Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Kasuwanci Da Neman Arziƙi

A cikin wannan darasin zamu san ma'anar neman arziki da hukunce-hukunce da kuma ladduban da suke rataye da su.

  • Sanin ma'anan neman arziki. 
  • Sanin hukunce-hukunce da kuma ladduban da suke rataye da neman arziki. 

Mahimmancin Dukiya

Mutum yana buƙatan dukiya domin biyan manya-manyan buƙatunshi; Kaman abinci da abun sha, da tufafi, da wasunsu, kaman yadda zai yi amfani da ita wajen samun ababe masu amfani da yawa da kuma maslahohin da zasu inganta mishi yanayin rayuwarshi. kuma haƙiƙa Musulunci ya baiwa kuɗi mahimmanci mai girman gaske, kuma ya shar'anta hukunce-hukunce da dama waɗanda suke da alaƙa da nemanshi da kuma kashe shi.

Ma'anan Nema da kuma neman arziki

Abunda ake nufi da nema da kuma neman arziki shi ne dukkanin hanyoyi da ayyukan da mutum yake aikatawa domin samun dukiya da kuma ababen da lamarin rayuwarshi zasu tsaya dasu, sawa'an hakan ya kasance ta hanyan Kasuwanci ne, ko ta hanyar sana'a, ko noma ko waninsu.

Hukunci nema da kuma neman arziki

١
Nema kuɗi yana zamtowa wajibi akan mutum musulmi a cikin wasu yanayi; kaman neman abunda zai biya buƙatunshi da buƙatun iyalanshi da shi, da kuma ciyar da waɗannan ciyar dasu ya wajaba akanshi, ko domin biyan bashi, ko domin kamewa daga abunda yake hannun mutane.
٢
Neman kuɗi yana zamtowa mustahabbi (Abun so) idan ya kasance domin samun damar aikata nafiloli daga cikin kyawawan ayyuka ne da kuma ayyukan da suke kusantarwa zuwa ga Allah; Kaman ya sadar da zumuncin wani makusancin shi da shi, ko ya taimakawa wani matalauci.
٣
Neman kuɗi yana zamtowa halal idan ya kasance domin hutu da jin daɗi ne da ababen da Allah ya halalta na daga abinci, da abun sha da tufafi, da wasunsu na daga ababen halal waɗanda suke kari ne akan manyan bukatu.
٤
Neman kuɗi yana zamtowa haramun ne idan ya kasance ana nemanshi ta hanyan haramun, ko kuma idan nemanshi ya kai ga tozarta farillai ko faɗawa cikin ababen da Allah Ya haramta.
٥
Neman kuɗi yana zamtowa makaruhi ne (Abun ƙi) idan ya fita daga cikin ababen da aka ambata a baya, kaman ya hana shagaltuwa da nafiloli na daga ibadu.

Idan kuma manufan neman kuɗi ya kasance domin alfahari da tarawa ne, to anan ya zamto makaruhi, wasu daga cikin malaman fiƙihu kuma suna gani haramun ne.

Ya wajana akan musulmin da yake neman arziki ko neman kuɗi da ya nemi ilimin da yake da alaƙa da hakan, domin sanin hukunce hukuncen mu'amalolin kuɗaɗe; kaman hukuncin kasuwanci da ƙwadago, da kamfanoni, da riba, da waninsu na daga mu'amolin da yake aikata su, domin kada ya faɗa cikin abunda Allah Ya haramta yayin neman kuɗinshi.

Ladduban Nema Da Kuma Neman Arziki

1- Daga cikin ladduban da suke wajibi a cikin neman kuɗi: Kada ya hana ko ya tozarta wani farilla daga cikin farillun Allah Ta'ala, domi waɗannan farillun ya kamata su kasance su ne ginshiƙin da musulmi zai gina rayuwanshi da kuma lokutanshi akai.

2- Daga cikin ladduban da suke wajibi kuma: Kada neman kuɗin ya kai ga cutar da wasu, domin babu cuta kuma babu cutarwa.

3- Mutum ya kasance yana da kyawawan manufa a cikin nemanshi; Kaman kame kanshi da waɗanda ciyar dasu ya zamto wajibi akanshi daga roƙon mutane, da kuma amfani da kuɗi wajen aikata alheri, saboda haka kada manufarshi ta kasance ita ce alfahari da tarawa, ko wanin haka na daga cikin munanan manufofi.

Idan Musulmi ya tsarkake niyyarsa cikin neman arzikinshi, sai niyyarshi ta kasance domin tara abunda zai yiwa mutane sadaka dashi ne da kuma abunda zai yalwata musu, to babu shakka a cikin nemanshin nan zai kasance a cikin ibadah ne, kuma zai samu babban matsayi a wurin Allah Ta'ala. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Mafi soyuwan mutane a wurin Allah shi ne wanda ya fisu amfanar da mutane" (Al-Awsad Aɗɗabrani: 6026).

4- Daidaito da kuma auna tsakanin neman kuɗi da sauran bukatun mutum, kada ya mayar da neman kuɗi ya zamto shi ne manufa bayan kuma hanya ne shi zuwa ga manufa. Salman ya gayawa Abud Darda'i Allah Ya kara musu yarda: "Lalle ubangijinka Yana da haƙƙi akanka, kuma mutanenka ma suna da haƙƙi akanka, saboda haka ka baiwa kowana mai haƙƙi haƙƙinshi, sai yaje wajen Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ambata mishi hakan, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Yayi gaskiya ya kai Salman» (Bukhari: 1968).

5- Dogaro akan Allah Mai girma da ɗaukaka yayin neman kuɗi: Kuma haƙiƙanin tawakkali shi ne mutum yayi riƙo da sabbuban shari'a, tare da rataya zuciyarshi akan Allah.

6- Mutum ya sakankace cewa lalle arziki ba zai samu ba sai daga Allah Ta'ala Shi kaɗai, kuma arziki ba daga nema ne kawai ba, domin zai iya riƙo da dukkanin sabbuban arziki amma ba lalle ne yayi arzikin ba; domin wata hikimar da Allah Shi kaɗai ne Ya santa.

7- Yarda da abunda Allah Ya raba mishi da kuma rashin ganin cewa arzikinshi yayi jinkiri; domin abu ne wanda Allah Ya ƙaddara shi kuma bazai faruwa ba sai a cikin lokacinshi, sai musulmi ya nemi arziki cikin ladabi, da wadatar zuci, da kuma yarda da abunda Allah Ya rubuta mishi, yana mai neman halal daga barin haram. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ya ku mutane kuji tsoron Allah kuma ku kyautata nema, domin lalle babu wani rai da zai mutu har sai ya kammala arzikinshi koda ace yazo da jinkiri ne, kuji tsoron Allah kuma ku kyautata nema, ku ɗauki abunda Ya halalta, kuma ku bar abubda ya haramta» (Ibnu Majah: 2144).

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa