa shari'a; kaman riba da caca, da yaudara, da damfara, da ha'inci da makamantansu na daga ababen da akwai zalumtan bayin Allah a cikinsu, da kuma cin dukiyar mutane da ƙarya. Kuma wannan nau'in babu shakka rai yanaso, saboda hakane aka tsawatar sosai akansu aka kuma bayyana uƙubar da zata hana mutum Faɗawa a cikinsu. Allah Ta'ala Yace:(Lalle waɗanda suke cin dukiyar maraya a bisa zalumci, to babu shakka wuta suke ci a cikinsu, kuma da sannu za a cusa su cikin wutan Sa'ira) (Annisa'i: 10). Kuma Allah Mai girma da ɗaukaka Yace: (Ya ku waɗanda sukayi imani ku ji tsoron Allah kuma ku bar abunda ya rage na daga riba idan har kun kasance muminai * Idan kuma ba haka ba to kuyi shirin yaƙi daga Allah da ManzonShi, amma kuma idan kuka tuba, to dukiyoyinku naku ne, kada kuyi zalumci kuma kada a zalumce ka)(Albakara: 278,279).