Alkur'ani Mai Girma
Allah Maɗaukaki Ya sauƙar da Alkur'ani a bisa mafi alherin halittunShi kuma cikamakin AnnabawanShi Muhammadu (S. A. W) domin shiryar da mutane da kuma fitar dasu daga duhu zuwa haske, Allah Maɗaukaki Yace: {Haƙiƙa haske da kuma littafi mabayyani yazo muku daga Allah * Allah Yana shiryar da duk waɗanda sukabi yardarShi zuwa tafarkin aminci, kuma yana fitar dasu daga duhu zuwa haske da izininShi, Yana kuma shiryar dasu zuwa miƙaƙƙen tafarki)[AlMa'idah: 15, 16].