Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Matsayin iyali a Musulunci

A cikin wannan darasin zaka san abunda ake nufi da iyali a Musulunci da kuma matsayinsu a cikinshi.

  • Gabatarwa akan ma'anan iyali a cikin addinin Musulunci. 
  • Bayani akan matsayin iyali a Musulunci. 
  • Sanin ginshiƙun gina iyali a Musulunci.  

Abun nufi da Al-ummah.

Al'umma ta ƙunshi gungun mutane waɗanda suka haɗu a gama garin al'amura; kamar asali, harshe, tarihi, da kuma mafi mahimmanci addini. Waɗannan mutane sun fito ne daga gidajen aure, a matsayin mata da maza, kuma su ma za su kafa sabbin iyalai da za su haifi ƴaƴa maza da mata waɗanda za su ci gaba da tafiya, ta yadda za a tabbatar da ɗorewar al’umma da kuma ci gabanta.

Rayuwar aure ta gari ita ce ginshiƙin rayuwar al’umma, kuma daga nan ya zama dole a kula da tushe, wato iyali.

Duk da kasancewar mutum an halicce shi don ya rayu a cikin mutane ne, to baya samun kwanciyar hankali da natsuwa sai ta hanyar rayuwa cikin mutanen da alaƙoƙi da dama suka haɗa shi da su, haka kuma har ila yau yana buƙatan keɓance yanayinshi da aɗifarshi ga wasu tsirarun mutane waɗanda sune iyalanshi. iyali kuma a musulunci shi ne rukunin zamantakewar da ya ƙunshi mace da namiji waɗana suka haɗu ta hanyar auren halal, da kuma abunda zasu haifa na daga zuriyarsu.

Kuma haƙiƙa musulunci ya ɗauki nauyin kulawa da wannan tsarin, farawa da kwaɗaitar da mutane akan auratayya, zuwa ci gaba da kiyaye haƙƙin ƴaƴa, karewa da tsara alakƙar da ke tsakanin mutanen da suke cikin iyali guda ɗaya. Wannan tsarin iyali shi ne kyakkyawan yanayin tsarin halittar ɗan Adam kamar yadda Allah Maɗaukakin Sarki ya nufa.

Matsayin iyali a Musulunci

١
Iyali a Musulunci shi ne asalin ginshiƙin samar da ingantacciyar al'umma, kuɓutacciya kuma daidaitacciya.
٢
Iyali shi ne tsari mai haske da tsafta wanda ɗaiɗaikun mutane suke fitowa daga gare shi kuma ake ƙulla alaƙoƙi a ƙarƙashin inuwarshi.
٣
Iyali a Musulunci shi ne tsarin halitta na farko wanda mutum yake samun kyawawan halaye a cikinshi, kuma a cikinshi ne zai san menene haƙƙoƙinshi da kuma ayyukan da suke wajibi akanshi.
٤
Iyali a musulunci shi ne ke kula da dabi'ar mahaifi na karkatanshi zuwa tsawaita zuriyarsa, wanda ta hakan ne za a cimma burin kiyaye nau'in bil Adama.
٥
Daga cikin ababen da ke nuna girman matsayi da iyali ke da shi a Musulunci shi ne cewa lalle Allah Ta’ala Ya lissafa shi cikin ɗimbin ni’imomin da Ya yi wa ɗan Adam. Allah Ta'ala Yace: {Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi, matarshi, kuma ya watsa daga gare su maza da mata masu yawa} [Nisa: 1].

Aure a Musulunci

Allah Maɗaukakin sarki Ya cusa sha'awar juna a tsakanin maza da mata, kuma ya sanya aure ya zama halaltacciyar hanyar cika wannan sha'awa, da tabbatar da ci gaban bil Adama. Kuma haƙiƙa musulunci a cikin Alkur’ani mai girma da Sunnar Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kwaɗaitar akan yin aure.

Gina iyali a Musulunci ya dogara ne akan manyan ginshiƙai guda biyu

Ginshiƙin rai

Wannan kuwa ya haɗa da natsuwar rai, da ƙauna, da jinƙai kamar yadda ya zo a faɗinSa Maɗaukaki: {Kuma daga cikin ayoyinSa ne cewa Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku natsu a cikinsu; Kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.} [Ar-Rum: 21].

Ginshiƙin Dukiya

Kuma wannan ya haɗa da cika sharuɗɗan ɗaurin aure, da kuma lizimtar kowanne daga cikin ma’aurata ayyukansu, na daga ciyarwa da, lura, da kula da harkokin cikin gida, da maslahar yara.

Musulunci ya kwaɗaitar da dukkan ma'aurata da su kula su kuma kiyaye wannan tsarin don kada ya ruguje, kuma waɗanda suka samu mafaka a cikinsa su watse. Saboda haka ne ya buƙaci ma'auratan da yin haƙuri domin ci gaba da zamantakewar auratayyan ko da soyayya ta gushe tsakaninsu .Allah Ta’ala ya ce: {Kuma ku rayu da su da kyautatawa. To, idan kun ƙi su, to, wataƙila kun ƙi wani abu da Allah Ya sanya alheri mai yawa a cikinsa} [AlNisa,i: 19].

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa