Ɓangaren yanzu model
Darasi Ababen da aka haramtawa mai ihrami aikatawa
Ababen da aka haramta wa mai ihrami
Su ne ababen da aka hana mai harama da aikin hajji ko aikin umrah aikata su
Ababen da aka hana mai ihrami aikatawa sun kasu zuwa kashi uku
Daga cikin ababen da aka haramtawa Maza da Mata yayin sanya ihrami
Daga cikin ababen da aka haramta wa maza aikatawa yayin kasancewa cikin ihrami
Daga cikin ababen da aka hana Mata aikatawa yayin kasancewar a cikin ihrami
Kuma duk wanda ya aikata wani abu daga cikin waɗannan ababen da aka hanan, yana mai mantuwa ko ya jahilci hakan, ko kuma an tilasta shi akansu, to babu laifi akanshi domin faɗin Allah Ta'ala: (Kuma babu laifi akanku cikin abunda kukayi kuskure dashi, sai dai abunda zukatanku suka aikata su da gangan) (Al-Ahzab: 5), amma kuma idan ya tuna ko ya sani ya wajaba akanshi da ya kiyaye su nan take.
Duk wanda ya aikata wani abu daga cikin ababen da aka hana da gangan domin wani uzurin da ya ba da daman aikata shi to hadaya ya wajaba a gare shi, kuma babu laifi akanshi.
Allah Ta'ala Yace: (Kuma ku cika hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne) (Albakara: 196).
Duk wanda ya aikata waɗannan ababen da aka hanan ba tare da wani uzuri ba to hadaya ya wajaba akanshi kuma ya aikata laifi