Ɓangaren yanzu model
Darasi Bashi
Allah Mai girma da ɗaukaka ya raba arziki a tsakanin mutane da adalcinshi da kuma hikimarshi; sai ya kasance a cikinsu akwai mawadaci da matalauci, da wanda yake cikin tsanani da mabuƙaci, kuma mutane sun saba wa junansu bashi a tsakaninsu domin samun daman biyan buƙatunsu. Kuma kasancewan addinin Allah gamamme ne kuma cikakke, haƙiƙa ya zo da hukunce-hukunce masu yawa waɗanda suke da alaƙa da bashi. kuma Allah Ya keɓance bashi da mafi tsawon aya a cikin Alkur'ani mai girma, kuma ita ce aya ta 282 na daga cikin Suratul Baƙara, kuma ana ƙiranta Ayar bashi.
Ma'anan bashi
Shi ne bada kuɗi domin tausayawa wanda zaiyi amfani da shi da sharaɗin mayar da kwatankwacin shi bayan wani lokaci.
Hukuncin Bashi
Bashi abun so ne (Mustahabbi ne) ga wanda zai bayar, kuma halal ne ga wanda zai karɓa. Kuma karɓan bashi baya daga cikin makaruhan abubuwa; domin mai karɓan bashi zai karɓa bashin ne domin ya amfana da shi wajen biyan buƙatunsu, sa'annan sai ya mayar da kwatankwacin shi daga baya.
Amma kuma yayin da bashi ya kasance zai dawo da wani amfani zuwa ga wanda ya bayar to wannan ya zamto riba wanda yake haramun; Kaman ya bada bashin kuɗi da sharaɗin za a dawar mishi da ƙari. hakanan idan ya haɗa bashin da wani saya ko sayarwa ko wanin haka, to hakan ya haramta, domin bashi da ciniki baya halatta.
Allah Ya halatta bashi ne domin a cikinshi akwai tausaya wa mutane, da sauƙaƙa musu lammuransu, da yaye musu baƙin cikinsu, da taimakon mubaƙata. kuma bashi wata ƙofa ce na samun kusanci ga Allah Mai girma da ɗaukaka ga wanda ya bayar, kuma a duk lokacin da buƙata tafi tsanani ladan mai bada bashi yafi girma.
Anason tabbatar da bashi -Babba ne ko ƙarami- ta hanyan rubuta shi da kafa shaidu akanshi; sai a rubuta ƙimarshi, da nau'inshi, da lokacinshi; domin kiyaye wannan bashin, kuma domin wannan ya bayar da bashin ya samu natsuwa cewa lalle dukiyarshi ba za ta salwanta ba ko da ace wanda ya baiwa bashin ya mutu, ko ya manta, ko ya bore ko wani abu makamancin haka, Allah Madaukakin Sarki Yace a cikin Ayar bashi: (Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta. Kuma wanda bãshin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsõron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gareshi) (Albakara: 282). Kuma Allan Ya sake cewa a cikin wannan ayar: (Kuma kada ku ƙõsa ga rubũta shi, ƙarami ya kasance kõ babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi ãdalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku) (Albakara: 282).
Sharuɗan ingancin bashi
Duk wanda ya ranci kuɗi a wurin wani, to ya yi niyyar biyanshi, Haramun ne mutum ya karɓi kudin mutane ba tare da ya yi niyyar mayar musu da su ba. Idan lokacin biyan bashin ya yi, sai ya mayar da shi kaman yadda ya amsa. An karɓo hadisi daga Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda, daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Duk wanda ya karɓi dukiyar mutane da nufin ya biya su, Allah zai biya a madadinshi, kuma wanda ya karɓe ta yana nufin ya halaka ta, Allah zai halaka shi” (Bukhari 2387).
Yanayin wanda ya ranci kudi a lokacin mayar da rancen
Hukuncin Ajjiye Kuɗaɗe a Cikin Banki
Kuma ba ya halatta a sanyawa wanda ake bi bashi tara idan ya makara wajen biya a kan lokaci, domin riba ce, kuma bai halatta a yi rance da wannan sharaɗi ba, ko da wanda ya karɓa yana ganin zai iya biya a kan lokaci ba tare da an ci shi tarar ba, domin yin hakan ya shiga cikin yarjejeniyan da riba ke lizimta a cikin shi.
Kyautatawa yayin biyan bashi
Kyautatawa wajen biyan bashi -Kaman a ba shi rancen wani abu sai ya dawar da wanda ya fishi kyau, ko wanda yafi girma, ko ya fishi yawa- wannan mustahabbi ne (Abun so) idan har hakan bai kasance sharaɗi bane; domin wannan yana daga cikin kyakkyawar biya, da kyawawan halaye, idan kuma hakan ya kasance sharaɗi ne toh wannan shi ne riban da aka haramta.