Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Waƙafi

A cikin wannan darasin zamu san abunda ake nufi waƙafi da kuma hukunce hukuncen da suke da alaƙa da shi a cikin shari'ar Musulunci.

  • Sanin ma'anan wakafi da hikimar dake cikin shar'anta shi. 
  • Sanin hukunce-hukuncen da suke da alaƙa da waƙafi. 

Wasu daga cikin waɗanda Allah Ya yalwata musu na daga cikin mawadata da masu hali suna da buƙatan sanya wani ɓangare daga cikin asalin dukiyarsu- Na daga cikin wanda asalinshi da amfaninshi zai ci gaba- waƙafi domin Allah, wanda zasu dinga ciyar da abunda aka samu daga gare shi a fuskokin alheri; domin su samu kyawawan ayyuka a rayuwansu da kuma bayan mutuwansu, kuma domin wannan waƙafin ya samar da amfani masu yawa ga mabuƙata.

Abun nufi da waƙafi

Shi ne tsayar da asalin dukiya, da kuma gudanar da amfaninta wajen neman sakamako daga Allah Mai girma da ɗaukaka.

Hukuncin waƙafi

Waƙafi mustahabbi ne kuma yana daga cikin mafificin sadaka, da kuma maɗaukakan biyayya na kusantan Allah da kuma kyautatawa, kuma waƙafi shi ne sadaka mafi amfani kuma mafi girman fa'idah; domin lalle shi yana daga cikin ayyukan da basa yankewa har bayan mutuwa.

Hikimar dake cikin waƙafi

Allah Ya shar'anta waƙafi ne domin abunda ke cikinshi na maslahohin duniya da na addini da kuma na lahira, domin bawa zai girmama ladanshi ta hanyar yin waƙafi da dukiyarshi don neman yardan Allah, kuma kyawawan ayyukanshi zasu ci gaba da gudana har bayan mutuwarshi, kuma wanda aka tsayarwa wannan waƙafin zai amfana da wannan dukiyar kuma zai yiwa mai waƙafin Addu'a; sai a samu hadin kai a cikin Al-ummah.

Kuma yana daga cikin mafifitan sadakah, domin lalle shi sadaka ce tabatacciya na dindindin a hanyoyin biyayya ga Allah da kuma kyautatawa.

Allah Maɗaukaki Yace: (Ba zaku taɓa riskan haƙiƙanin biyayya ga Allah ba har sai kun ciyar daga abunda kukeso, kuma duk wani abunda ku ka ciyar to lalle Allan Ya san da shi) (Ali Imran: 92).

Daga Ɗan Umar Allah Ya kara musu yarda yace: Umar ya samu wani fili a Khaibar, sai yaje wajen Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace mishi: Na samu wani fili wanda ban taɓa mallakan wani abu mai tsadanshi ba, saboda haka wana umarni zaka bani akanshi? sai yace: «idan kaga dama ka tsare asalinshi sai kayi sadaka da shi» sai umar yayi sadaka kuma yace lalle shi ba zai sayar da asalinshi ba, kuma ba zai kyautar ba, kuma ba zai gadar ba, sai dai ta kasance sadaka ne akan talakawa, da makusanta, da bayi, da matafiya a tafarkin Allah, da baƙi, babu laifi akan duk wani wanda ya wuce shi da yaci daga gare shi da kyautatawa ya kuma ciyar da abokinshi daga gare shi" (Bukhari: 2772, Muslim: 1632).

Nau'ukan Waƙafi

١
Waƙafi akan amfanin Addini.
٢
Waƙafi akan amfanin Duniya.

Waƙafi akan amfanin Addini

Kaman mutum ya samar da waƙafin masallaci ko na makaranta ga ɗaliban ilimi, ko wani gida ga masu rauni da talakawa da marayu da zawarawa, da makamancin haka.

Waƙafi akan amfanin Duniya

Kaman mutum ya gina gida sai ya sanya shi ya zamto waƙafi ne ga magadanshi, ko ya tsayar da wani gona ya sanya amfaninshi ya zamto nasu ne.

