Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Kyawawan siffofin Annabi Muhammadu (S. A. W)

Allah Mai girma da ɗaukaka ya keɓance AnnabinShi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da da kyawawan siffofi masu yawa waɗanda suka sanya zukata suke son shi kuma suke girmama shi. A cikin wannan darasin zaka san wasu daga cikin waɗannan kyawawan siffofin.

Sanin wasu  kyawawan halayen Annabi tsira da amincin Allah su abbata a gare shi domin ka kara sonshi

Kyawawan siffofin Annabi (S. A. W)

Annabi Muhammadu (S. A. W) shi ne ma'abocin mafi kyawun siffofi, domin haƙiƙa yanada kyawawan siffofi, da halaye maɗaukaka, da kuma kyawawan ɗabi'u, kuma duk wanda yayi dubi cikin halayensa da mu'amalarsa zai samu cewa lalle shi Annabi (S. A. W) shi ne mutum mafi darajah wanda tarihin bil Adama ya sani.

Saboda haka shi ne mafificin bayin Allah kuma mafi soyuwansu zuwa ga Allah Mai girma da ɗaukaka, Badaɗen Allah kuma abun zaɓinShi kuma abun jinjinawa a gare Shi, wanda yafi dukkanin bayin Allah Ibadah, kuma wanda ya fisu kyawawan halaye, kuma wanda ya fisu tsarkakakkiyar zuciya, kuma wanda ya fisu kyawawan mu'amala, kuma wanda yafi dukkanin mutane sanin Allah Maɗaukaki, kuma yafi kowa tabbatar da bautata miShi; Allah Ya zabe shi domin ya kasance ManzonShi kuma AnnabinShi zuwa ga mutane, kuma shi ne mai sadarwa tsakaninShi da su wajen nuni zuwa ga alheri da kuma kira zuwa ga shiriya.

Allah Ya zaɓe shi daga cikin waɗanda suka fi kowa Nasaba, kuma Ya keɓance shi da cikakkun siffofin mutane na daga Halitta da kuma halaye, kuma Ya keɓance shi da mafi cikan siffofi masu kwarjini wajen halittarshi, da kyawun ganinshi, da fuskarshi mai sheƙi, da kuma siffofinshi maɗaukaka tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Daga cikin kyawawan siffofin shi:

1. Siffar Tsawon Annabi (S. A. W)

١
Yafi kowa kyawun diri, shi ba dogo bane sosai kuma ba gajere ba, amma kuma yafi kusa da dogo, ba zasu taɓa tafiya kafaɗa da kafaɗa da wani ba face ya ɗara shi a tsawo, idan kuma ya zauna kafuɗunshi zasu kasance a sama da wanda yake zaune kusa da shi. Tsawonshi da kuma faɗinshi madaidaita ne a bisa mafi cikar siffa.
٢
Shi ba ramamme bane kuma ba mai ƙiba ba, cikinshi ya daidaita da ƙirjinshi, sa'annan bai kasance mai yawan nama a jikinshi ba kuma bai zamto a rame ba.
٣
Shi ne mafi kyawun mutane kuma shi ne mafi kwarjininsu daga nesa, ya fisu ɗaukaka kuma yafi kowa kyau daga kusa.

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya kara mishi yarda yana wasafta Annabi (S. A. W), yace: "Ya kasance madaidaicin mutum ne, ba dogo ba kuma ba gajere ba" [Bukhari: 3547].

2. Siffar Fuskarshi Mai Daraja (S. A. W)

Annabi (S. A. W) ya kasance mafi kyawun mutane a fuska, fuskarsa a mulmule take, amma kuma bata mulmule sosai ba, sai dai ya kasance a sassauce, ya kasance mai tsananin kyawu, yanada haske da kuma haskakawa a bayyane, tana walƙiya tamkar yadda wata take walƙawa a daren sha huɗu, duk wanda ya ganshi zai samu natsuwa, idan yayi farin ciki sai ɓangarorin fuskarshi suyi sheƙi, kuma su ne layukan da suke kasance akan goshi, yanada cikakkun kunnuwa biyu.

Siffar Fuskarshi Mai Daraja (S. A. W)

١
Giranshi suna da tsawo kuma sun mike har zuwa karshen idanunshi, suna nan tamkar baka kuma suna haɗe sosai ta yadda babu yadda zakaga fātarsu sai ka saka ido sosai.
٢
Idanunshi suna da fadi, farinsu fari ne fat, baƙinsu kuma baƙi ne wuluk, babu wani abunda da yafi baƙinsu kasancewa baki, amma farin kuma yana cakuɗe da ja kadan, gashin idanunshi suna da tsawo, kuma idanunshi sun kasance tamkar an sanya musu kwalli.
٣
Hancinshi madaidaita ne, tsawonsu mai kyau ne, raminsu ya daidaita, tsakiyansu kuma ya ɗan tashi, kuma a samansu akwai haske.
٤
Kumatunsu a mike suke, babu nama da yawa akansu, fatansu kuma yana da taushi, kuma basuyi tudu ko kori ba.
٥
Yana da yalwataccen baki, laɓɓanshi suna da taushi, haƙoranshi suna haske suna walƙiya, laɓɓanshi tsarkakakku madaidaita, ya kasance yana da wushirya idan yayi magana sai a ga haske yana fitowa ta tsakanin haƙoranshi, baya dariya sai dai murmushi.
٦
Yanada wuya mai tsawo; siffar wuyarshi tamkar azurfa wajen haskenta.

