Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Sallar mara lafiya da na matafiyi

Musulunci addini ne mai sauƙi kuma mai yayi ƙunci, daga cikin bakan akwai sauƙaƙe wasu daga cikin hukunce-hukuncen sallah a yanayin rashin lafiya da kuma tafiya. A cikin wannan darasin zaka san hukunce-hukuncen sallar matafiyi da na mara lafiya.

  • Sanin hukunce-hukuncen sallar matafiyi. 
  • Sanin hukunce-hukuncen sallar mara lafiya. 

Sallah wajibi ne akan kowana musulmi a cikin kowana yanayi muddin yana cikin hankalinshi kuma ya san abunda yakeyi, sai dai musulunci addini ne mai la'akari da yanayin mutane da bukatunsu, daga cikin hakan akwai yanayin rashin lafiya da kuma tafiya.

Menene aka sunnantawa matafiyi?

An sunnantawa matafiyi yayin kai komonshi ko yayin zamanshi na wani lokaci wanda ya kasa kwanaki huɗu da ya taƙaita salloli masu raka'ah hurhuɗu zuwa raka'a biyu. sai ya sallaci azahar da la'asar, da isha raka'a bibbiyu maimakon raka'a hurhuɗu sai dai idan ya sallace su tare da limami mazauni to anan zaiyi koyi da shi cikin sallarshi sai ya sallace su raka'a hurhuɗu kaman shi.

An shar'anta wa matafiyi barin sunnoni ratibai sai dai na sallar asubahi, kuma an shar'anta mishi kiyaye sallar witiri da tsayuwar dare.

Ya halatta a gare shi da ya haɗa tsakanin sallar azahar da ta la'asar da kuma tsakanin Magariba da isha'i a cikin lokacin ɗaya daga cikin su. musamman idan hakan ya kasance a yayin da yake zirga-zirga ne a cikin tafiyarshi, wannan kuma sauƙi ne daga wurin Allah da rahama da kuma yaye ƙunci.

Sallar Mara Lafiya

Tsayuwa na faɗuwa akan mara lafiyan da ba zai iya tsayuwa ba, ko tsayuwar zata ba shi wahala ko kuma zata iya jinkirta samun lafiyarshi, sai yayi sallah a zaune, idan kuma ba zai iya ba, to yayi a bisa gefenshi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Kayi sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba to kayi ta a zaune, idan kuma ba zaka iya ba to kayi ta a bisa gefenka" (Bukhari: 1117).

Hukunce-hukunce na musamman ga sallar mara lafiya

١
Duk mara lafiyan da ba zai iya ruku'u ko sujjada ba to zai ɗan sunkuyar da kanshi ne gwargwadon ikonshi.
٢
Wanda ba shi da ikon zama akan ƙasa zai iya zama akan kujera ko wani abu makamancinshi.
٣
Wanda tsarki ga kowace sallah zai ba shi wahala sakamakon rashin lafiya, to ya halatta a gare shi da ya haɗa tsakanin azahar da la'asar da kuma tsakanin Magariba da isha.
٤
Wanda amfani da ruwa zai bashi wahala sakamakon rashin lafiya, taimama ta halatta a gare shi domin gudanar da sallah.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa