Ɓangaren yanzu model
Darasi Ciniki
Ma'anan ciniki
Ciniki a harcen larabci shi ne musayar wani abu da wani abu. A shar'ance kuma shi ne musayan kuɗi da kuɗi mallaka da mallakarwa.
Hukuncin ciniki
Ciniki abu ne wanda ya halatta a cikin littafin Allah da sunnar Annabi da kuma ijma'in malamai. Allah Maɗaukakin Sarki Yace: (Kuma Allah Ya halatta ciniki Ya kuma haramta riba) (Albakara: 275).
Hikimar dake cikin halalta ciniki
1- Lalle mutum yana da buƙatan abunda yake mallakin wani ne; na daga abinci da abin sha da tufafi da wurin zama, da wanin haka, kuma mamallakin waɗannan ababen ba zai bashi su ba tare da ya biya shi ba, kuma a cikin saya da sayarwa akwai hanyar isan kowa zuwa ga abunda ya keso; Mai sayarwa ya samu kuɗi, mai saya kuma ya samu abunda yake buƙata na daga kaya.
2- Kasantuwan rayuwar mutane a bisa mafi kyawun yanayi; Saboda lalle mutum ba zai iya samun dukkanin buƙatunshi ba sai ta hanyar saya.
3- Hana sata da damfara da zamba da wanin haka na daga ababen da suke lalata rayuwar Al-ummah; domin mutum zai iya samun abunda ya keso ta hanyar saya.