Ɓangaren yanzu model
Darasi Haƙƙoƙin ma'aurata (Mata da miji)
Allah Ya baiwa kowanne daga cikin ma'aurata biyu haƙƙoƙi masu yawa waɗanda suka dace da ayuukan da suka rataya a wuyarshi. kuma ta hanyan gudanar da waɗannan haƙƙoƙin, da kuma rashin tauyewa mai haƙƙi haƙƙinshi ne, alaƙa zata tsaru a tsakaninsu, wacce zata kare musu mutuncinsu, kuma su samu damar gina iyali mai nasara wanda zai iya cimma manufar da dominta ne Allah Mai girma da ɗaukaka Ya halicci Annabi Adam da zurriyarshi.
Haƙƙoƙin miji akan matarshi
Ta sallamawa jagorancinshi a cikin iyali
Allah Ta’ala ya ce: {Maza masu tsayuwa ne akan mata saboda abun da Allah Ya fifita sashinsu a bisa shashi da kuma abin da suke ciyarwa na daga dukiyoyinsu} [Nisa: 34]. Wannan yana nuna cewa dole ne ya gudanar da ayyukan wannan tsayuwar ta hanya mafi kyau, ba tare da bautarwa da zalunci ba, sannan ita kuma dole ne tayi mishi biyayya a kan abin da ya dace, kada ta yi jayayya da shi cikin matsayin da Allah Ya ba shi cikin adalcinShi da hikimarShi.
Ta kiyaye mishi dukiyarshi kada tayi sakaci a cikinta
Kada ta ciyar daga dukiyarshi sai da izininshi, izinin bayyane ko na nuni. amma kuma idan ya tawaye ciyar da iyalanshi alhali yana da ikon aikata hakan, to anan tana da haƙƙin ɗaukan abunda zai ishe ta ita da yaransu ba tare da izininshi ba, amma ba tare da israfi ko almubazzaranci ba.
Ta kiyaye shi yayin da baya nan
Kada ta baiwa wani wanda ba muharraminta ba izinin shiga gidanshi alhalin kuma baya nan, babu bambanci a cikin haka tsakanin danginta da danginshi da kuma waninsu.
Ta kiyaye mishi yaranshi
Tayi tarayya da shi wajen kyautata tarbiyarsu, musamman a farkon rayuwarsu; domin lalle yaran sunfi rayuwa da ita a mafi yawan lokaci, kuma suna koyo daga gare ta fiye da yadda suke koyo daga gare shi.
Ta kula da al'amuran gida da na yara
Ta yadda zata shirya su ta tsara su, kuma ta kula da dukkanin abin da zata iya a cikin gidan.
Haƙƙoƙin mata akan mijinta
Sadaki
Sadaki haƙƙin mace ne wanda miji zai biya ta a matsayin kyauta da kyautatawa domin haɗuwan zuciya kuma hakan zai saka taji cewa yana sonta kuma yana da buƙatanta. Allah Ta'ala Yace: (Kuma ku baiwa mata sadakokinsu cikin sauƙi) (Alnisa'i: 4).
Ciyar da matan da gidanshi da kuma ahalinshi.
Kuma hakan zan kasance a cikin dukkanin ababen da suke buƙata; na daga abinci da abin sha, da tufafi, da mazauni, yadda ya dace ya kuma kamata, gwargwadon ikonshi, ba tare da israfi ko tawayewa ba. Allah Ta'ala Yace: (Mai wadata ya ciyar daga wadatarshi, wanda kuma aka tawaye mishi arzikinshi sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bashi, domin Allah Baya tilastawa rai sai dai abin da ya hore mata, da sannu Allah Zai kawo sauƙi bayan wahala) (Aɗɗalaƙ: 7).
Rayuwa da kyautatawa
Mijin ya kasance mai kyawawan halaye mai sauƙin rayuwa tare da ita ta wajen zance da aiki, ba mugu mai tsanani ba, kuma yayi haƙuri da matarshi kuma kada ya maida hankali akan kowana kuskurenta domin hakan zai sa ya tsane ta. Allah Ta'ala Yace: (Kuma ku rayu da su cikin kyautatawa, idan kuma kuka ƙi su, to zaku iya ƙin wani abu kuma Allah Ya sanya alheri mai yawa a cikinshi) Alnisa'i: 19). Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Kada mumini ya tsani wata mumina, domin idan ya ki wani hali tattare da ita wani daga cikin halayenta zai burge shi" «Muslim: 1469».