Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Ma'anar Suratul Fatiha

Karatun fatiha yana daga cikin mafi mahimmancin rukunnan sallah wacce bata tsayuwa sai da shi. A cikin wannan darasin zaka san ma'anonin wannan surah mai girman gaske.

Sanin ma'anar ayoyin suratul fatiha

Ma'anar suratul Fatiha

Karatun fatiha yana daga cikin mafi mahimmancin rukunnan sallah wacce sallah bata tsayuwa sai da shi.

Ina yabawa Allah da dukkanin siffofinShi, da ayyukanShi, da ni'imominShi na bayyane da na ɓoye tare da soyayya da kuma girmamawa zuwa gare Shi, Ubangiji kuma shi ne Mahalicci Mamallaki Mai sarrafawa Mai ni'imtawa,(Talikai) kuma su ne duk wani wanda ba Allah Mai girma da ɗaukaka ba na daga cikin mutane da aljan da mala'iku da dabbobi da wanin haka.

Sunaye biyu daga cikin sunayen Allah, Arrahmanu yana nufin Mai gamammiyar rahama wacce ta yalwaci komai da kowa, Arrahimu kuma Shi ne wanda rahamarShi take kaiwa ga bayinShi Muminai kawai.

Ma'ana Mamallaki Mai sarrafa komai a ranar sakamako da hisabi, kuma a cikin haka akwai tunatarwa ga mumini dangane da ranar alkiyama da kuma kwaɗaitar dashi akan ayyuka na gari.

Lalle mu muna keɓance Ka Kai kaɗai ya Ubangijin mu da ibadah, ba ma Maka tarayya da kowa a cikin kowana irin nau'i na ibadarka, kuma muna neman taimako daga gareKa Kai kaɗai a cikin dukkanin al'amuranmu, domin dukkanin lammura a hannunKa suke ba wani wanda ya mallaki dai dai da ƙwayan zarra daga cikin su.

Ka nuna mana, Ka shiryar da mu, Ka kuma datar da mu zuwa hanya madaidaiciya kuma Ka tabbatar da mu akanta har sai mun riske Ka, kuma hanya madaidaiciya ita ce bayyanannen addinin musulunci wanda yake kaiwa zuwa ga yardan Allah da AljannarShi, kuma shi ne wanda cikamakin Annabawa da Manzanni Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi nuni zuwa gare shi, kuma babu wata hanya da bawa zai bi ya rabauta sai da tabbata akan wannan addinin.

Ma'ana hanyar waɗanda Kayi ni'ima a gare su da shiriya da kuma tabbata na daga cikin Annabawa da managarta waɗanda suka san gaskiya suka kuma bi ta. Kuma Ka tsirar damu, Ka nisantar damu daga hanyar waɗanda Kayi fushi dasu ka kuma tsane su, domin lalle su sun san gaskiya amma kuma basuyi aiki da ita ba, kuma Ka nisantar damu daga hanyar ɓatattu kuma su ne waɗanda basu shiryu zuwa gaskiya ba saboda jahilcinsu.

Ka saurari tilawar Suratul Fatiha

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa