Ɓangaren yanzu model
Darasi Kyawawan halayen musulunci cikin mu'amalolin kuɗaɗe
kyawawan halaye suna da nasaba sosai da dukkan ɓangarorin rayuwa, kuma watakila ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke bambance tsarin kuɗi na Musulunci da shi, shj ne kyawawan dabi'un da suka samo asali daga gare su, waɗanda kuma suke la'akari da su; kuma wannan shi ne abin da ya sa tsarin kuɗi na Musulunci ya bambanta da sauran tsarin hada-hadar kuɗaɗe.
Shi ne dukkan ayyukan da shari'ar Musulunci ta amince da su na neman halal. Ma'amaloli na kuɗi sun haɗa da duk kwangilolin da suka danganci kuɗi ko waɗanda ke haifar da haƙƙin kuɗi, kamar siye, siyarwa, ƙwadago, Kamfanoni, da sauran yarjejeniyoyi makamantan haka. Hukunce-hukuncen da suka shafi mu’amalar muslunci su ne ka’idojin shari’a da suke tafiyar da mu’amalar kuɗi da tattalin arzikin mutane.
Manufofin Hada-hadan kuɗaɗe a cikin Musulunci
Musulunci shi ne addini na gaskiya, kuma ya zo da abin da yake da amfani ga mutane da abin da zai amfane su, domin daga mahaliccin mutane ne yake, Allah Maɗaukakin Sarki, shi ne mafi sani game da su da abin da yake da amfani a gare su. Allah Ta'ala Yace: {Shin wanda ya yi halitta bai san abinda ya halitta ba ne, alhali kuwa shi ne Mai tausasawa, Masani?} [Mulk: 14]. Ba kamar sauran dokoki da tsare-tsare ba, Musulunci ya zo ne da tsarin kuɗi wanda ya yi la’akari da buƙatun jiki da na duniya, da kuma buƙatun ruhi da al’amuran Lahira.
Na farko: Ɓangaren duniya: Shari’ar Musulunci ta tsara hada-hadar kuɗi na mutane ta hanyar da za ta tabbatar da adalci a tsakanin duk waɗanda abun ya shafa, da baiwa kowa haƙƙinsa, da kuma tabbatar da yadda kowa zai samu gamsuwa. Haka nan kuma ta faɗaɗa ƙofar halaltattun mu'amala tare da haramta duk wani abu da zai cutar da duk wani ɓangaren da abin ya shafa.
Na biyu: Ɓangaren Addini: Babban burin dukkanin hukunce-hukuncen Shari’a shi ne samun yardar Allah da kuma rabauta da gidan Aljanna. Haka nan kuma dukkanin hukunce-hukuncen mu’amalar muslunci suna samar da ƴan uwantaka ne a tsakanin muminai ta hanyar yaɗa adalci da kwaɗaitarwa akan kyautatawa, kamar jinkirtawa wanda yake cikin ƙunci, da kuma haramta duk wani abunda yake jawo ɓacin rai, kamar riba da caca.
Na farko: Adalci: Kuma wannan shi ne abunda zai kula da haƙƙin dukkanin ɓangarori biyun waɗanda suke hada-hadar kuɗi ba tare da ƙari ko ragi ba, kaman saya da sayarwa, ƙwadago da farashin da ya dace, da wanin haka. Allah Ta'ala Yace: (Kuma Allah Ya halalta kasuwanci) (Albakara: 275). Na biyu: Falala: Kuma shi ne kyautatawa; Kaman jinkirtawa wanda yake cikin ƙunci ko yafe mishi bashin dake kanshi, Allah Ta'ala Yace: (Idan kuma ya kasance yana cikin kunci to a jinkirta mishi har zuwa lokacin yalwa, amma kuma da zakuyi sadakah da shi yafi muku alheri da kun kasance masu sani) (Albakara: 280). Kuma kaman suyi yarjejeniya da wani ma'aikaci akan wani lada sa'annan sai ya bashi fiye da ladanshi, Allah Maɗaukaki Yace: (Kuma ku kyautata domin lalle Allah Yana son kyautatawa) (Albakara: 195).
Na Uku: Zalumci: Kuma shi ne mutum ya ɗauki abunda yafi haƙƙinshi, da cin dukiyar mutane da zalumci; Kaman riba, da caca, da hana masu aiki haƙƙinsu, da wanin haka, Allah Ta'ala Yace: (Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance mãsu ĩmãni (279) To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yãƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tũba to kuna da asalin dũkiyõyinku, bã ku zãlunta, kuma bã a zãluntar ku) (Albakara: 278,279). Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Allah Ta'ala Yace: (Mutane uku Ni ne mai husuma dasu a ranar Alkiyama, Mutumin da aka bashi domin Ni sai yayi yaudara, da mutumin da ya sayar da ɗa kuma yaci kuɗinshi, da mutamin da ya baiwa wani aiki kuma ya hana shi kudinshi bayan ya kammala aikin) (Bukhari: 2227).