Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Tarayya (Kamfani)

A cikin wannan darasin zamu san ma'anar tarayya da kuma hukunce-hukuncen da suke da alaƙa da ita a cikin shari'ar Musulunci.

  • Sanin abunda ake nufi da tarayya a cikin shari'ar Musulunci. 
  • Sanin nau'ukan tarayya. 
  • Sanin nau'ukan Yarjejeniya. 
  • Sanin wasu daga cikin hukunce-hukuncen tarayya. 

Ma'anan tarayya

Shi ne tarayya a cikin haƙƙi ko aiki, tsakanin mutane biyu ko fiye da haka; Misalin na farko: Shi ne kaman mutane biyu suyi tarayya cikin gado ko kyauta, Misalin na biyu kuma suyi tarayya a cikin saya da sayarwa.

Hukuncin Tarayya

Tarayya halal ne, domin asali a kowana abu shi ne halacci. kuma Allah Ya halattawa bayinShi ne domin sauƙaƙa musu hanyar neman arziki, kuma za a iya tarayya da musulmi da waninshi, saboda haka tarayya da kafuri ya halalta da sharaɗin kada ya kasance shi kaɗai ne zai dinga tasarrufi ba tare da musulmi ba.

Hukuncin halaccin tarayya

Babu shakka mutum yana da buƙatar bunƙasa dukiyarshi, kuma babu mamaki ba zai iya aikata hakan shi kaɗai ba; domin rashin ikonshi da gogewarshi, ko domin ƙarancin jarinshi. hakama lalle Al-ummah tana da buƙatar manya-manyan ayyuka, zaiyi wuya a samu mutumin da zai iya gudanar da dukkanin sungullolinshi shi kaɗai, kuma tarayya tana saukƙaƙe dukkanin wannan.

Nau'ukan tarayya

١
Tarayyan mallaka
٢
Tarayya akan kwangila

Tarayya na dukiya ta kasu zuwa kashi biyu:

١
Tarayyan zaɓi.
٢
Tarayyan dole.

Tarayyan zaɓi

Ita ce wacce take kasancewa a tsakanin ɓangarori biyu, Kaman su sayi wani abu na daga fili ko abunda za a iya jigilarshi, sai su kasance suna tarayya a cikin mallakanshi.

Tarayyan dole

Ita ce wacce zata tabbata a tsakanin ɓangarori biyu ba tare da zaɓinsu ba, kaman mutane biyu su gaji wani abu, sai mallakin wannan abunda suka gadan ya zamto a tsakaninsu.

Tasarrufin ɓangarorin tarayya a cikin tarayyan mallaka

Kowanne daga cikin ɓangarori biyun zai zamto ne tamkar wanda abun bai shafe shi ba a cikin kason abokin tarayyanshi, saboda haka ba zaiyi tasarrufi a cikinshi ba tare da izininshi ba, idan har zaiyi tasarrufi to zaiyi tasarrufi ne kawai a cikin kasonshi sai dai idan abokin tarayyanshi ya bashi dama, to sai yayi tasarrufi a ciki duka.

Tarayyan Kwangila

Shi ne tarayya a cikin mu'amala, kaman tarayya a cikin saya da sayarwa, da haya, da makamancin haka.

Nau'ukan Tarayyan kwangila

١
Tarayyan kaso.
٢
Tarayyan Fuskoki.
٣
Tarayyan kai da kai.
٤
Tarayyan gangan jiki.
٥
Tarayyan wakiltawa.

Tarayyan Kaso

Wannan shi ne yadda ɗaya daga cikin abokan tarayya zai ba da kuɗi ga ɗayan don yin kasuwanci dashi a bisa yarjejeniyar karɓar wani kaso da aka ƙayyade na daga riba, kamar kwata ko kashi ɗaya cikin uku, sauran riban kuma zai zamto na mai kuɗin ne. Idan kuma aka yi hasara a cikin kasuwancin, to za a maye gurbin kuɗin da aka rasa ne daga ribar da aka samu, kuma mai juya kuɗin ba shi da wani alhaki. Idan kuma akayi asarar kuɗin ba tare da sakaci ko ganganci daga ɓangaren mai juya dukiyar ba, to ba shi da haƙƙi. Mai juya kuɗin amintacce ne akan karɓar kuɗin wakili ne wajen sarrafa su, ma'aikaci ne a cikin aikin, kuma abokin tarayya a cikin riba.

Tarayyan Fuskoki

Shi ne yadda mutane biyu zasuyi tarayya ba tare da kasancewa suna da jari ba, akan su sayi wani abu a bisa zasu biya kuɗi anan gaba -Domin alfarman da suke dashi a wurin mutane- sai su sayar dashi kudi a hannu, kuma sai su kasa abunda Allah Ya basu na daga riba a tsakaninsu, kuma duk asaran da aka samu ma tare zasu ɗauka, kuma kowana ɗaya daga cikinsu wakilin abokin tarayyanshi ne, kuma ya isan mishi wajen saya da sayarwa da kuma tasarrufi, kuma an saka mata suna tarayyan fuskoki ne domin ba a sayar da abu ba tare da an bayar da kuɗi ba sai ga wanda yake da fiska a cikin mutane.

