Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Saki

A cikin wannan darasin zamu san ma'anar saki da wasu hukunce-hukuncen da suke da alaƙa da shi.

  • Sanin abunda ake nufi da saki 
  • Gabatarwa akan wasu kyawawan ababe a Musulunci masu alaka da saki
  • Sanin nau'ukan Saki
  • Sanin ma'anar Iddah da kuma wasu ababen da suke da alaka da ita. 

Alkawari Mai Kaushi

Musulunci ya Kwaɗaitu a bisa kiyaye rayuwar iyali, kuma ya kare alaƙan ma'aurata da alƙawarin da Alkur'ani ya wasafta shi da cewa lalle shi alƙawari ne mai kaushi, kuma wannan alƙawari mai kaushin shi ne ɗaurin Aure.

Kuma domin tabbatar da kiyaye alakar aure a cikin Musulunci, hakika Musulunci ya umurci magidanta da su riƙe matansu kada kuma su sake su ko da sun tsane su ko kuma sun tsani wani abu a tattare da su. Allah Ta’ala ya ce: {Kuma ku rayu da su da kyautatawa. To, idan kun ƙi su, to, akwai tsammanin ku ƙi wani abu, kuma Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa} [Nisa: 19]. Kuma domin kada alkawari mai kaushi ya samu damuwa, Musulunci ya yi gargaɗi da kakkausar murya kan yunƙurin haifar da fitina tsakanin ma'aurata ta hanyar ɓata mace ga mijinta. An karɓo daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ba ya daga cikinmu duk wanda ya zuga mace a kan mijinta.” (Abu Dawud 2175). Ma'anar "ya zuga" a nan yana nufin yaudara da lalata.

Adalcin Musulunci

Duk da cewa Musulunci yana da sha'awar ci gaba da zamantakewar auratayya, amma shi addini ne na gaskiya wanda ba ya zuwa da wani abu da ya saɓa wa ɗabi'ar mutane ta hanyar danne buƙatunsu da takura musu. Maimakon haka, lalle shi addini ne wanda yake la’akari da yanayinsu, da yadda suke ji, da kuma buƙatunsu. Allah Ta’ala ya sani cewa ci gaba da rayuwar auratayya a lokuta da dama zai iya zama illa fiye da karasar da shi. Kuma Ya san cewa lalle saki na iya zama abun buƙata a wani lokacin, ko kuma dole; domin haka ne halatta saki ya kasance wata hikima ce mai girman gaske da kuma yalwata wa mutane, akan abunda zasu iya shiga ciki na daga ƙunci da cutarwa.

Shar'anta Saki

Akwai ayoyi da dama waɗanda suka zo akan halaccin saki a cikin Alkur'ani mai girma da kuma sunnar Annabi, kuma wasu ayoyi da hadisan sunzo suna masu bayyana hukunce-hukuncen shi da kuma laddubanshi, Kuma an sakawa ɗaya daga cikin surorin Alkur'ani ma surar saki.

Saki a harcen larabci

Shi ne warware ƙulli da kuma sakewa

Saki a shar'ance

Shi ne wargaza igiyan aure nan take da wani lafazi na musamman, kuma wannan lafazin: ya kan iya kasancewa a bayyane; kamar lafazin saki, ko a sakaye; kamar lafazin rabuwa da haramci ko nisanta da makamantansu, kuma rubutu ko nuni mai fahimtarwa zai iya maye gurbin wannan lafazi, kuma lafazin "Khul'u" ma yana daga cikin laffuzan saki, hakama fadin alkali na raba tsakaninku yayin raba aure.

Daga cikin amfanin saki

١
Buɗe ƙofar gina wani sabon iyali akan ingantatttun ginshiƙai waɗan da basu kasance a cikin iyalin farko ba, kuma fallan Allah tana da yalwa, Allah Maɗaukaki Yace: (Kuma idan suka rabu Allah zai wadata kowanne daga yalwarShi, kuma Allah Ya kasance Mayalwaci ne Mai hikima) (Alnisa'i: 130).
٢
Ture babban ɓarna wanda ci gaba da rayuwar aure wanda yake cike da ƙiyayya da gaba zai iya kawo wa, kuma shi ne abunda zai iya kaiwa zuwa ga faɗawa cikin alfasha. Allah Ya tsare.
٣
Ɗaukan izina daga darasin auren farko, da sake nazarin da yawa daga cikin al'amura, da bayyana wa rai laifukanshj, da ƙoƙarin cin galaba akanshi, wanda hakan ne zai taimka wajen samun nasara a cikin aure na biyun.
٤
Kawo ƙarshen faɗa da saɓani, da abin da zasu iya haifarwa na daga ƙiyayya, ɓacin rai, rashin ɗa'a, da gaba.
٥
Kare yara da tunaninsu da kuma halayensu daga halaka sakamakon zama a gidan da ba shi da natsuwa da kwanciyar hankali, wanda hakan zai yi matuƙar cutar da yaran.

