Ɓangaren yanzu model
Darasi Mace da da'awar zamani
A zamanin da da kuma a mafi yawan tsoffin wayewa, mata ba su sami wata kulawa ta mutuntaka da mutunci ba. Maimakon haka, an yi watsi da su kuma ba ayi la'akari da su ba. Ba su da wani haƙƙi ko doka, kuma sun kasance ana sayansu kuma ana sayar da su ba tare da la’akari da yanayinsu na ɗan adam ba. Ana kallon su a matsayi da darajar da ta kasa na maza.
Wannan tsari na wulaƙanta mata ya ci gaba a cikin wayewa da al'adu daban-daban har zuwa kwanan nan. Ko da yake alal misali ƙasashen yammacin duniya (Nahiyan turai), daga baya sun fara wani salon canji da ƴantar da su daga zaluncin dauloli da kuma rashin adalci na coci, wannan sauyin bai kai ga mata da al’amuransu ba sai daga baya.
Wannan karkataccen ra'ayi game da wulaƙanta mata ya sami goyon baya ne ta manyan ɓangarori guda biyu:
Masana falsafa a zamanin da sun raina mata, sun wulaƙanta su, ba su ba su wani matsayi ko haƙƙi ba. Daga cikin waɗannan masana falsafa akwai Socrates, Plato, da Aristotle.
A addinin Hindu mace ba ta da damar gadon iyayenta, kuma idan mijinta ya mutu dole ne a ƙona ta tare da shi domin gara ta daina rayuwa bayansa! Su kuma Yahudu da Nasara, mata basu da daraja a cikinsu, kuma suna zarginsu da cewa su ne tushen mugunta da fasiƙanci da zunubai, kuma sun ɗauke su a matsayin Najasa. Kuma an samo waɗannan ra’ayoyin ne daga gurɓatattun littattafansu, waɗanda suka fito daga taron addini da aka yi, kuma shugabancin firistoci da coci sun goyi bayansu.
A zamanin da muke ciki a yau wasu tarun ra'ayoyi, da aƙidu sun bayyana waɗanda suka yi tasiri -kuma basu gushe ba suna ci gaba da tasiri- akan ra'ayoyi, hasashe, da halayen al'ummomi da yawa game da al'amuran mata.
1- Zamani da abunda ke bayan Zamani
Zamani ya sanya ɗan Adam ya zamto shi ne abun mai da hankali akai a cikin duniya, kuma ya tabbatar da cewa lalle mutum bai da buƙatan wahayi, kuma lalle zai iya amfani da hankalinshi wajen ba da bayani game da kansa, da yanayinsa, da kuma duniya gaba ɗaya. Kuma yawancin waɗannan ra'ayoyi, da tunani, da nazarin sun samo asali ne daga zamani.
2- Hankali
Wannan kuma shi ne ɗaukaka sha'anin hankali da ma'aunan shi, dubi da la'akarin cewa lalle mutum shi ne cibiyar Kauni.
3- Ƴanci da kaɗaici
Yana nufin tabbatar da ƴancin ɗan adam wajen samar da yadda zai gudanar da al'amuran rayuwarshi kaman yadda yakeso.
Wannan ita ce nazariyyar da take magana game da asalin mutum da juyin halittarsa cikin miliyoyin shekaru har ya zamto a cikin yanayin da yake a yanzu.
5- Ƴanta Mace
Tunanin Ƴanta mata ya taso ne daga nahiyar Turai, inda mata suka sha fama da zalunci iri-iri da rashin adalci, wanda hakan ya sa mata suka riƙa ɗaga tutoti masu taken sama musu ƴanci da kuma ƴantar da su daga tsoffin al’adu. Mata a can sun samu da yawa daga ƴancin ɗan adam, na zamantakewa, da siyasa, da kuma tattalin arziki, amma waɗannan buƙatun ba su kasance akan wani tsari na addini ko ɗa'a ba. sai suka juya suka koma ƙira ne zuwa ga ƴantarwa daga addini da kyawawan dabi’u, ba ƴantar da su daga zalunci da wulaƙanci ba, kuma aka kulle dukkanin waɗannan ababe da da’awar ƴantarwa daga mulkin mazaje ko na ubanni.
