Ɓangaren yanzu model
Darasi Sallar Jama'a
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Allah Ya umarci maza da su dinga sallah lokuta biyar a cikin jama'a, kuma lalle lada mai yawa yazo a cikin falalarta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Sallar jama'a tafi sallar mutum ɗaya da daraja ashirin da bakwai» (Bukhari: 645, Muslim: 650).
Mafi ƙarancin jama'a shi ne mutane biyu: Liman da mamu, kuma a duk lokacin da yawan jama'a ya ƙaru, to hakan yafi soyuwa a wurin Allah.
Ma'anar bin liman
Bibiyan Liman
Wanda za a gabatar da shi domin limanci shi ne wanda yafi ƙarfin hadda kuma yafi kyawun karatu, sai wanda yake binshi, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Wanda yake kasancewa limami akan mutane shi ne wanda ya fisu karatun littafin Allah, idan suka kasance daidai suke a karatu, toh wanda yafisu sanin sunnah..." (Muslim: 673).
Ya kamata liman yayi gaba kaɗan sai mamu kuma su jejjeru a cikin sahu a bayanshi, sai su cika sahun farko sai na biyu, idan kuma mamun ya kasance mutum ɗaya ne sai ya tsaya a gefen daman liman.
Duk wanda ya shiga sallah tare da liman bayan wani abu na daga sallar ya wuce shi, to lalle zai ci gaba da bibiyar liman ne har sai yayi sallama, sa'annan sai ya tashi ya cika abunda ya rage na daga sallarshi. sai kuma ya ɗauki abunda ya riska da liman shi ne farkon sallarshi, abunda zai aikata bayan haka kuma shi ne ƙarshen sallarshi.
Duk wanda ya riski ruku'u tare da liman to lalle ya riski wannan cikakkiyar raka'ar, kuma duk wanda ruku'u ya wuce shi to babu shakka wannan raka'ar ta wuce shi da kuma raka'o'in da suka gabace ta, sai ya shiga sallah tare da liman, idan liman yayi sallama sai ya tashi ya cika abunda ya wuce shi na daga sallar.
Misalai akan wanda farkon sallah ta wuce shi tare da liman
Wanda ya riski raka'a ta biyu na daga sallar asubahi tare da liman, to ya wajaba akanshi da ya tashi bayan sallamar liman domin ya cika raka'ar da ta wuce shi kuma ba zaiyi sallama ba har sai ya kammala ta; domin sallar asubahi raka'a biyu ce kuma shi raka'a ɗaya ya riska.
Wanda ya riski liman alhalin yana cikin tahiyyar ƙarshe na sallar magariba, ya wajaba akanshi da ya sallaci raka'o'i uku cikakku bayan sallamar liman; domin lalle shi ya riski liman ne a tahiyar ƙarshe, kuma ana riskan raka'a ne da riskan ruku'u tare da liman.
Wanda ya riski liman alhali yana cikin ruku'un raka'a ta uku na daga sallar azahar, to haƙiƙa ya riski raka'a biyu tare da liman (Kuma zasu zamto su ne raka'a biyun farko a wurin mamun), idan liman yayi sallama, sai ya tashi ya cika abunda ya rage na daga sallarshi, kuma su ne raka'a ta uku da ta huɗu, domin ita azahar sallah ce mai raka'o'i huɗu.