Tarayyan kai da kai

Shi ne yadda mutane biyu zasuyi tarayya da gangan jikinsu da kuma dukiyansu sananne, koda ace kuɗin wani yafi na wani yawa domin su juya shi da kansu. kuma an sharɗanta kasancewan jarin sananne ne a wajen kowanne daga cikinsu, kuma riba da hasara zasu kasance ne a bisa sharaɗin da suka gindaya da kuma fahimtar junan dake tsakaninsu.

Tarayyan gangan jiki

Shi ne mutane biyu suyi tarayya cikin abunda suke nema da gangan jikinsu, sawa'an tarayyan ya kasance a cikin sana'a da kasuwanci ne; kaman ƙira, da kafinta da makamancinsu, ko ya kasance cikin aikin ƙarfi wanda yake halal ne; Kaman saran itatuwa, da yanko ciyayi, kuma abunda Allah Ya azurta su da shi daga gare shi zasu raba shi a tsakaninsu gwargwadon yarjejeniya da fahimtar juna da sukayi.

Tarayyan Wakiltawa

Shi ne kowanne daga cikin abokan tarayyan ya wakilta abokinshi cikin dukkanin harkokin kuɗaɗe da na gangan jiki a cikin tarayyan; sai ya zamto kowanne daga cikinsu yanada damar tasarrufi kamar yadda yakeso a wajen saya, da sayarwa, da karɓa, da bayarwa, da lamuni, da wakilci, da bada bashi da kuma sadaukarwa, da makamancin haka na daga ababen da kasuwanci yake buƙata na daga tasarrufi.

Kuma duk wani abunda ɗaya daga cikin waɗannan abokan tarayyan zai aikata to hakan ya wajaba akan ɗayanshi ma, kuma tarayyan zata kasance ne a cikin ababen da sukayi yarjejeniya akansu na daga dukiyarsu, Kuma zasu raba ribansu ne a bisa sharadin da suka gindaya, haka kuma za a raba asara gwargwadon kason kowanne daga cikinsu a tarayyan. Kuma irin waɗannan tarayyan duk sun halalta, domin abunda ke cikinsu na taimakekkeniya wajen neman arziki da biyan buƙatun mutane da kuma tabbatar da adalci da maslaha.

Fa'idodin tarayya

1- Lalle ita ce mafi alherin hanyar bunƙasa dukiya, da samawa mutane aiki, da amfanar da Al-ummah, da yalwata arziki da kuma tabbatar da adalci.

2- Wadatuwa ga barin neman da yake haramun ne; kaman riba, da caca da makamantansu.

3- Yalwata hanyoyin neman halal; Domin haƙiƙa musulunci ya halaltawa mutum nema shi kaɗai, ko kuma tare da wani.

Ababen da suke lalata ƙulla tarayya

١
Fasa tarayyan daga wurin ɗaya daga abokan tarayyan
٢
Mutuwan ɗaya daga cikin abokan tarayyan
٣
Haukacewan ɗaya daga cikin abokan tarayyan
٤
Rasa ɗaya daga cikin abokan tarayyan da fakuwanshi na tsawon lokaci domin hakan tamkar mutuwa ne.

Rukunnan Tarayya

١
Abokan tarayyan biyu.
٢
Abunda akayi tarayya akanshi: Kuma shi ne kuɗi ko aiki ko dukkan su biyu.
٣
Siga: Kuma shi ne yarda da karɓa daidai da al'ada.

Sharruɗan Tarayya

١
Ya kasance kowanne daga cikin jari da aikin sananne ne a wurin kowana abokin tarayyan.
٢
Kowane abokin tarayya ya kasance yana da wani sanannen kaso na daga riba wanda suke rabawa a tsakaninsu, ko da wani kaso na musamman ne daga cikin ɗari ne, ko ɗayansu yana da kwata, ko ɗaya cikin uku ko wanin haka, sauran kuma na ɗayan ko wani abu makamancin wannan, baya inganta yadda za a raba riba ya zamto ba sananne ba; kaman ace ɗayansu yana da dubu ɗaya daga cikin riban sauran riban kuma na ɗayan ne.
٣
Aikin tarayyan ya kasance cikin ababen da suke halal ne a shari'a, saboda haka baya halatta ga musulmi da ya shiga cikin tarayyan da ake gudanar da haramtattun ayyuka; Kaman taba ko ƙwaya, ko giya, ko yayi kasuwanci a cikinsu, ko caca ko kamfanonin waƙe da wasannin koikoyo waɗanda suka haramta ko bankunan riba, da makamantan haka na daga Abunda Allah da Manzonshi suka haramta.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa