Ɓangaren yanzu model
Darasi Yaƙan Tsafi Da Camfe-camfe:
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Larabawa da kuma dukkanin mutane sun kasance gabanin musulunci sunyi imani da tsubbu da tatsuniya da canfi, kuma waɗannan ababen sun mamaye ko ina a ban ƙasa kuma babu wanda ya tsira daga gare su, har sai da larabawa sukayi tsammanin- A farkon lamari- cewa Alkur'ani mai girma wani nau'i ne na waɗannan tatsuniyoyin ko kuma sihiri.
A yayin da musulunci yazo da haskenshi da kuma shiriyarshi sai ya ƴanta hankali daga duhun tsubbu da camfi da tatsuniya, da shari'oinshi da kuma ƙa'idojinshi waɗanda suke tsabtace hankali da ruhi kuma suke mayar da alakar mutum da Allah shi kaɗai koma bayan waninshi, daga cikinsu akwai:
Yaƙan Tsafi Da Camfe-camfe:
Kaman yadda ya haramtawa musulmi zuwa wurin masu tsafi da bokaye tare da tambayarsu da neman waraka ko magani daga gare su, da neman warware matsaloli a wurinsu, kuma ya wasafta duk wanda ya aikata hakan da cewa ya kafurcewa abunda aka sauƙarwa manzon Allah (S. A. W) domin amfani da cuta duka suna hannun Allah ne, kuma babu wanda yasan gaibu sai Allah, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Duk wanda yaje wurin mai bugun ƙasa ko boka kuma ya gaskata shi akan abunda yake faɗa, to haƙiƙa ya kafurcewa abunda aka sauƙarwa Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi» [Mustadrakul Hakim: 15].
Amfani Da Cuta Suna Hannun Allah Maɗaukaki
Kuma duk wanda yayi ta'ammuli cikin girman waɗannan halittun da kuma irin ƙwararren halittan da aka musu, zai gane cewa lalle mahaliccinsu shi ne Allah Mai iko, mai gudanarwa, wanda ya wajaba a gudanar mishi dukkanin nau'ukan ibadah ba tare da waninshi ba, domin shi ne mahalicci, duk wani abunda ke koma bayanshi halitta ne, Allah Ta'ala Yace: {Daga cikin ayoyin shi akwai dare da rana da rana da wata, kada kuyi sujjada ga rana ko wata, kuyi sujjada ga Allah wanda ya halicce su idan har kun kasance shi kuke bautawa} [Fuussilat: 37].
Babu Wanda Yasan Gaibu Da Kuma Abunda Zai Faru Nan Gaba Sai Allah:
Har mafificin halitta da mafi darajansu ma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai kasance yana mallakawa kanshi amfani ko cuta ba, kuma bai san gaibu ba, baisan abunda zai faru nan gaba ba, ina kuma ga wanda yake ƙasa da shi wajen daraja da matsayi, Allah Ta'ala Yace: {Kace bana mallakawa kai na amfani ko cuta saidai abunda Allah Yaso, da ace na kasance na san gaibu da na yawaitawa kai na alheri kuma da cuta bai same ni ba, ni ba komai bane face mai gargaɗi da bishara ga mutanen da zasuyi imani} [Al'A'araf: 188].
Haramcin Tsubbu Da Camfi
Misalin camfi shi ne mutum ya ɗebe tsammani daga wata tafiyarshi ko balaguronshi idan yaga wani nau'i na tsuntsu ko yaji sautinshi a farkon tafiyarshi, ba mamaki ma ya yanke tafiyar ba tare da ya kammala ta ba, kuma haƙiƙa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya wasafta hakan da cewa lalle shirka ne, yace: "Camfi shirka ne" [Abu Dawood: 3910, Ibnu Majah: 3538]; saboda hakan ya saɓawa tabbataccen imani a gurin musulmi wanda yake tabbatar da cewa lalle Allah shi ne mai gudanar da kauni, kuma shi ne masanin gaibu shi kaɗai ba tare da waninshi ba. sai musulunci ya haramta ɗebe tsammani da kuma dakon sharri daga gani ko jin sauti wani tsuntsu ko wani daga cikin dabbobi.
Sai kuma Allah ya shar'anta kyautata zato, da zaɓan kalmomin da suke nuni zuwa gare shi, da kuma dakon alheri da kyautata zato ga Allah, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare ya kasance yana cewa: "Kyautata zato yana burge ni: wato kyakkyawar kalmah, ko daddaɗar kalmah" [Bukhari: 5776, Muslim: 2224].