Ɓangaren yanzu model
Darasi Caca
Menene Caca?
Caca: Ita ce duk wata wasar da wani ɓangare zai samu amfani wani ɓangare kuma zaiyi asara, ta yadda kowana ɓangare ya kasance cikin yiwuwan ya samu amfani waninshi kuma yayi asara ko kuma yayi asara waninshi ya amfana.
Caca haramun ne a cikin Alkur'ani da sunnar Annabi da kuma Ijma'in Malamai.
Babu shakka duk wanda yaci caca zai samu amfani da fa'idah, Amma Allah Maɗaukaki Ya bayyana cewa lalle zunubinta da cutarwanta yana da girman gaske kuma yafi amfaninta da fa'idanta yawa. Allah Maɗaukakin Sarki Yace: (Suna tambayarka game da Giya da kuma Caca, ka gaya musu cewa lalle akwai zunubi mai yawa a cikin su da kuma amfani ga mutane, amma kuma zunubinsu yafi amfaninsu yawa) (Albakara 219).
Allah Maɗaukaki Yace: (Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai shi ne, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara) (Alma'idah: 90).
Cutarwan Caca akan mutum ɗaya da kuma Al-Ummah:
1. Duk wani nau'in wasan da wanda yayi nasara a cikinshi zai karɓi wani abu daga wurin wanda baiyi nasara ba: Kaman wasu jama'a na daga mutane suyi wasa da wata fefa, kuma kowa daga cikinsu zai sanya wata ƙima ta kuɗi, duk wanda yayi nasara daga cikinsu shi zai kwashe dukkanin waɗannan kuɗaɗen.
2. Musu a bisa samun nasarar wata ƙungiya ko wani ɗan wasa ko makamancin haka: Sai masu wannan musun su sanya wasu kuɗaɗe, kowaye daga cikinsu yana musu akan cin nasarar ƙungiyarshi ko ɗan wasanshi, idan ƙungiyanshi ta samu nasara sai ya kwashe kuɗaɗen, idan kuma ƙungiyanshi batayi nasara ba to ya rasa wannan kuɗaɗen.
3. Cacar katin gwada sa'a: Kaman mutum ya sayi wani kati da dala guda sai a bashi damar cankan wasu katuna, idan katinshi ya samu nasara to zai samu kuɗi fiye da wanda ya sayi katin da shi, abunda ya samun da yawa ne ko kaɗan ne.
4. Shga cikin gasa ta hanyar ƙiran waya ko aika saƙonni wanda yake kasancewa da biyan kuɗi mai yawa, hakanan dukkanin nau'ukan wasannin lantarki da na Kwamfuta ko ta hanyar yanar gizo waɗanda mai wasan cacan zai kasance tsakanin yiwuwan samun riba ko yin asara.