Almaniyanci da ƴanta mace
Daga cikin ra'ayoyi da ƙiraye-ƙirayen da ke da alaƙa da manufar ƴanta mata akwai: raba addini da kowane fanni na rayuwa, da kuma amfani da ilimin boko a matsayin hanyar rayuwa. Wannan ra’ayi yana da nasaba da Almaniyya ta hanyar ƙiran ƴanta mata daga duk wani abunda zai iya kawo musu cikas wajen cika burinsu, musamman ma tsare-tsare da kuma koyarwar addini.
Yana nufin raba al’amuran da suka shafi gudanar da dukkanin al’amuran rayuwa da addini, farawa da la'akari da mutum a matsayin asalin ayyukan ɗan Adam a dukkanin ɓangarorinsu; na daga siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewa da sauransu.
7- Daidaita tsakanin jinsu biyu (Na miji da ta mace)
Wannan da'awar dai ta ginu ne bisa tushen daidaito tsakanin maza da mata ta fuskar ilimi da aiki da hakkokin jama'a da siyasa da dai sauransu, da kuma kawar da duk wani nau'i na nuna wariya ga mata. Sai dai kuma buƙatu na neman daidaiton sun karkata daga mahallinsu na asali, inda suka zama akwai rashin lura da bambance-bambancen da suke tsakanin maza da mata, sakamakon haka sai suka rikiɗe zuwa ƙira zuwa daidaita tsakanin ababe guda biyu waɗanda suka kasance daban-daban.
Matantaka ita ce da'awar da take ƙira zuwa ƴanta mata da kuma daidaita tsakanin su da maza, kuma daga wannan da'awar ne wani yunƙuri ya bayyana wanda suke gudanar da ayyuka da dama na daga ilimi, da siyasa, da zamantakewa, da dai sauransu. Kuma wannan tunani na ƴanta mata da ayyukansa daban-daban ya kafa ra'ayoyi da yawa da kuma ayyuka a cikin Al-ummah.
Tushen tunanin matantaka
Yarjejeniyar CEDAW
Kungiyoyin kare haƙƙin mata da na matantaka sun nemi samun goyon bayan siyasa ta hanyar amincewan ƙasashe da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙulla a shekara ta 1979 don kawar da duk wani nau'i na nuna wariya ga mata, kuma wannan shi ne Yarjejeniyar kawar da duk wani nau'i na nuna wariya ga mata (CEDAW).
Asalin yarjeneniyar CEDAW
Yarjejeniyar ta ginu ne a kan cikakkiyar daidaito da kamanta tsakanin maza da mata a kowane fanni; fannin siyasa, da na tattalin arziki, da na zamantakewa, da na wasanni, da na shari'a da makamantansu. Kuma babu shakka Wannan ka’ida ce da ba daidai ba, wacce ta saɓawa shari'o'in da aka sauƙar dasu daga sama, kuma ta saɓawa zahirin Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah da abin da hankali ya ke ganin cewa mai kyau ne, da kuma abin da aka gina ɗabi'un ɗan Adam akai. Amma ta inda ya saɓawa zahirin Alkur'ani, saboda faɗin Allah cewa: {Kuma namiji ba ya zama kamar mace} [Ali-imrana: 36], da faɗinSa: {Maza su ne masu lura da mata} [AlNisa: 34], da kuma faɗinSa: {Kuma maza suna da darajoji a kansu} [AlBaƙarah: 228]. Ta inda ya saɓawa Sunnah kuma shi ne saboda faɗin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Kowanenku makiyayi ne, kuma kowannenku za a tambaye shi game da kiwonshi... Namiji makiyayi ne a cikin gidansa kuma za a tambaye shi game da kiwonshi, kuma mace makiyayiya ce a gidan mijinta kuma za a tambaye ta game da kiwonta" (Bukhari 893, da Muslim 1829). Dangane da saɓawarsa ga abin da ya tabbata a cikin zukatan mutane kuma ba ya buƙatan wani bayani mai yawa, domin a fili yake cewa bambance-bambance wajen halittan gangan jiki da na hankali dole ne su haifar da bambance-bambance na ƙarfi da kuma ayyukan rayuwa, saboda haka, samun cikakken daidaito da kamanceceniya ya saɓawa ainihin halittar namiji da mace.
