Ɓangaren yanzu model
Darasi Tsarkin mace musulma
Musulunci ya wajabta wa mace musulma koyan ababen da take buƙata na daga hukunce-hukuncen tsarki waɗanda suka keɓanta da ita; kaman haila, da istihala, da kuma biki.
Daga cikin ababen da saninsu da kuma aiki da su ya wajaba akan mace
Wanka daga janaba
Janaba a harcen larabci shi ne nisanta, mai janaba kuma a shari'a shi ne duk wanda ya fitar da maniyyi ko yayi jima'i, kuma ana gayawa mace da miji kuma an sanya musu masu janaba ne domin an hanasu kusantar wuraren sallah har sai sun tsarkaka. Wankan janaba kuma wajibi ne saboda faɗin Allah Ta'ala: (Kuma idan kuka kasance masu janaba toh kuyi tsarki) (Alma'idah: 6).
Wanka yayin ɗaukewar jinin haila
Wanka ya wajaba akan mace musulma yayin ɗaukewar jinin haila; domin faɗin Allah Ta'ala: (Kuma suna tambayanka game da haila, kace musu shi ƙazanta ne saboda haka ku nisanci mata a cikin haila, kuma kada ku kusance su har sai sunyi tsarki, idan kuma suka tsarkaka sai kuzo musu ta inda Allah Ya umarce ku, domin lalle Allah Yana son masu yawan tuba kuma yana son tsarkaka) (Albakara: 222). to faɗinShi: (Idan suka tsarkaka) Ma'ana ida suka tsarkaka da wanka.
Haila da istihala
Haila: Shi ne jinin da yake fita daga mahaifar mace ba tare da haihuwa ko rashin lafiya ba. Amma kuma shi istihala: shi ne gudanan jini daga mahaifar mace ba a lokacin hailar da ta saba ba sakamakon rashin lafiya ko cuta.
Lokacin haila ya bambanta a wurin mata, kuma babu wani ƙayyadadden lokaci na mafi ƙarancin kwanakinshi a bisa magana mafi rinjaye na daga maganganun malamai, amma yawancin malamai sun tafi akan cewa mafi yawancin shi kwanaki goma sha biyar ne, abunda ya ƙaru akan wannan kuma to jinin istihala ne ba jinin haila ba, kuma mafi yawanci a cikin yanayin mata shi ne lalle lokacin haila kwanaki shida ne zuwa bakwai.
Wanka yayin ɗaukewan jinin biki
Malamai sun taru akan cewa lalle ya wajaba akan mace mai jinin biki da tayi wanka yayin da bikinta ya ƙare.
Ma'anan Biki
Shi ne jinin da mahaifa take zubo da shi tare da haihuwa da kuma gabanin haihuwa da kwanaki biyu ko uku, tare da wata alama -tamkar ciwo- da kuma bayan haihuwa har na tsawon kwanaki arba'in. Amma kuma lokacin biki mafi tsawonshi shi ne kwanaki arba'in, kuma babu wani lokaci na mafi ƙarancin shi, a duk lokacin da mace taga tsarki zatayi wanka ta kuma yi sallah.
Ababen da suke rataya akan haila da kuma biki
Haramcin Jima'i
Ya haramta ga mutum da ya sadu da matarshi wacce take da jinin haila, domin faɗin Allah Ta'ala: (Kuma suna tambayanka game da haila, kace musu shi ƙazanta ne saboda haka ku nisanci mata a cikin haila, kuma kada ku kusance su har sai sunyi tsarki, idan kuma suka tsarkaka sai kuzo musu ta inda Allah Ya umarce ku, domin lalle Allah Yana son masu yawan tuba kuma yana son masu tsarkaka) (Albakara: 222), haka ma saduwa da mace mai biki ya haramta da ijma'in malamai.
Haramcin Saki
Saboda faɗin Allah Ta'ala: (Ya kai Annabi, idan zaku saki mata to ku sake su ga iddarsu) (Aɗɗalaƙ: 1). Kuma ma'anan faɗin Allah Maɗaukakin Sarki: (Ku sake su ga iddarsu) shi ne kada ya sake ta alhali tana cikin jinin haila ko na biki, ko a cikin tsarkin da ya sadu da ita a cikinshi kuma ɗaukan cikinta bai bayyana ba.
Haramcin Sallah da Azumi
Saboda faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: (Shin ba idan suna haila basa sallah kuma basa Azumi ba, to wannan yana daga cikin tawayar addininsu) (Bukhari: 1951).
Haramcin Ɗawafi
Domin faɗin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ga Aisha yayin da tayi haila a cikin aikin hajji: «To alle wannan abu ne wanda Allah Ya rubutawa ƴaƴan Adam (Mata), ki aikata duk wani abunda mahajjaci yake aikatawa sai dai kada kiyi ɗawafi da ɗakin Allah har sai kin tsarkaka» (Bukhari: 305, Muslim: 1211).
Haramcin shafar Alkur'ani
Domin bin umarnin Allah Ta'ala: (Babu wanda zai shafe shi sai tsarkaka) (Alwaki'ah: 79), amma kuma zata iya karatun Alkur'ani daga haddanta a bisa zance mafi rinjaye, koma bayan mai janaba, domin lalle ita ba zata karanta Alkur'ani ba har sai tayi wanka. kuma idan mace mai haila ko biki ta buƙaci muraja'ar wata aya daga cikin Alkur'ani ko karantar da wata ko makamancin haka, to zata iya shafan Alkur'ani da wani shamaki; kaman safar hannu da makamancinshi.
Haramcin zama a cikin Masallaci
Domin faɗin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Lalle Masallaci baya halatta ga mai haila ko mai biki" (Abu Dawood: 232), Amma kuma wucewa a cikinshi ko ɗaukan wani abu domin larura, to ya halatta, an karɓo daga Aisha Allah Ya kara mata yarda tace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gaya mini: «Miƙa mini sallaya daga cikin masallaci», tace: sai nace: Ina haila, sai yace: «to ai hailarki ba a hannunki take ba» (Muslim: 298).
Ababen da haila yake wajabta su
Balaga
Mutum yana zama mukallafi ne yayin da ya balaga, kuma haila tana daga cikin ababen da suke tabbatar da alamun balaga ga budurwa.
Yin Iddah da shi ga wanda aka sake ta
Lalle iddar wanda aka saketa yana ƙarewa ne da yin haila har sau uku ga wanda ta kasance tana yin hailan, domin faɗin Allah Ta'ala: (Matan da aka sake su suna jira ne da kawukansu har na lokacin haila uku) (Albakara: 228).
Abunda ke nuna cewa mace ta tsarkaka daga haila
Farin abu
Wani abu ne mai kama da farin zare wanda yake fita daga farjin mace a ƙarshen ranakun hailarta, kuma ya kasance alama ne na tsarkinta.
Daukewar jini da bushewa
Shi ne mace ta cusa wani abu kaman auduga a cikin farjinta ta fito da shi ba tare da ya jirkata da jini ko wani abu makamancinshi ba.
Wanka yana da farillai guda biyu: Anniyyah da game gashi da kuma dukkanin gangan jiki da ruwa, kuma isar da ruwa zuwa mafitan gashi ya wajaba, ta inda zai isa zuwa fatar da take ƙarƙashin shi, ko da gashin ya kasance da yawa ne ko kaɗan ne.
Yadda mace zata yi wanka daga haila da kuma janaba
Daga Aisha Allah Ya kara mata yarda, lalle Asma'u ta tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi game da wankan mai haila? sai yace: «Ɗayanku zata ɗauki ruwanta da abun wankanta, sai tayi tsarki ta kuma kyautata shi, sai ta zuba ruwa akanta ta cuccuɗa shi cuccuɗawa mai tsanani har sai ta kai fatar kanta, sa'annan sai ta zuba ruwa a jikinta sai ta samu soso ta tsarkaka da shi» sai Asma'u tace: to ta yaya zata tsarkaka da shi? sai yace «Subhanallahi! zaki tsarkaka da shi» Aisha tace: Kamar tana ɓoye wannan kina bin alamun jinin. kuma sai ta tanbaye shi akan wankan janaba sai yace:«Ki ɗauka ruwanki sai ki kyautata tsarki, sai ki kwara ruwa akanki ki cuccuɗa shi sosai har sai ya kai matsiran gashinki sa'annan sai ki kwara ruwa a jikinki, Aisha tace hakane matan Ansar suke kunya bata hanasu neman fahimtar Addini) (Bukhari: 332, Muslim 314).
Lalle duk wani shamakin da zai hana ruwa daga isa zuwa gangan jiki to zai lalata wanka kuma ya mayar dashi bai inganta ba, kaman mace ta sanya wani abunda zai hana ruwa isa zuwa farcenta, ko samuwan wani abunda ruwa bazai shige shi ba.
Wani abu yelo-yelo
Wasu ababe ne da suke fitowa daga farjin mace -gabanin haila ko bayanta- idan ya kasance yana haɗe da haila to lalle yana daga gare ta, to anan ya wajaba ta dakatar da sallah da kuma sauran ababen da haila take hanawa, amma kuma idan ta kasance bata tare da haila to bata da wani tasiri; domin hadisin Ummu Aɗiyyah Allah Ya kara mata yarda: «Mun kasance ba ma la'akari da abu yelon da yake fitowa bayan tsarki a matsayin wani abu» (Bukhari: 326, Abu Dawood: 307 kuma lafazin nashi ne)