Gemunshi yana da yawan gashi, gashin baki ne sosai kuma yana kewaye da haɓanshi, abin da ke tsakanin haɓanshi da kuma leɓenshi na ƙasa ya bayyana kuma yana da tudu, a ƙarkƙashin leɓen shi na ƙasa akwai wani gashi wanda ya tafi zuwa gemunshi tamkar daga gemun yake.

3. Launin Fatar Annabi (S. A. W)

Annabi (S. A. W) ya kasance mafi kyawun mutane launi, Launinshi fari ne wanda yake cakuɗe da ja, mai hasken fuska kuma fara mai haskakawa. Daga Jubairu Ɗan Muɗ'im daga Aliyu Ɗan Abi Ɗalib: lalle ya wasafta Annabi ( S. A. W) sai yace: "ya kasance mai babban kai, farinshi ya cakuɗa da ja, kuma ya kasance mai tsananin yawan gemu" [Musnadu Ahmad: 944].

4. Gashin Annabi (S. A. W)

Annabi (S. A. W) ya kasance mai yawan gashi gashin kanshi yana taba kunnuwanshi idan ya rage shi idan kuma ya barshi yayi tsawo yana zubewa akan goshin shi, gashin shi ba a watse yake ba, kuma ba a kakkarye yake ba, saidai shi yana tsaka-tsaki ne, wani lokaci yana watsa shi akan goshin shi wani lokacin kuma yana rabashi a tsakiyan kanshi ba tare da ya bar wani ɓangarenshi akan goshin shi ba.

Daga Ƙatadah yace: na cewa Anas Bin Malik Allah Ya kara mishi yarda: yaya gashin Manzon Allah (S. A. W) ya kasance? sai yace: "Bai kasance mara gashi ba kuma bai kasance mai yawan gashin da ke zubewa a tsakanin kunne da kafada ba" [Bukhari: 5905, Muslim: 2338]

Farin gashin dake kan shi da kuma gemun shi basu kai guda ashirin ba, da yawansu a gemunshi suke, a tsakanin haɓan shi da leɓenshi na ƙasa, amma kuma farin gashin dake kan shi yana nan ne a tsakiyan kanshi.

Kuma Annabi (S. A. W) ya kasance yana tace gashin shi kuma yana tsaftace shi yana kuma kyautata shi, ba tare da wuce gona da iri wurin watayawa da kuma ni'imtuwa ba, kuma yana farawa ne da ɓangaren dama.

5. Siffofin Kafaɗun Annabi Da Zira'inshi Da kuma Hannayenshi (S. A. W)

١
Ya kasance yana da kafaɗu masu faɗi, tsakanin kafaɗunshi akwai nisa kuma ƙirjinshi da bayanshi suna da faɗi, kuma akwai gashi mai yawa akan kafaɗunshi.
٢
Bayanshi ya kasance fari ne fat, haskenshi tamkar na Azurfa.
٣
Yanada Zira'a masu tsawo da kuma faɗi, yanada manyan tafin hannu, yatsunshi suna da tsawo, Kashushuwan hannayenshi miƙaƙƙu ne babu karkata, akwai gashi a zira'inshi biyu, tafin hannayenshi masu faɗi ne kuma suna cike da nama, sunfi hariri laushi dukda cewa sun kasance masu tudu.

An karɓo daga Anas Allah Ya kara mishi yarda yace: "Ban taɓa taɓa wani Hariri ko Dibaji wanda yafi tafin hannun Annabi (S. A. W) laushi ba" [Bukhari: 3561, Muslim: 2330].

6. Siffar Tambarin Annabta

A kafaɗarsa ta dama akwai tambarin Annabta, kuma shi ɗin wata nama ce wacce ta taso wacce take kama da launin jikinshi, girmanta kimanin ƙoyin tantabara, a kewaye da ita kuma akwai alaman baki guda biyu, kuma gashi ya taru akanta.

Daga Jabir Ɗan Sumrata Allah Ya kara mishi yarda yace: «Kuma naga tambarin a kafaɗarsa tamkar ƙoyin tantabara kuma yana kama da launin jikinshi» [Muslim: 2344]

7. Siffar Ƙirjinshi Da Cikinshi (S. A. W)

١
Yana da faɗin ƙirji.
٢
Cikinshi ya daidaita da ƙirjinshi.
٣
Bai kasance mai manyan cinyoyi ba, kuma cinyoyinshi ba tsirara bane.
٤
Daga ƙarƙashin maƙogoronshi zuwa cibiyarshi akwai wani gashin da ya haɗa tsakaninsu tamkar wani zare, amma kuma babu gashi akan ƙirjinshi da kuma cikinshi.
٥
Hammatanshi farare ne fat babu gashi a cikinsu.

