Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Ladduban Aure

A cikin wannan darasin zamu san da dama daga cikin ladduban aure.

  • Bayanin mahimmancin siffantuwar kowanne daga cikin Ango da Amarya da ladduban aure. 
  • Gabatarwa akan da dama daga cikin ladduban aure waɗanda Musulunci ya shiryar zuwa gare su. 

Ƙari a bisa hukunce-hukuncen shari'a waɗanda suke da alaƙa da aure, waɗanda a cikinsu akwai wanda yake kasancewa gabanin ɗaura aure, daga cikinsu akwai na yayin ɗaura aure, a cikinsu kuma akwai waɗanda na bayan ɗaura aure ne su, to babu shakka musulunci ya kewaye aure da wasu ladduba masu yawa waɗanda ya kamata kowanne daga cikin ma'aurata su kiyaye su; domin neman lada daga Allah Mai girma da ɗaukaka, da kuma burin kiyaye ƙarfi da ƙargon zamantakewar aure.

1- Niyyah

Niyyan tana da babban matsayi a cikin Musulunci, kuma shahararren hadisin nan yana nuni zuwa hakan wanda shi ne faɗin Manzon Allah (S.A.W): «Lalle kowana aiki sai da niyyah, kuma lalle kowana mutum abunda yayi niyyah yana gare shi» (Bukhari: 1, Muslim: 1907). Saboda haka ya kamata ma'aurata da su ɗaura ingantacciyar niyyah yayin aure, balma yana daga cikin hikima su yawaita yin niyyah domin su ƙara samun lada da sakamako, kuma daga cikin ingantacciyar niyyah a cikin aure, bayyana aya daga cikin ayoyin Allah, da kuma zantar da hukuncin shari'a wanda ya kwaɗaitar akan aure, da kuma tsammanin zurriyya ta gari ta fito daga gare shi wacce zata kaɗaita Allah ta kuma bauta miShi, da kuma kamewan kowannensu da ma'abocinshi, da kuma kaucewa abkawa zuwa fitina da wanin haka.

2- Bin sunnah a cikin daren ginawa (Daren farko)

١
Tausayawan miji ga matarshi yayin saduwa da ita.
٢
Miji zai sanya hannunshi a bisa goshin matarshi, sai yayi addu'ar da Annabi (S. A. W) ya koyar damu ita: "Ya Allah lalle ni ina roƙonKa alherinta da alherin da ka ɗaura ta akai, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin da ta ɗauru akai" (Ibnu Majah: 1918).
٣
Miji zaiyi sallah raka'a biyu tare da matarshi kaman yadda aka shiryar da wasu sahabbai zuwa hakan.
٤
Yin Addu'a gabanin Jima'i: Mijin zai ce: Da sunan Allah, ya Allah Ka nisantar damu daga shaiɗan kuma Ka nisantar da shaiɗan daga abunda zaka azurta mu da shi» (Bukhari: 3271, Muslim: 1434), kuma babu laifi idan matar ma ta faɗa hakan.
٥
Nisantar ababen da Allah Ya haramta yayin zamantakewa, domin ya haramta ga mutum da ya zowa matarshi ta duburanta ko kuma yayin hailanta.
٦
Kuma idan mutum ya zowa matarshi sa'annan sai ya buƙaci komawa, to an sunnanta mishi yin alwala domin hadisin da Annabi yace: «Idan ɗayanku ya zowa matarshi sa'annan sai ya buƙaci ya koma, to yayi alwala» (Muslim: 308).
٧
Rashin yaɗa sirrin jin daɗi a tsakaninsu ta ɓangare na miji ko ta mace, Manzon Allah (S. A. W) yace: Lalle daga cikin mafi sharrin mutane masauki a wurin Allah ranar alkiyama shi ne mutumin zai huta da matarshi ita ma ta huta da shi sa'annan sai ya yaɗa sirrinta» (Muslim: 1437).

3- Walimar Aure

Walimar aure sunnah ce ƙarfaffa domin faɗin Annabi (S. A. W) ga Abdurrahman Bin Auf yayin da yayi aure: «Kayi walima koda da tunkiya ne» (Bukhari: 2048, Muslim: 1427).

Daga cikin ababen da ya kamata a kula da su yayin walima

١
Kada ya takƙaita gayyatan akan mawadata kawai, domin faɗin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: «Mafi sharrin abinci shi ne abincin walimah, ana gayyatan mawadata zuwa gare shi kuma ana barin talakawa» (Bukhari: 5177, Muslim: 1432).
٢
Walimar ta kasance da tinkiya ne ko sama da haka idan ya kasance akwai wadata a cikin lamarin, amma kuma banda almubazzaranci.
٣
Walimar zata iya kasancewa ba sai da nama ba.

4- Waƙen mata yayin biki

Ya halatta ga mata da suyi waƙe da kalaman da suke halal suna masu buga mandiri amma kuma nesa da maza, ba tare da amfani da ganguna ba; saboda bayyana murna da farin ciki da wannan babban bikin halal ne a Musulunci.

5- Zamantakewa da kyautatawa

Daga cikin ladduban aure masu ƙarfi shi ne zamantakewa cikin kyautatawa; Domin tabbatar da soyayyar da ita ce zata raya gidan cikin natsuwa da jin daɗin ma'auratan da yardan Allah, Allah Maɗaukaki Yace: "Kuma ku rayu da su da kyautatawa)(Alnisa'i: 19).

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa