Ɓangaren yanzu model
Darasi Sadar da zumunci
Shi ne tarayya da makusanta cikin alheri, da kyautata musu, da tausaya musu, da jin ƙansu, da ziyararsu, da binciken yanayin da suke ciki, da kashewa mabuƙacinsu kuɗi.
Ayoyin Alkur’ani mai girma da Sunnar Ma’aiki da dama sun zo akan kwaɗaitar da sadar da zumunci da kuma hana yanke shi. Allah Ta’ala ya ce, yana siffanta kafirai cewa: {Waɗanda suke warware alƙawarin Allah bayan tabbatar da shi, kuma suka yanke abin da Allah Ya yi umarni da a sadar da shi, kuma suke ɓarna a bayan ƙasa, waɗannan su ne masu hasara} [Baqarah: 27]. Kuma Allah Maɗaukaki Ya ce: {To, shin, ku, idan kun juya baya ku yi fasadi a cikin kasa, kuma ku yanke zumuntanku?} [Muhammad: 22].
Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya sadar da zumuncin shi” (Bukhari 6138). Ya kuma ce: “Lalle Allah ne ya halicci halitta, a lokacin da ya gama halittanShi, sai zumunci ya ce: ‘Wannan shi ne matsayin wanda yake neman tsarinka daga yanke ni. Ya ce: Na’am, Shin ba zaka so na sadar da wanda ya sadar da kai, kuma na yanke wanda ya yanke ka ba? sai yace: Eh ya ubangiji sai Allah Yace: lalle Na ba ka wannan. sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan kun so, ku karanta faɗin Allah Ta'ala: {To shin watakila idan kun juya baya ku yi fasadi a bayan ƙasa, kuma ku yanke zumuncinku? [Muhammad: 22]" (Bukhari 5987, da Muslim 2554).
Kuma haƙiƙa shari'ar Musulunci tayi umarni da sadar da zumunci gwargwadon kusanci da kuma zumunta.
Sadar da zumunci wanda yake wajibi
Shi ne sadar da zumuncin muharramai; Kaman iyaye, da ƴaƴa maza da mata, da ƴan uwa maza da mata, da baffani, da kawunai, da goggoni, da yafendoni.
Sadar da zumunci wanda yake mustahabbi
Shi ne sadar da zumuncin waɗanda ba muharramai ba; Kaman yaran baffa, da yaran kawu, da wanin haka.
Yadda ake sadar da zumunci
Sadar da zumunci yana kasancewa ta hanyar isar da abunda ya sawwaƙa da daga alheri da kuma kamewa daga dukkanin abun da zai yiwu na daga sharri gwargwadon iko. Saboda haka zai iya kasancewa da sallama da magana, ko da dukiya da taimako yayin buƙata, ko kore cutarwa, ko sakin fuska, ko Addu'a, ko wanin haka.
Misalai akan sadar da zumunci
Daga cikin falalan sadar da zumunci
1- Lalle tana janyo soyayyar makusanta tana kuma ƙarfafa alaƙar ƴan uwantakan dake tsakaninsu.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ku san danginku waɗanda zaku sadar da zumuncinsu, domin lalle sadar da zumunci yana jawo soyayya a tsakanin mutane, yana haɓaka dukiya, yana kuma ƙara shekaru» (Attirmizi: 1979).
2- Lalle tana yalwata arziki kuma tana ƙara shekaru
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Duk wanda yake so a yalwata mishi cikin arzikinshi, a kuma a ƙara mishi a cikin shekarunshi to ya sadar da zumuncinshi» (Bukhari: 2067, Muslim: 2557).
3- Lalle Allah Yana sadar da wanda ya sadar da zumuncinshi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “Lalle Allah ne ya halicci halitta, a lokacin da ya gama halittanShi, sai zumunci ya ce: ‘Wannan shi ne matsayin wanda yake neman tsarinka daga yanke ni. Ya ce: Na’am, Shin ba zaka so na sadar da wanda ya sadar da kai, kuma na yanke wanda ya yanke ka ba? sai yace: Eh ya ubangiji sai Allah Yace: lalle Na ba ka wannan" (Bukhari 5987, da Muslim 2554).
4- Lalle sadar da zumunci sababi ne na shiga Aljannah
Haƙiƙa wani mutum ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi game da aikin da zai shigar da shi Aljannah, sai yace mishi: «Ka bautawawa Allah kuma kada kayi miShi tarayya da komai, ka tsayar da Sallah, kuma ka bayar da zakkah, kuma ka sadar da zumunci» (Bukhari: 1396, Muslim: 13).