Waƙafi yana ƙulluwa kuma yana inganta da ɗayan ababe biyu

١
Zance: Kaman yace: Na tsayar da kaza, ko na sanya shi waƙafi, ko na karkatar da shi ko wani lafazi makamancin wannan.
٢
Aiki: Kaman ya gina masallaci sai yayiwa mutane izinin sallah a cikinshi, ko ya saya fili ya maida shi maƙabarta ya kuma baiwa mutane daman binne gawaki a cikinta, ko ya tsayar da wata Makaranta ya bawa mutane izinin karatu a cikinta, ko ya tona rijiya ya bawa mutane izinin sha daga gare ta.

Sharruɗan Waƙafi

١
Ya zamto wanda zaiyi waƙafin ya kai yayi kuma abunda zai tsayar ya kasance mallakinshi ne.
٢
Abun waƙafin ya zamto dukiya ne na halal, sananne, kuma mallakin wanda zai mai da shi waƙafin ne.
٣
Waƙafi ya zamto sanannen abu ne wanda za ana amfana da shi tare da raguwan sauranshi.
٤
Waƙafin ya kasance na aikin alheri ne kaman masallaci, ko makaranta, ko gida, ga talakawa da makusanta.
٥
Waƙafin ya kasance akan wani sanannen abu ne daga wata hukuma; kaman Masallacin kaza, ko na mutane kaza, ko na talakawa, ko na wani mutum kaman Zaidu alal misali.
٦
Waƙafin ya kasance na har abada ne ba na tsawon wani lokaci ba, wanda aka bayar da shi ba wanda aka sanya mishi sharaɗi ba, saidai idan ya alaƙanta shi da mutuwarshi to hakan ya inganta amma kuma zai bar wasiyya.

Kuma waƙafi ba shi da wani ƙayyadadden dukiya, sai dai shi yana bambanta ne da yanayin mutane ta ɓangaren yalwa da kuma wadata, duk wanda ya kasance mawadaci ne kuma ba shi da magada, to ya halalta a gare shi da ya mayar da dukkanin dukiyarshi waƙafi, kuma wanda ya kasance mawadaci ne amma kuma yana da magada, to ya halalta a gare shi da ya mayar da wani ɓangare daga cikin dukiyarshi waƙafi, sauran kuma ya barwa magada.

Kuma waƙafi ana barinshi ne gaba ɗayanshi ga Allah mai girma da ɗaukaka kuma ba a ƙayyade mishi lokaci, duk wanda ya tsayar da wani fili ko gida ko gona domin Allah Mai girma da ɗaukaka, to ya fita daga mallakanshi da tasarrufin shi, ba za a sayar ba, kuma ba za a kyautar ba, kuma ba za a janye shi ba, kuma magada ba za su sayar da shi ba domin ya riga ya fita daga cikin ababen da zasu gada.

Kuma idan mutum ya riga ya furuta sigar wakafi, ko ya aikata wani abunda yake nuna cewa lalle yayi waƙafi, toh shikenan wakafin ya tabbata, kuma tabbatan waƙafi baya buƙatan karɓan abun waƙafin, kuma baya buƙatan izinin shugaba, kuma idan waƙafi ya riga ya tabbata to baya halatta ayi tasarrufi da abunda da zai kawar da kasancewanshi wakafi a cikinshi.

Kuma lalle Allah Maɗaukaki tsarkakakke ne baya karɓa saidai mai tsarki, to idan musulmi ya buƙaci mayar da wani abu waƙafi don neman yardan Allah Mai girma da ɗaukaka, ya kamata ya zaɓi mafi kyawun dukiyarshi, da kuma mafi tsada a gurinshi, da kuma mafi soyuwa a gare shi, kuma hakan yana daga cikin kamalan biyayya da kyautatawa.

Kuma mafifin Waƙafi shi ne wanda amfaninshi ya game musulmai a kowana zamani da kuma wuri, kaman waƙafin masallaci, da neman ilimi, da ƙoƙari a tafarkin Allah Maɗaukaki, da makusanta, da talakawan musulmai, da raunanansu da makamantansu.

Daga cikin hukunce-hukuncen Waƙafi

١
Waƙafi yana inganta akan mawadaci, da talaka, da makusanci, da na nesa, da hukumomi, da ɗaiɗaikun mutane.
٢
Waƙafi yana inganta ga mutane daban-daban; kaman talakawa, da malamai, da ɗalibai da makamantansu.
٣
Waƙafi baya halatta da abunda amfani da shi zai karar da shi; Kaman kuɗi, da abinci, da abun sha, ko kuma abunda sayar da shi baya halatta; Kaman abun jingina ko abunda aka ƙwato shi.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa