Ɓangaren yanzu model
Darasi Riba
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Allah Mai girma da ɗaukaka cikin hikimarShi ya hukunta Riba da ta kasance cikin manya-manyan zunuban da aka haramta su a cikin shari'ar Musulunci, kuma lalle an haramtawa Al-ummun da suka rigaye mu ma; saboda masifa da bala'in dake cikinta akan Al-umma da kuma ɗaiɗaikun mutane, Allah Ta'ala Yace:(To, saboda zalumci daga waɗanda suka tuba (Yahudawa) Muka haramta musu abubuwa masu daɗi, waɗanda aka halatta su a gare su, kuma saboda yawan tusherwarsu ga hanyan Allah * Da karɓansu ga riba alhali kuma an hane su daga gare ta...) (Annisa'i: 160,161).
Kuma daga cikin ababen da suke bayyana haɗarin Riba, tsawatarwa mai tsananin da yazo a cikin ta, Allah Mai girma da ɗaukaka Yace: (Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance mãsu ĩmãni (279) To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yãƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tũba to kuna da asalin dũkiyõyinku, bã ku zãlunta, kuma bã a zãluntar ku) (Albakara: 278,279); Sai Allah Maɗaukaki Ya hana cin Riba Ya haramta ta, Ya kuma yiwa ma'abocinta alƙawarin yaƙi.
Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tabbatar da haramcinta da tsawatarwa mai tsanani a kanta, daga Jabir Allah Ya kara mishi yarda yace: "Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsinewa maciyin riba, da wanda ya ciyar da ita, da wanda ya rubuta ta, da waɗanda suka shaida ta, sai yace: dukkansu ɗaya ne" (Muslim: 1598).
Ma'anan Riba
Ma'anan Riba
Nau'ukan Riba
Riban fadali
Riban Nasi'ah
Hukuncin Riba
Hikimar haramta riba
2. Hana nema ba tare da maye gurbi ba: Domin Musulunci babu shakka ya tsara harkokin kuɗi ta yadda ɓangarori biyu duka zasu amfana, saboda haka kowa daga cikinsu zai bayar da wani abu kuma zai karɓi wani abu a madadinshi, kuma ba a samun irin wannan a harkar riba.
3. Lalle riba tana yanke kyautatawa a tsakanin mutane: Kuma hakan ya saɓawa manufar shari'a wajen yaɗa kyautatawa da alheri a tsakanin mutane.
4. Hana amfani da wani: Domin mai bayarwa a koda yaushe yana amfani ne da buƙatar wanda yake baiwa; sai ya bashi akan tsarin riba.
5. Hana zalumci: Domin riba zalumci ne ga ɓangare ɗaya, Kuma Allah Ya haramta zalumci da dukkanin nau'ukanshi.
Cutarwan Riba
1- Cutarwa akan halaye da ruhi
Riba abu ne wanda yake rusa Al-ummah ta yadda zai mayar da ita a watse kuma a ɗaiɗaice; Mai ƙarfi yana cin mara ƙarfi, kuma babu wanda zai taimaki ɗan uwanshi sai dai domin maslaharshi.