Ɓangaren yanzu model
Darasi Tufafin Mace Musulma
Tufafi babban ni'ima ce daga Allah Mai girma da ɗaukaka wanda ya ni'imtawa mutane da shi; da shi ne mutum yake suturta jikinshi yake kuma kiyaye shi daga zafin rana da kuma sanyi da wanin haka, haka kuma ado ne da ƙawa: Allah Ta'ala Yace: (Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!) (Al-A'arafi: 26). Kuma tufafi daga cikinshi akwai wanda yake wajibi ga kowa na miji da ta mace, kuma shi ne abunda zai suturta Al'aura, daga cikinshi kuma akwai wanda na ado ne da kuma ƙawa domin zuwa bukukuwan aure, da Eidi da wanin haka.
Hukunce-hukuncen Musulunci dangane da suturar mata suna cimma manyan-manyan manufofi; ta ɓangaren mace, suna ba ta sirri, da kariya daga kallon maza, da kuma kariya daga miyagun ayyuka da zantuka .Tufafin Musulunci kuma yana baiwa mace natsuwa da kwanciyar hankali da mutunci da mutuntawa. Kuma ta hanyar riƙo da suturar Musulunci, babu shakka mace tana bayyana bautarta da ƙasƙantar da kai ne ga Allah Maɗaukakin Sarki, ta hanyar bin umarninSa da nisantar haninSa, don haka ta cancanci falala da baiwa da kuma rahamar Allah Mai girma da ɗaukaka.
A ɓangaren al'umma kuma, lalle suturar mace ko hijabi yana kare al'umma gaba ɗaya daga fitina kuma zai tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro ga dukkan ɗaiɗaikun mutane a cikin Al-ummah. kuma fitina idan ta auku zata lalata Al-umma kuma zata watsar da ita da dukkanin ababen dake cikinta na maza da mata, daga nan kuma za a rasa natsuwa da jin daɗi da kwanciyan hankali a cikin iyalai. kuma wannan abu ne wanda muke gani a kasashe da yawa.
Sharruɗan hijabin mace musulma
1- Suturta Jiki
Allah Ta’ala ya ce: {Ya kai Annabi ka ce wa matanka da ƴaƴanka mata da matan muminai su kusantar da tufafinsu (idan sun fita). Wancan ne mafi cancantar a gane su, kuma kada a zãlunce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin kai.} [Ahzab: 59]. Malamai sun yi saɓani game da rufe fuska da hannu. Wasu sun ce wajibi ne, wasu kuma sun ce mustahabbi ne, amma duk sun yarda cewa wajibi ne a rufe komai.
2- Kada ya kasance Ado ne a karan kanshi
Kuma wannan ya shiga cikin faɗin Allah Ta'ala: (Kuma kada su bayyana adonsu) (Alnur: 31).
3, 4- Ya kasance mai kauri kuma mai faɗi.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Kashi biyu na daga mutane suna daga cikin ƴan wuta amma ni ban gansu ba, wasu nutane suna ɗauke da bulala kaman biccon shanu suna dukan mutane da su, da kuma wasu mata da tufafi a jikinsu amma kuma tsirara suke, a karkace suke kuma suna karkatarwa, kansu tamkar tozon raƙumi mai girgiza, ba za su shiga Aljannah ba kuma ba zasu ji ƙamshinta ba, kuma lalle ana samun ƙamshinta ne daga tafiyar kaza da kaza» (Muslim: 2128). Daga Usamah Ɗan Zaid Allah Ya kara musu yarda yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tufatar dani da wani tufafin Ƙibdiyyah mai kaushi yana daga cikin abunda Dahiyyatul Kalbi ya bashi, sai na tufatar da mata ta da shi, sai manzon Allah yace mini: «Ya baka sanya tufafin da na baka ba?» sai nace mishi na baiwa mata ta ne, sai yace: «To ka umarce ta da ta saka wani abu a ƙarƙashin shi domin ina tsoron kada ya dinga nuna jikinta» (Ahmad: 21786).
5- Kada ya kasance an turara shi yana ƙamshi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Duk wata matan da ta sanya turare ta wuce wasu mutane domin suji ƙamshinta to mazinaciya ce» (Annasa'i: 5126).
6- Kada yayi kama da tufafin maza
Daga Ɗan Abbas Allah Ya kara mishi yarda yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Allah Ya tsinewa masu kama da mata daga cikin maza da kuma masu kama da maza daga cikin mata" (Bukhari: 5885).
7- Kada yayi kama da tufafin Kafurai
Lalle ya tabbata a cikin shari'ar musulunci cewa baya halatta ga musulmi na miji ne ko ta mace da suyi kama da kafurai cikin ibadunsu, da bukukuwansu da kuma tufafinsu da suka keɓanta da su, saboda faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: «Duk wani wanda yayi kama da wasu mutane to yana daga cikinsu» (Abu Dawood: 4031).
8- Kada ya kasance tufafin alfahari ne
Saboda faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: «Duk wanda ya sanya tufafin alfahari a duniya Allah Zai sanya mishi tufafin ƙasƙanci a ranar alkiyama, sa'anna ya sanya mishi wuta a cikinshi» (Ibnu Majah: 3707). Tufafin alfahari shi ne duk wani tufafin da ake neman shahara a tsakanin mutane da shi.
Sharruɗan da suka gabata suna da alakƙa ne da tufafin mace musulma yayin fitanta daga gida ko kuma yayin da zata kasance a cikin maza waɗanda ba muharramanta ba. Kuma baya wajaba akanta da ta aiwatar da waɗannan sharruɗan a gaban muharramanta ko yayin haɗuwa da ƴan uwanta mata, a cikin wannan yanayin an halatta mata sanya turari tare da bayyana wani shashi na daga adonta cikin wasu ƙa'idoji sanannu.
Bayyana Tsaraici (Tabarruji)
Shi ne mace ta bayyana wa maza waɗanda ba muharramanta ba adonta da kuma kyawunta wanda ya wajaba akanta ta ɓoye shi daga gare su.
Tufafin mace musulma dubi da waɗanda suke kewaye da ita
Tufafin mace musulma a gaban waɗanda ba muharramanta ba (Baƙi)
Shi ne hijabin shari'a wanda Allah da ManzonShi sukayi umarni da shi, kuma shi ne wanda aka ambaci sharruɗan shi a baya.
Tufafin mace musulma a gaban muharramanta na daga maza
Ya wajaba akanta da ta suturta dukkanin jikinta a gaban su sai dai abunda yake yawan bayyana daga gare ta; kaman wuya, da gashi, da diga-digai, da kuma fuska da tafukan hannu. Allah Ta'ala Yace: (Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõmãtan) (Alnur: 31).
Tufafin mace musulma a gaban wasu musulmai mata
Ya wajaba a gare ta da ta suturta dukkanin jikinta sai dai abunda yake yawan bayyana daga gare ta kaman wuya da gashi da diga-digai ƙari akan fuska da tafukan hannu. Allah Ta'ala Yace: (Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu) (Alnur: 31). faɗinshi (Ko matan ƙungiyansu) yana nufin musulmai mata.
Tufafin mace musulma a gaban matan Ahlul kitabi.
Ya wajaba akanta -Kaman yayin da take gaban musulmai mata- da ta suturta dukkanin jikinta sai dai abunda yake yawan bayyana daga gare ta; kaman wuya, da gashi, da diga-digai, domin matan ahlul kitabi sun kasance suna shiga kan uwayen muminai, kuma ba a rawaito cewa lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarce su da su ƙaurace musu ba.
Nau'ukan tufafin mace musulma da adonta ta ɓangaren halacci da haramci
Tufafi da Ado waɗan da suke halal.
Asali a cikin Tufafi da ado shi ne halalci, kuma ba a togace kowanne daga cikin hakan sai dai wanda shari'a tazo da haramcin shi; Saboda haka ya halalta ga mace da ta sanya dukkanin nau'ukan Tufafi a bisa bambance-bambancen launinsu da yanayin yadinsu, kuma tayi ado da dukkanin nau'ukan ado waɗanda suke halal, kuma tayi amfani da turaruka da ababen ƙawa, amma da sharaɗin ya kasance ba zai cutar da ita ba, kuma kada ya kasance a cikinshi akwai kama da kafurai, kuma ya kasance ba ayi amfani da haramtattun abubuwa yayin ƙera shi ba kaman man alade alal misali.
Tufafi da Ado waɗan da suke mustahabbi ne
Abunda ake nufi da hakan shi ne duk wani abunda shari'a ta zo da shi na mustahabbi, da kuma dukkanin tufafin da mace zata yiwa mijinta ado da shi domin burge shi da kuma nuna mishi soyayya, amma da sharaɗin kada ya kasance na haramun ne.
Tufafi da Ado waɗan da suke haramun ne
Abunda ake nufi da hakan shi ne duk wani abunda shari'a ta haramta ta kuma tsawatar akanshi na daga tufafi da ado, ko da nassin shari'a ne ya haramta shi ko kuma ya saɓawa ƙa'idojin shari'a waɗan da aka umarci musulmi da lizimtarsu, kaman saɓawa Yahudu da Nasara, da rashin kama da maza, da wanin haka.