Daga cikin cutarwar saki

١
Tarwatsa iyali da kuma lalata gidan da ya kamata a gina shi abisa ƙauna da tausayi.
٢
Kuma Idan iyaye basu kyautata mu'amala bayan rabuwarsu ba, ko dai ta hanyar ci gaba da gaba da wargaza tunanin ƴaƴansu na kasancewa tare da kowannensu, ko kuma ta hanyar takurawa ƴaƴan a tsakaninsu, ko kuma wanin haka, to yaran za su kasance cikin ruɗani da hargitsi na hankali, kuma hakan zai karkatar da hankalinsu da dabi’unsu kuma zasu rayu da munanan illolin hakan har zuwa ƙarshen rayuwarsu.
٣
Kiyayya da rashin jituwa tsakanin mata da miji, kuma hakan na iya kaiwa ga iyalansu, ta yadda za a faɗaɗa da’irar saɓani. Wannan kuma ya saɓa wa abin da Musulunci yake so na jituwa da haɗin kan al’umma.

Nau'ukan Saki

١
Sakin da za a iya dawowa
٢
Sakin rabuwa (ƙaramar rabuwa).
٣
Sakin rabuwa (Babban rabuwa).

Sakin da za a iya dawowa

Shi ne sakin da mutum zai yiwa matarshi a karon farko da na biyu, kuma sai ya kasance yana da haƙƙin dawo da ita muddin bata gushe tana cikin iddarta ba, ko ba tare da izininta ba, kuma ba tare da buƙatar sake daura sabon aure ba.

Sakin rabuwa (ƙaramar rabuwa).

Shi ne sakin da zai kasance a cikin karon farko ko karo na biyu amma kuma har bayan ƙarewan Iddah, to anan bata halatta a gare shi da ya dawo da ita sai dai da sabon ɗaura aure.

Sakin rabuwa (Babban rabuwa).

Shi ne sakin da yake kasancewa a karo na uku, kuma a cikin shi miji bai da haƙƙin dawo da matarshi sai dai da sabon ɗaura aure da sadaki bayan kuma ta auri waninshi sai suka rabu da shi -ba tare da kasancewa an tsara hakan don ta komawa mijin farkon ba- ko kuma mijinta na biyun ya rasu ya barta.

Babu shakka hukunce-hukuncen da suke da alaƙa da dawo da mace bayan sakanta, da waɗanda suke da alaƙa da ƙaramin rabuwa da na babban rabuwa dukkaninsu suna nuni ne zuwa ga kyawawan yanayin shari'ar Musulunci a bayyane, domin saki ba shi ne ƙarshen al'amari ba, kuma lokacin da miji yake da damar dawo da matarshi da yayin da akayi karamin rabuwa, kowanne daga cikin ma'auratan zai samu dama da isashshen lokaci domin lissafi da kuma sake nazari cikin ababen da suka faru cikin natsuwa nesa da matsala da kuma damuwa, hakama bayan miji na biyu ya saki mace a babban rabuwa, dukkanin ɓangarori biyun zasu iya ganin cewa komawa zuwa ga juna abu ne mai yiwuwa kuma ma basu da wani zaɓin da ya fishi, sau dayawa ma wannan dawowar take zamtowa ita ce sabibin sake gina zamantakewar aure a bisa ingantatttun ginshiƙu masu ƙarfin gaske.

Iddah

Shi ne lokacin da shari'a ta ƙayyadewa mace bayan rabuwa -da mutuwa ko da saki- wanda ya wajaba akanta da ta zauna ta jira a cikinshi ba tare da tayi aure ba har sai wannan lokacin ya wuce.

Mace tana da haƙƙin kammala iddarta a gidan mijinta kuma a wannan lokacin ciyar da ita yana kanshi, kamar yadda za ta gaje shi idan ya mutu a cikin wannan yanayin. Kuma ya haramta a gare ta da wasu maza su nemi aurenta a yayin da take cikin lokacin iddarta.

Hikimar dake cikin shar'anta Iddah

١
Ibadah, domin lalle musulmi na miji da musulma ta mace sun sallama lamarinsu zuwa ga Allah, saboda haka, idan Ya hukunta wani abu zasuyi gaggawa ne zuwa zantar da shi; domin bayyana bautarsu zuwa ga Allah.
٢
Tabbatar da cewa babu ciki ko jariri a cikin mahaifar mace.
٣
Bayar da lokaci isashshe ga na miji bayan saki, domin ya dawar da sakakkiyar matarshi.
٤
Nuna damuwa akan mijin da ya rasu.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa