Ɓangaren yanzu model
Darasi Ababe masu ƙara imani tattare da lokacin hunturu
Hunturu lokaci ne daga cikin lokutan shekara, Allah Ya ƙaddara shi saboda wata babbar hikima.
Lafazin hunturu ya zo sau ɗaya ne kawai a cikin Alkur'ani mai girma, kuma hakan yazo a cikin suratu Ƙuraish, Allah Maɗaukaki Yace: {Saboda sabon Kuraishawa, Sabonsu na tafiyar hunturu da bazara) [Kuraish: 1- 2], tafiyar hunturu ita ce: Tafiyan kasuwancin Ƙuraishawa a hunturu; kuma sun kasance suna fiskantar Yaman ne a cikinta, a cikin tafiyar bazara kuma suna fiskantar garin Sham.
Kuma hunturu shi ne kishiyar Bazara, kuma lokacin kaka da na damuwa suke raba tsakaninsu, saboda hakane ma wasu daga cikin malamai suka ce: Lalle shekara lokaci biyu ne: Bazara da hunturu.
Hunturu yana daga cikin alamomin Ƙaddarar Allah Maɗaukaki da hikimarShi da kuma rahamarShi:
Lalle Allah Mai girma da ɗaukaka Shi ne Wanda yake jujjuya dare da rana, da zafi da sanyi, da hunturu da bazara, Allah Maɗaukaki Yace: (Lalle a cikin halittan sammai da ƙasa, da saɓawar dare da yini akwai ayoyi ga masu kaifin hankali) (Ali Imran: 190), kuma koda ace wannan saɓanin ya kasance saboda sabbuban ɗabi'a ne, to babu shakka Allah Shi ne Wanda Ya halicci waɗannan sabbuban.
Hunturu lokaci ne na ribatan shekara da kuma tuna ni'imomi
Hunturu da kuma jujjuyawar lokaci wata dama ce da mutum zai tuna tafiyan shekaru tare da gazawarShi wajen ribatansu, sai mutum ya tuna bazarar da ta wuce, da kuma yadda ta wuce cikin sauri, sai yaga wata dama a cikin sabon lokaci don maye gurbin gazawar da yayi a lokackin da ya wuce.
Allah Maɗaukaki Yace: (Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini masu saɓawa, ga wanda yake son yayi tunani, ko kuma yake son yayi godiya) (Alfurƙan: 62), Umar Ɗan Khaɗɗab Allah Ya kara mishi yarda yace: "Ka riski abin da ya kuɓuce maka na daga darenka a cikin rana, domin lalle Allah Ya sanya dare da yini su zamto masu saɓawa ga wanda yake so yayi tunani ko yayi godiya"
Lokacin hunturu wata dama ce ta tunawa da ni'imar Allah wajen samar da ɗumi ta hanyar ulu, kayan aiki, da sauran hanyoyi. Allah Ta’ala yana cewa: {Kuma da dabbobin da Ya halitta muku; a cikinsu akwai ɗumi da amfani, kuma daga gare su kuke ci.‛ (An-Nahl: 5). Waɗannan ni'imomin sun cancanci a yarda da su tare da godiya. Allah maɗaukaki yana cewa: (Kuma a lokacin da Ubangijinka Ya ce: "Idan kun gode, to, lalle ne zan ƙara muku, kuma idan kuka kafirta, to, lalle azabaTa mai tsanani ce." (Ibrahim: 7).
A cikin tsananin sanyi akwai darasi da izina da zamu ɗauka daga hadisin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayin da yace: "Jahannama ta kai ƙara zuwa ga Ubangijinta tana cewa: "Ya Ubangiji wani ɓangare na daga gare ni yana cinye wani ɓangaren, sai Ya halatta mata numfashi guda biyu a shekara, ɗaya a cikin hunturu, daya kuma a lokacin rani, wannan shi ne zafi mafi tsanani da kuke fuskanta da kuma tsananin sanyin ya yake damunku." (Al-Bukhari 3260, Muslim: 617).)
Kuma za a azabtar da ƴan wuta da sanyi kamar yadda za a azabtar da su da zafi, Allah Maɗaukaki Yace: (Ba su ɗanɗanar wani sanyi a cikinta kuma ba su ɗanɗanan wani abun sha * Sai dai tafasashshen ruwa da ruɓaɓɓen jini * Sakamako ne wanda ya dace) (Annaba'i: 24- 26). ruɓaɓɓen jinin kuma zai kasance ne mai tsananin sanyi wanda sanyinshi yake ƙuna; ƴan wuta zasu nemi agajj daga zafi, sai a taimaka musu da wani iska mai tsananin sanyi wanda zai tsatstsaga ƙashushuwansu da sanyinshi, sai su sake nema a taimakesu da zafin jahannama kuma..., Allah Ya kare mu.
Wani daga cikin magabata masu bautar Allah yace: A duk lokacin da naga ƙanƙara yana faɗowa daga sama sai na tuna yadda za a rabawa bayi takardun aikinsu a ranar tayar da mutane da kuma tara su.