Ɓangaren yanzu model
Darasi Gado a cikin Musulunci
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Gado tsari ne na ɗan Adam na duniya baki ɗaya, al'ummomi da dama sun yarda da tsarin gado a zamanin da da na yanzu, domin ya dace da yanayin halittan ɗan Adam wajen so da kuma ƙoƙarin mallakar abu, kuma yana magance matsalar amfani da kuɗin mamaci bayan rasuwarsa.
Hukunce-hukuncen gado a cikin shari'ar Musulunci ta bambanta ta hanya bayani filla filla akan ababe da yawa, waɗanda suke da alaƙa da yanayin wanda za a gada, da waɗanda za suci gado, da kuma kason kowanne daga cikinsu, cikin wani cikakken tsari abun mamaki. kuma daga cikin amfanin bayani a cikin tsarin gado a Musulunci daƙile sabbuban tarzoma tsakanin Makusantan mamaci; saboda idan magada suka san cewa lalle an raba musu gado ne da umarnin Allah Mai girma da ɗaukaka, to rayukansu zasu samu natsuwa, kuma zasu yarda da kason Allah Maɗaukaki, kuma daga cikin amfaninshi shi ne kiyaye haƙƙin dukkanin magadan ta yadda ba a bar abun a hannun wasu su rabashi yadda suke so da ƙoƙarinsu ba domin kada su baiwa wanda suke so su hana wanda suke so wanda hakan kuma zai iya haifar da saɓani da gaba tsakanin magada.
Rukunnan Gado
Shi ne mamaci -ko wanda yake cikin hukuncin mamata- wanda ya bar abunda za a gada.
Shi ne rayayye bayan wanda za a gada -ko kuma wanda yake cikin hukuncin rayayyu- wanda ya cancanci ya gaji wanda za a gada da wani sababi daga cikin sabbuban gado.
Shi ne abunda wanda za a gada ya bari na daga dukiya ko wani abunda za a gada.