8. Siffar Ƙobri Da Diga-Digan Annabi (S. A. W)

١
Ƙashin Ƙobrin Annabi da ƙashin ƙafanshi sun kasance suna da tsawo, Ƙobrinshi tamkar tsololuwan bishiyar dabino saboda haskensu, kuma kyawawa masu walƙiya.
٢
Ya kasance yana da manyan Diga-Digai masu taushi, babu karaya a gare su kuma basu tsatstsage ba, manuniyar kafarshi tafi sauran yatsun ƙafanshi tsawo.
٣
Babu nama sosai akan idanun ƙafanshi
٤
Ya kasance mai ɗagaggen diga-digai; abun nufi shi ne cewa lalle diga-diganshi basu da tudu, cikinsu kuma ya rabu da ƙasa, kuma ƙasan diga-diganshi suna masu tsananin rabuwa da ƙasa.

9. Kyakkyawan Ƙamshin Annabi (S. A. W)

Zufanshi yafi turaren miski ƙamshi, idan mutum yayi musafaha dashi zai yini yana jin kamshin shi a tafin hannunshi, kuma ya kasance yana amfani da turare a mafi yawan lokutanshi.

Daga Anas yace: «Ban taɓa shekan wani turare ko wani abu mai ƙamshin da yafi kamshin Manzon Allah (S. A. W) ba» [Muslim: 2330].

Gamammen Zance Dangane Da Wasafta Kyawawan Halayen Annabi Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi

Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma lalle kai kana da manyan Kyawawan halaye}[Alkalam: 4], kuma a yayin da Mala'ika Jibrilu ya zowa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a karon farko, ya tsorata sosai, sai ya gayawa uwar muminai Khadijah Allah Ya kara mata yarda cewa: «Haƙiƙa na tsorata a bisa kaina», sai tace da shi: Na rantse da Allah, Allah ba zai taɓa wulaƙanta ka ba, domin lalle kana sadar da zumunci, kuma kana gaskiya a zance, kuma kana ɗaukan nauyin mai rauni, kuma kana baiwa wanda bai da shi, kuma kana girmama baƙo, kuma kana taimakawa wajen tabbatar da gaskiya». [Bukhari: 4953, Muslim: 160].

1. Amanar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya shahara da amana, har sai da mutanen shi suka sanya masa suna "Amintacce" dukda cewa sun kasance suna adawa dashi bayan aiko shi da akayi, amma kuma sun kasance suna ajjiye amanarsu a wurinshi.

2. Tausayinshi Da Jin Ƙanshi Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mai tausayi kuma mai jin ƙai ga Al-ummarshi; Allah Maɗaukaki Yace: {Haƙiƙa manzo yazo muku daga gareku mai damuwa da abunda ya dameku, mai tsananin kwaɗayi akanku, kuma mai tausayi da jin ƙan muminai} [Attaubah: 128], kuma Allah Maɗaukaki Yace:{Da rahamar Allah ne ka zamto mai tausasawa a gare su, da ka kasance mai tsanani kuma mai kaushin zuciya da tuni sun watse daga kewayenka} [Ali Imran: 159].

3. Yafiyarshi Da Kuma Gafararshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Yayin da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shiga garin Makkah yana mai buɗe ta, manyan mutanen Makkah da kuma jigoginta suka tsaya a gabanshi suna masu ƙasƙantar da kai, bayan sun kai maƙura wajen yi mishi adawa, da cutar dashi da kuma cutar da sahabbanshi na tsawon shekaru, sai dai babu abunda yayi musu face ya gaya musu cewa: Baku da wata matsala a yau, ku tafi kuna sakakku.

4. Damuwarshi Akan Shiriyar Mutane tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Kuma haƙiƙa yawan damuwarshi a bisa shiriyan mutane ya kai ya kai matakin da ya kusa halakar da kanshi domin baƙin cikinshi a garesu, Allah Maɗaukaki Yace: {Toh ka kusa ka halaka kanka saboda baƙin ciki domin basuyi imani da wannan labari ba}[Alkahfi: 6]

5. Jarumtanshi Da Ƙarfinshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Aliyu Allah Ya kara mishi yarda yace:- Kuma ya kasance mafi jarumtan jarumai- yana mai wasafta jarumtan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Mun kasance idan yaƙi ya turnuƙe, kuma musulmai suka haɗu da kafurai, muna ɓuya a bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya kasance babu wani mutum wanda yafi kusa da kafurai tamkar shi".[Ahmad: 1347]

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa