Ɓangaren yanzu model
Darasi Aro
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ma'anan aro
Hukuncin aro
Hikimar shar'anta aro
Daga cikin rahamar Allah Mai girma da ɗaukaka ne Ya halalta aro; domin biyan buƙatan wanda za a lamuncewa, tare da samun ladan wanda ya ba da aron, domin ya amfanar da ɗan uwanshi ne ba tare da ya rasa abunshi ba.
Allah Maɗaukakin Sarki Yace: (Kuma kuyi taimakekkeniya akan bin Allah da taƙawa, amma kuma kada kuyi taimakekkeniya akan zunubi da zalumci) (Alma'idah: 2).
An karɓo daga Anas Ɗan Malik Allah Ya kara mishi yarda yace: Akwak wani lokacinda ya kasance akwai tsoro a cikin Madina, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ari doki daga Abu Ɗaljata ana cewa dashi: Almandubu, sai ya haushi, a yayin da ya dawo sai yace: «Babu wani abunda muka gani, idan ma akwai wani abunda muka samu to shi ne kogi» (Bukhari: 2627, Muslim: 2307).
Sharadin ingancin aro
Rukunnan Aro
Ya wajaba akan wanda aka baiwa aro da ya kiyaye aron, ya kuma lura da shi, ya kuma yi amfani da shi yadda ya kamata, ya kuma komar da shi zuwa ma'abocinshi ba tare da wani aibi ba. Idan abun aron ya salwanta a hannun wanda aka arawa ba tare da yayi amfani da shi ba, to zai biya sawa'an yayi sakaci da shi ne ko baiyi ba, amma kuma idan abun ya samu damuwa ta hanyan amfanin da aka mishi izini da shi ne, to babu biya, sai dai idan wanda aka arawan ya baiwa wani ko yayi sakaci da shi.
Ya wajaba akan wanda ya ari wani abu da ya komar da shi yayin da ya gama biyan buƙatarshi, kuma ya mayar da shi ba tare da wani aibi ba kaman yadda ya are shi, kuma baya halatta a gare shi da ya barshi a wurinshi ko yayi sakaci da shi, idan kuma har ya aikata hakan to ya zamto mai ha'inci mai laifi.
Wanda ya bayar da aro yanada damar karɓo abunshi a duk lokacin da yaga dama muddin hakan ba zai cutar da wanda ya ara ba, idan kuma ya kasance akwai cutarwa ga wanda ya ara a cikin karɓowan, sai ya jinkirta karɓan har sai wannan cutarwar ta gushe; kaman wanda ya ari fili yayi shuki akanshi, to baya halatta ga wanda ya ara mishi da ya karɓi filin har sai ya girbe shukan shi.
Allah Madaukakin Sarki Yace:(Lalle Allah Yana umartan ku da ku mayar da amana zuwa ga masu su, kuma idan kunyi hukunci a tsakanin mutane kuyi hukuncin da adalci, lalle madallah da abunda Allah Yake muku wa'azi da shi. Lalle Allah Ya kasance Mai yawan ji mai yawan gani) (Albakara: 58).