CEDAW da gaba tsakanin maza da mata
Ƙungiyar CEDAW da masu kare haƙƙin mata suna kallon dangantakar da ke tsakanin maza da mata a matsayin alaƙar kishiya da rikici na tarihi wanda suke son kawo ƙarshen su, kuma hanyarsu ta yin hakan ita ce cikakken daidaito tsakanin maza da mata, suna masu da'awar cewa duk wani ƙarin fa'ida ga maza yana cin gajiyar mata ne. Wannan gurgun ra'ayi ne; domin alakar dake tsakanin mace da namiji alaƙa ce ta haɗin kai da taimakekkeniya, ba ta gasa da gaba ba. Kowannensu yana da matsayinsa da aikinsa, cikin jituwa da haɗin kai, don wadatar da rayuwa, da kuma samar da sanayya, da ƙauna, da jinƙai, da kiyaye nau'in. Allah Ta'ala Yace: (Ya ku mutane, lalle Mun halicce ku ne daga na miji da ta mace, kuma Muka sanya ku dangi daban-daban da ƙabilu daban-daban domin ku san junanku. Lalle mafifici a cikinku shi ne wanda ya fiku tsoron Allah, Lalle Allah Mai yawan sani ne Mai yawan ƙididdiga) (Alhujurat:13), kuma Allah Ta'ala Yace: Kuma daga cikin ayoyinShi cewa Ya halitta muku mata daga gareku domin ku samu natsuwa zuwa gare su, kuma Ya sanya a tsakaninku ƙauna da tausayi. Lalle a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani) (Arrum:21), Haka kuma lalle bambancin matsayin rayuwa yana wajabta samun bambanci a haƙƙi da ayyuka ba tare da zalunci ko rashin adalci ba. Saboda haka, duk wani ƙarin aiki yana samar da ƙarin haƙƙi, kuma wannan shi ne adalci.
Shin shari'a tana kira zuwa ga daidaita tsakanin na miji da ta mace?
Shari'ar Musulunci ta tabbatar da daidaiton mata da maza a cikin mutuntakarsu da karamcinsu na halitta, da alhaƙin da suke da shi, da amanarsu, da sakamakonsu na duniya da na lahira, da kuma yadda kowanne daga cikinsu ya cancanci haƙƙoƙinshi, da kiyaye dokokin addini, da kyawawan halaye. Sa'annan kuma, lalle shari'ar Musulunci ta bambanta tsakanin su saboda bambance-bambancen da suke da shi na yanayin halittan gangan jiki da na hankali. Ba a buƙatar mata da yin jihadi domin raunin ƙiransu, kuma ba sa sallah ko azumi a lokacin haila ko jinin biki, haka nan ba a wajabta musu ciyar da gida ko da mawadata ne. Dalilin haka ne, Shari’a ta ɗaurawa maza jihadi, kuma ta ɗaura musu ciyar da mata da ƴaƴansu, kuma ta sanya hakan wajibi ne wanda za a hukunta su akai idan suka ƙi ko suka gaza. Haka nan kuma ta ba su ƙarin haƙƙoƙi a madadin waɗannan ƙarin ayyuka, kuma wannan shi ne ainihin asalin adalci.
Adalcin shari'a a cikin gado
A shari’ar Musulunci babu zaluntar mata a gado, kamar yadda wani lokaci ta kan ɗauki ƙasa da kason namiji, wani lokaci daidai da kasonshi, wani lokaci fiye da nashi, wani lokacin kuma ta kan yi gado alhalin shi bai yi ba. Duk wannan saboda wasu dalilai da Allah Ya sani, kuma hakan ya zo a cikin littattafan malamai.
Daga cikin irin girmama mata da Musulunci yayi
Mata suna da kariya da daraja a shari’ar Musulunci, kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa: {Duk wanda ya aikata mummunan aiki to ba za a saka masa ba face da makamancinsa. Amma kuma duk wanda ya aikata aiki na ƙwarai, na miji ne ko kuwa mace, alhali yana muminai, waɗannan za su shiga Aljanna, ana azurta su a cikinta ba tare da lissafi ba} [Ghafir: 40]. Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Mata takwarorin maza ne" (Tirmizi 113). Waliyin mace (mahaifi ko miji) wajibi ne ya samar mata da gidan zama ya kuma ciyar da ita, kuma ba za a tilasta ta da ta kashe ko dinari ɗaya ba – sai da son ranta – komai arzikinta. Ita ta zama daidai da namiji ne wajen cancanta dukiya, kuma ba wanda yake da iko akanta dangane da dukiyarta, uba ne ko miji. Kuma Mata suna da ƴancin shiga cikin saye da siyarwa, da harkokin haya, da na jinginar gida, da rarrabawa, da amincewa, da ba da lamuni, da sasantawa, da duk wasu kwangiloli da wajibai.