Ɓangaren yanzu model
Darasi Haya
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Shi ne yarjejeniya akan wani aiki ko amfani wanda yake halal kuma sananne daga abunda yake sananne ko abun wasaftawa wanda yake hannu na wani sanannen lokaci, da lada sananne.
Hukuncin haya a cikin Musulunci
Daga cikin dalilan halaccin haya
An karɓo daga Aisha Allah Ya kara mata yarda tace: "Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi da Abubakar sun ɗauki hayan wani mutum daga cikin bani Dayyil, a matsayin mai shiryarwa wanda zai kula musu da ababen hawansu alhali kuma ya kasance akan addinin kafuran ƙuraishawa, sai suka bashi ababen hawansu suka ce mishi ya kawo musu su zuwa kogon thauri bayan kwanaki uku, a safiyar rana ta ukun sai gashi ya kawo musu ababen hawansun" (Bukhari: 2264).
Hikimar dake cikin shar'anta haya
Nau'ukan haya (Ijarah)
Nau'ukan ɗan hawa (Mataimaki)
Mataimaki na musamman
Shi ne wanda zai na amfanar da sama da mutum guda; kaman maƙeri, da masaƙi, da baduƙu, da taila, idan ya kasance zaman kanshi yakeyi kuma yana karɓan aiki ne a wurin waɗanda suke buƙatan aiki daga gare shi, to wannan baya halatta ga wanda ya bashi aiki da ya hana shi yiwa wasu aiki, kuma baya cancantan ladan aikinshi har sai yayi aikin.
Rukunnan ƙulla haya (Ijarah)
Masu ƙulla yarjejeniya guda biyu
Kuma ita ce bayarwa da karɓa da kuma duk wani abunda zai tabbatar da ƙulla yarjejeniya a dokance ko a al'adance.
Amfani ko aiki
Shi ne abunda za a baiwa wanda yayi aiki ko ya amfanar sakamakon aikinshi, kuma shi ne kaman kuɗi ko farashi a babin saya da sayarwa.
Sharruɗan ingancin haya (Ijarah)
Lokacin da haya take wajaba
Idan kuma suka yarda da ƙarin lokaci ko rage lokaci, to hakan ya halalta, kuma wanda aka baiwa aiki yana cancantan cikakken ladanshi ne idan ya gama aikin shi yadda ya kamata.
Idan kuma hayar ta kasance akan wani abu ne, to za a iya biyan kuɗi bayan cikan sharruɗan amfana da shi. Daga Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Allah Ta'ala Yace: Mutane uku da Ni zasuyi husuma a ranar Alkiyama: Mutumin da aka ba shi domin Ni sai yayi yaudara, da mutumin da ya sayar da Ɗa yaci kuɗinshi, da mutumin da ya ɗauki hayan wani ya kammala mishi aikinshi sa'annan ya hana shk haƙƙinshi» (Bukhari: 2227).
Yanayin ƙarewan yarjejeniyar haya (Ijarah)
Kuma haya bata lalacewa da mutuwan ɗayan ɓangarori biyun, kuma ba zai sayar da abunda aka bada hayanshi ba, kuma duk wanda aka ɗauki hayarshi domin wani aiki na musamman sai ya mutu, to babu shakka wannan hayar ta lalace. kuma a duk lokacin da hayan ta ƙare to wanda ya ɗauki hayan zai cire hannunshi ya kuma miƙawa wanda ya bashi haya abunshi idan abun miƙawa ne.